10/08/2025
Ugo wani ɗan fashi ne wanda ke yin sata ne kawai a ƙarshen mako. A wani dare na ranar asabar, ya kutsa cikin wani gida domin ya yi sata, amma sai "Ana", wata kyakkyawar mata mai shekaru kusan talatin ya shigo cikin gidan ta, Bayan ya yi mata barazana da bindiga, ta mika masa kayan zinarenta da dukiyarta da kayan ta masu tsada, tana roƙonsa da kada ya kusanci ’yarta "Pauli", yarinya ’yar shekara uku, Ugo ya yi tunani yace Ina mijinki, tace baya gari yana wajan aiki ba ze dawo ba se gobe lahadi da yamma:
Aransa yace Me xe ya sa in tafi da wuri, alhali komai yana tafiya daidai a nan?”
Ya ga cewa zai iya zama a gidan har zuwa ya kwana ya more, tunda mijin Ana ba zai dawo daga tafiya ba sai yammacin Lahadi,
ya san wannan ne bayan da ya ke bibiyan rayuwarsu. Bai ɓata lokaci ba wajen yanke shawara ya sa kayan mijin gidan, ya umurci Ana ta dafa masa abinci, ta kawo ruwan lemo mai dadi, kuma ta kunna faifan kiɗa yayin cin abincin dare, domin a wurinsa, babu rayuwa ba tare da kiɗa ba.
Ana na cikin damuwa da kulawa da ’yarta Pauli, amma yayin da take dafa abinci sai wata dabara ta fado mata don kawar da wannan barawon. Amma ba ta da damammaki da yawa, domin Ugo ya yanke igiyar sadarwa na wayar taraho, gidan kuma a kebance yake da daddare babu wanda zai zo.
Saboda haka, ta yanke shawarar zuba masa ƙwayar barci cikin ruwan lemo Yayin cin abincin dare, sai Ugo wanda a sauran ranakun mako yana aiki a matsayin mai gadin banki, ya gano cewa Ana ita ce mai gabatar da shirin kiɗan gargajiya da yake sauraro kullum ba fashi. Ya yi matuƙar sha’awarta tun da daɗewa. Yayin da suke sauraron fitaccen mawaki "Benny" yana rera “Cómo fue”, s**a fara hira game da kiɗa da mawaka. Ana ta fara jin kunyar abin da ta yi, domin lamarin yana tafiya lafiya, kuma bai nuna wata niyyar cutar ga ita ba. Amma abin mamaki Ugo ya shanye shi duka cikin annashuwa.
Amma sai wani kuskure ya faru, ba Ugo ba ne ya sha ruwan da aka zuba ƙwayar barci, ita Ana ce ta kwankwadeshi duka Nan take barci ya ɗauketa.