18/08/2025
🕌 Akidar Ahlus-Sunna: Gaskiya, Ilimi da Adalci
Ahlus-Sunna ba wata kungiya ce kawai ba, akida ce ta gaskiya wacce duk musulmi ya hau kan ita idan yana bin Allah da ManzonSa ﷺ.
⚠️ Ka sani: Duk wanda bai da ilimi akan wani abu, ya kyautu ya daina kafurta abu ko halarta shi, domin Annabi ﷺ ya ce:
> “Duk wanda ya yi magana ba da ilimi ba, to laifin nasa a kansa yake.”
(Musnad Ahmad)
🔹 Akwai wasu suna cewa Izala kafurci ce — amma wannan ba gaskiya ba ne.
Izala ba wani sabon addini ba ne, ma’anar sa ita ce:
“Kawarda bidi’a da tsada Sunna.”
Wato duk inda aka ga an aikata bidi’a, a tabbatar da Sunna ta Manzon Allah ﷺ. Wannan kuwa aikin duk wani musulmi ne, ba na wata kungiya kadai ba.
Allah Madaukaki Ya ce:
> “Duk abin da Manzon Allah ya baku ku ɗauka, kuma abin da ya hanaku ku guje shi.”
(Suratun Hashr: 7)
Manzon Allah ﷺ ya kuma ce:
> “Duk wanda ya ga wani abu daga mummunan aiki, to ya canza shi da hannunsa; idan bai iya ba, to da harshensa; idan bai iya ba, to da zuciyarsa, wannan shi ne mafi rauni na imani.”
(Sahih Muslim)
🔹 To idan kai musulmi ne, kuma ka yarda cewa kawarda bidi’a da tsada Sunna dabi’a ce mai kyau, sannan kai ma kana aikata hakan — to kai ma Dan Izala ne.
✅ Abin da ya wajaba gare mu shi ne mu daina zagin juna, mu guji kiran musulmi kafiri ba tare da hujja ba. Domin duk wanda yake bin Allah da ManzonSa da gaskiya, to shi ma Dan Ahlus-Sunna ne.
Allah Ya ce:
Kada ku rarrabe ku zamanto bangarori daban-daban, ku tuna ni’imar Allah a kanku.”
(Suratun Ali-Imran: 103)
✨ Sakonmu shi ne:
Ahlus-Sunna akida ce ta bin Al-Qur’ani da Sunna, ba kungiya da za a zagi ba. Mu rike gaskiya da ilimi, mu guji jahilci da kafurta mutane.
Izala ba kafurci bace, izala tsada Sunna ce da kawarda bidi’a.