05/09/2025
Jagoran da ya k**ata ya zama kariya ga jama’a ya juya ya zama barazana garesu; Shin a haka zamu cigaba da rayuwa?
By Yakub Nasir Khalid
Mutum mai iyali da yara sama da ashirin, amma bai iya tsayawa wajen kare ‘ya’yan al’ummarsa daga yunwa, rashin ilimi, damuwa da lafiyarsu da rashin aikin yi. Tunda ya kasa kare jama’arsa daga wulakanci da samar da abin da ya dace, shin mai yasa ya tsaya tsayin daka wajen kare kansa daga zarge-zargen kisa......?
Jagoran da ya k**ata ya zama kariya ga jama’a ya juya ya zama barazana gare su. Lokacin da ake buƙatar kulawa da ci gaba, ya jefa jama’arsa cikin damuwa da far aba musamman lokutan zabe. Lokacin da ake bukatar shugabanci da adalc, hakan ya tabbatar da cewa shi ba jagora na gari bane.
An zarge shi akan abubuwa da dama da ya k**a ta amasa hukunci akan domin kare alumma daga koma bayan tarbiyya da kuma samun ingantaccen Shugaban a yankin, amma ya Shiga rigar mulki ya buya.
A shekarar 2023 akwai tarin zarge-zargen kisa, kone gidaje, da jefa jama’a cikin rikici sun tabbatar da cewa siyasar sa bata kawo ci gaba ko zaman lafiya bace, illa tashin hankali da rugujewar al’umma yankinmu. Wanda hakan kawo rasa rayuwakan mutane da dama, shin a haka zamu cigaba da rayuwa?
Alhassan ba jagora ba ne, bala’i ne ga jama’a. An zarge shi da kisan kai, tashin hankali da kone ofis, abin kunya da wulakanci. Shugabancinsa kazanta ne da ke rusa alumma, mutum mai irin wannan tabo bai cancanci kujerar jama’a ba.
A 2023 ya shiga hannun jami’an tsaro bisa zargin kisan kai da haɗin baki wajen tada rikici a Tudun Wada. Shugaba na gaskiya da kuma son cigaban alumma bazai bai k**ata a taɓa danganta shi da jinin al’ummarsa ba; tabbas muna bukatar sauyi.
A lokacin yaƙin neman zaɓe a 2022, Doguwa ya ce a fili: “Ranar zabe ko dai ku zabi jam’iyyar APC, ko kuma a yi muku hukunci.” Wannan magana ba siyasa ba ce, barazana ce ga jama’a. Shugaban da ke barazanar jama’arsa ba shugaba ba ne, mai zalunci ne.
Yakub Nasir Khalid
Email: yakubunasirukhalid@gmail