Dagiya online news

Dagiya online news For a better tomorrow

Ɗan Takarar Gwamnan Jihar Kano A Ƙarƙashin Jam'iyyar ADP Malam Sha'aban Ibrahim Sharaɗa Tare Da Mawaƙin Siyasar Nan Alha...
02/09/2022

Ɗan Takarar Gwamnan Jihar Kano A Ƙarƙashin Jam'iyyar ADP Malam Sha'aban Ibrahim Sharaɗa Tare Da Mawaƙin Siyasar Nan Alhaji Dauda Kahutu Rarara Sun Ziyarci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Yau Juma'a

Dagiya online news

Yadda aikin rusau ke gudana a kasuwar Kantin Kwari bayan umarnin Gwamna Ganduje.📸 Dagiya online news
02/09/2022

Yadda aikin rusau ke gudana a kasuwar Kantin Kwari bayan umarnin Gwamna Ganduje.

📸 Dagiya online news

Kabilar da mata ke yanke yatsansu guda a duk sanda masoyinsu ya mutu, A Ƙabilar Dani, Da Ke Ƙasashen Indonesia Da Pupua ...
02/09/2022

Kabilar da mata ke yanke yatsansu guda a duk sanda masoyinsu ya mutu,

A Ƙabilar Dani, Da Ke Ƙasashen Indonesia Da Pupua Guinea, Mata Su Na Da Wata Al'ada, Duk Lokacin Da Wani Masoyinsu Ya Mutu Sai Sun Yanke Ɗan Yatsa Daya.

Yan Matanmu na nan masu dan karen farin jini da an sha gundulmi🤣

Dagiya online news

Kungiyar Fatih Karagumruk ta Turkiya ta soke kwantiragin Ahmad Musa Kaptin ɗin super Eagles, Daga Mustapha MusaYanzu dai...
02/09/2022

Kungiyar Fatih Karagumruk ta Turkiya ta soke kwantiragin Ahmad Musa Kaptin ɗin super Eagles,

Daga Mustapha Musa

Yanzu dai Ahmad Musa bashi da kungiya kenan

Dagiya online news

Sheikh Dahiru Bauchi: Malamin Da Ya Fi Kowa Yawan Zuri’ar Mahaddata Alkur’ani A DuniyaDaga Aminiya 2/9/2022 ✍️.Fitaccen ...
02/09/2022

Sheikh Dahiru Bauchi: Malamin Da Ya Fi Kowa Yawan Zuri’ar Mahaddata Alkur’ani A Duniya

Daga Aminiya 2/9/2022 ✍️.

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya kafa tarihin zama mutumin da ya fi kowa yawan zuri’ar da ta haddace Alkur’ani a tarihin duniya.

Alkaluma sun nuna cewa shehin malamin, wanda a kwanan nan ya cika shekara 98 a duniya — ranar 2 ga watan Almuharram 1444 Hijiriyya — yana da ’ya’ya da jikoki da ma tattaba-kunne kusan 300 da s**a haddace Alkur’ani.

A cewar kundin tattara bayanai na Cholan Book Of World Records, wadanda s**a karrama malamin da lambar yabo, Sheikh Dahiru Bauchi shi ne mutum na farko da ya taba samun irin wannan baiwar.

Bayanai sun nuna mashahurin malamain yana da ’ya’ya 95 da jikoki 406 da tattaba-kunne 100. Daga cikin wannan adadin, ’ya’yansa 77 da jikoki 199 da kuma tattaba-kunne 12 ne s**a haddace Alkur’anin

Yana daga cikin Halifofin Sheikh Inyass

Sheikh Darihu Bauchi ne daga cikin halifofin Shehu Ibrahim Inyass, Halifan Darikar Tijjaniyya, bayan wanda ya assasa ta, wato Sheikh Ahmadu Tijjani.

Yana daga cikin manyan malaman Musulunci a Najeriya, shi ne Mataimakin Shugaban Majalisar Koli da ke bayar da Fatawar Musulunci a Najeriya sannan babban jigo ne a Darikar Tijjaniya a Najeriya da ma Afirka.

A zantawarsa da ’yan jarida shekarun baya a Bauchi, Sheikh Dahiru ya ba da takaitaccen tarihinsa, inda ya ce, “Tarihina dai ni Bafulatani ne, dukanin kakannina hudu Fulani ne, domin kowane mutum yana da kakanni hudu — ta wajen mahaifinsa biyu, ta wajen mahaifiyarsa biyu.

To ni dukanin kakannina Fulani ne babu inda muka hadu da wata kabila ta kowace fuska. Mu Fulanin Bauchi ne a lokacin da Jihar Bauchi take hade da Jihar Gombe.

“Bayan da aka raba Jihar Bauchi da Jihar Gombe, sai muka zama mu Fulanin Jihar Bauchi ne, a lokaci guda kuma Fulanin Jihar Gombe ne.

