22/12/2025
Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ce ya kammala dukkan shirye-shiryen tsaro domin bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara a fadin jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ’Yan Sanda ta Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a yau Litinin.
Sanarwar ta bayyana cewa Kwamishinan ya gudanar da muhimmin taron tsaro da manyan jami’an rundunar, bisa umarnin Sufeto Janar na ’Yan Sanda, IGP Kayode Egbetokun, domin tabbatar da zaman lafiya a lokacin bukukuwan.
A taron, CP Bakori ya umarci jami’an da su ƙara yawan sintiri, su tabbatar da ganin ’yan sanda a fili, tare da ƙarfafa tsaro a wuraren ibada, wuraren shakatawa da manyan tituna.
Rundunar ta kuma gargaɗi jama’a da su guji tuki cikin ganganci da sauran ayyukan da ka iya tayar da hankalin jama’a.
An bukaci al’umma da su kai rahoton duk wani abu da suke zargi ga ofishin ’yan sanda mafi kusa ko ta lambobin gaggawa da aka tanada.
Kwamishinan ya gode wa al’ummar Kano bisa haɗin kai, tare da yi musu fatan bikin Kirsimeti lafiya lau da sabuwar shekara mai albarka.