12/05/2026
Atiku Ya Caccaki Matakan Tsaron Tinubu Bayan Rasuwar Tsohon Dan Majalisa a Hannun ’Yan Bindiga
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya caccaki matakan tsaron gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu bayan rasuwar tsohon ɗan Majalisar Wakilai, Hon. Abba Adamu, a hannun masu garkuwa da mutane.
Rahotanni sun bayyana cewa an sace marigayin ne a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna a ranar 3 ga watan Mayu, sannan ya rasu bayan kwana tara yana hannun ’yan bindiga duk da ƙoƙarin da iyalansa s**a yi na ganin an sake shi.
A cikin wata sanarwa da Babban Mataimakinsa na Musamman kan Hulɗa da Jama’a, Phrank Shaibu, ya fitar a Abuja, Atiku ya bayyana lamarin a matsayin wata babbar alama da ke nuna yadda matsalar rashin tsaro ke ƙara ta’azzara a Najeriya.
Ya ce ci gaba da kashe-kashe da sace mutane na nuna cewa gwamnati ta gaza kare rayuka da dukiyoyin al’umma, yana mai kira ga gwamnatin tarayya da ta ɗauki matakan gaggawa domin magance matsalar tsaro a ƙasar.