Ta wajen mahaifina ni Bafulatanin Jihar Bauchi ne, ta wajen mahaifiyata ni Bafulatanin Nafada ne da ke Jihar Gombe

Dagiya online news

DA-DUMI-DUMINSA :Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya sha ruwan duwatsu a jihar KogiWasu fusatattun matasa ƴan jami’yyar NNPP...
01/09/2022

DA-DUMI-DUMINSA :Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya sha ruwan duwatsu a jihar Kogi

Wasu fusatattun matasa ƴan jami’yyar NNPP a jihar Kogi sun yiwa ɗan takarar shugaban Najeriya a jam’iyyar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ruwan duwatsu tare da ihun ba ma yi a lokacin da ya kai ziyara jihar kamar yadda jaridar Daily Post Nigeria ta rawaito.

Fusatattun matasan sun yi wa tawagar ɗan takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar NNPP ruwan duwatsu a lokacin da ya halarci bikin buɗe ofishin yaƙin neman zaɓensa a birnin Lokoja a jiya Laraba.

Tun da farko lokacin da Sanata Rabi’u Kwankwaso ya kai ziyara jihar Kogi, ya fara da ziyarar kabarin tsohon ɗan takarar gwamnan jihar a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar APC marigayi Alhaji Abubakar Audu da ke garin Ogbonicha, inda ya yi masa addu’a tare da ganawa da iyalansa da sauran magoya bayansa, wanda hakan ne ya fusata wasu mambobin jami’yyar NNPP da su ke zaman jiransa a birnin Lokoja.

Wasu ƴan jami’yyar da su ka zanta da manema labarai sun bayyana cewa tun da sanyin safiya su ke zaman jiransa a Lokoja, amma sai ɗan takarar shugaban ƙasar ya watsar da su tare da tafiya ga magoya bayan marigayi Abubakar Audu waɗanda s**a ce har yanzu mambobin jam’iyyar APC ne.

Sai dai jami’an tsaro sun yi ƙoƙari sun baiwa Sanata Rabi’u Kwankwaso kariya ta musamman inda su ka garzaya da shi wani Hotel da ke birnin na Lokoja.

Wani mai taimaka wa Kwankwaso kan harkokin yaɗa labarai mai suna Musa Yunusa, ya bayyana abin da magoya bayan s**a yi a matsayin al’ada a harkokin siyasa, inda ya bayyana jihar Kogi a matsayin gidan ɗan takarar shugaban kasa na NNPP.

Dagiya online news

Kawo yanzu Erling Haaland, ya zura kwallo tara a gasar Firimiya,   a dadin Lambar rigar bayansa.Shin ya dau hanyar lashe...
01/09/2022

Kawo yanzu Erling Haaland, ya zura kwallo tara a gasar Firimiya, a dadin Lambar rigar bayansa.

Shin ya dau hanyar lashe takalmin zinare kuwa?

Abbas Adam

Dagiya online news

Yau ake kyautata zaton za'ayi zama na karshe akan matsalar yajin aikin Malam Jamioin na kasa ASUU da s**a shafe Wata 8 s...
01/09/2022

Yau ake kyautata zaton za'ayi zama na karshe akan matsalar yajin aikin Malam Jamioin na kasa ASUU da s**a shafe Wata 8 suna yakin aiki .

A yayin zaman na yau zai hada da kungiyoyin iyayen Yara da bangaren ASUU da gwamnatin tarayya Wanda ba'a Saba ganin hakan ba .

Kuna ganin zaman zai zamo na karshen ne kuwa ko akwai sauran Magana ?

A kalla mutane biyu ne s**a rasa rayunka su sakamakon ruftawar wani bene mai hawa uku a ranar Talata a kasuwar GSM ta Be...
01/09/2022

A kalla mutane biyu ne s**a rasa rayunka su sakamakon ruftawar wani bene mai hawa uku a ranar Talata a kasuwar GSM ta Beirut da ke cikin birnin Kano.

Sakataren kungiyar agaji ta Red Cross ta Najeriya da ke Kano Musa Abdullahi ya ce nan take, wayar wutar lantarki ta yi sanadiyyar mutuwar wani ma'aikacin kamfanin rarraba wutar lantarki na Kano (KEDCO) a yayin yake aikin ceto.

Hakazalika, Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta tabbatar da cewa mutum daya ya mutu daga cikin mutane takwas da aka ceto.

Dagiya online news

Yadda Kaburbura sama da 200 s**a rufta a makabartar Abbatuwa=========================Damunar bana ba wai gidaje da kasuw...
01/09/2022

Yadda Kaburbura sama da 200 s**a rufta a makabartar Abbatuwa
=========================
Damunar bana ba wai gidaje da kasuwanni ta yiwa barna ba har da makabartu da hankalin jama'a bai kai kai ba.

A don hakan ne ake bukatar tallafin kasa da tukwane domin gyaran wadannan Kaburbura

Idan ana bukatar taimakawa sai a tuntubi wannan lambar 09039612552 ta masu hakan kabari ce

Address

Dala Local Government
Kano
700001

Telephone

+2348101632004

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Dagiya online news posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Dagiya online news:

Share