29/06/2025
Da dumi'dumi: Kwankwaso ba zai wa Shugaban kasa Tinubu mataimaki ba kuma ba zai shiga jam'iyyar APC ba -Cewar NNPP
Shugabanin bangarorin biyu na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party NNPP a jihar Kano, Hashimu Dungurawa da Sanata El-Jibril Doguwa, sun yi gargadi kan jawo tsohon gwamnan jihar, Rabiu Kwankwaso, cikin muhawarar da ake yi kan wanda zai wa Shugaban kasa Bola Tinubu mataimaki a 2027.
Sun kuma yi watsi da rahoton cewa Kwankwaso na shirin sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress mai mulki.
A ’yan kwanakin da s**a gabata cece-ku-ce, da dama daga cikin manazarta siyasa ke alakanta Kwankwaso da yunkurin yin mataimakin Shugaba Tinubu a 2027.
Hasashen ya kara dagula ne a ranar Juma’a bayan murabus din da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje ya yi, wanda da yawa ke ikirarin cewa an yi shi ne don samar da fili ga Kwankwaso a sansanin Tinubu.
Duk da cewa babu wata sanarwa a hukumance daga fadar shugaban kasa ko kuma jam’iyyar APC dangane da abokin takarar Tinubu na gaba, wasu masu lura da al’amura na ganin cewa kawo Kwankwaso cikin wannan tsari na daga cikin dabarun da Tinubu zai bi wajen samun kuri’u a yankin Arewa maso Yamma a 2027.
Sai dai a wata tattaunawa daban-daban da s**a yi da ‘yan jaridu a ranar Asabar, makusantan Kwankwaso sun yi gargadi kan cece-kucen da ake yi kan abokin takarar Tinubu.
Sun yi nuni da cewa, duk da cewa shugaban nasu ya cancanci tikitin takarar mataimakin shugaban kasa, amma tada batun a wannan lokaci na iya haifar da dambarwar siyasa a sassan kasar.