Kwallon kafa News

Kwallon kafa News Zamu na kawo muku labarai da Dumi Dumin su kama da na gida da waje, tarihi, sakamakon wasanni, DS....

Amadadin Kwallon ƙafa News muna taya PSG murnar lashe kofin zakarun turai na biyu a jere 2025/2026Kuna ganin shekara mai...
30/05/2026

Amadadin Kwallon ƙafa News muna taya PSG murnar lashe kofin zakarun turai na biyu a jere 2025/2026

Kuna ganin shekara mai zuwa zasu iya sake tafiya dashi????

Tunda nake kallon Madrid ko livescore na duba naga an cimu sai naji ba dadi amma wlh a wannan lokacin duk yan wasanmu su...
10/05/2026

Tunda nake kallon Madrid ko livescore na duba naga an cimu sai naji ba dadi amma wlh a wannan lokacin duk yan wasanmu sun ciremun wannan kishin, (Inji wani Fans ɗin Madrid)

Ina magoya bayan Madari kuma haka abun yake???

Muna taya Barcelona murnar ɗaukar gasar Laliga ta bana 2025/2026, Ƴan Barca kuna ganin a nan kusa zaku kamo Madari???Hau...
10/05/2026

Muna taya Barcelona murnar ɗaukar gasar Laliga ta bana 2025/2026,

Ƴan Barca kuna ganin a nan kusa zaku kamo Madari???

HausaFootball

A halin yanzu, Real Madrid ta dage kan samun mai horas war da zai iya sanya Vinicius Junior, Kylian Mbappe da Jude Belli...
05/05/2026

A halin yanzu, Real Madrid ta dage kan samun mai horas war da zai iya sanya Vinicius Junior, Kylian Mbappe da Jude Bellingham a tawaga ɗaya kuma su yi aiki tare. Matsayar ƙungiyar har yanzu bata sauya ba: dukkan ƴan wasa ukun suna da muhimmanci a kakar wasa mai zuwa, don haka babu wanda zai tafi.

Babban aikin farko na sabon mai horaswar da zai zo shine gina tawagar ƙungiya mai ƙarfi tare da ƴan wasan da suke cikin Real Madrid a halin yanzu. Real Madrid na da manufa ɗaya bayyananniya ne kawai: Ƙarawa Kylian Mbappe ƙaimi domin ya cika abun da ake sanya masa rai a ƙungiyar don ci gabanta.

Shi kansa Mbappe an rahoto cewa ya fahimci akwai buƙatar abubuwa su sauya. Duk da ƙalubalen da yake fuskanta na ƴan kwanakin nan, Real Madrid na da kwarin gwiwar cewa Vinicius Junior da Mbappe zasu iya taka rawar gani a tare. Yanzu ƙungiyar ta mayar da hankali kacokan kan naɗa mai horaswar da zai iya taimakawa waɗannan ƴan ukun su yi aiki kuma su samu nasara a Real Madrid.

Kwallon kafa News

Real Madrid tana da cikakken kwarin gwiwa kan Jude Bellingham, Kylian Mbappé da Vinícius Júnior, waɗanda za su zama many...
05/05/2026

Real Madrid tana da cikakken kwarin gwiwa kan Jude Bellingham, Kylian Mbappé da Vinícius Júnior, waɗanda za su zama manyan jiga-jigan kungiyar a kakar wasa mai zuwa.

Kungiyar ta yi imanin cewa sabon kocin da zasu naɗa zai sanya su yin aiki tare da gina ƙungiya mai ƙarfi a tare da su. [Diario AS]

Kwallon kafa News

An tabbatar: Hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Sifaniya ba za ta bari akai kofin gasar La Liga ya kasance a Camp Nou a ranar...
05/05/2026

An tabbatar: Hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Sifaniya ba za ta bari akai kofin gasar La Liga ya kasance a Camp Nou a ranar Lahadi ba yayin fafatawar wasan hamayyar El Clásico, koda kuwa Barcelona tayi nasarar wasan 🇪🇸🏆

Barçelon za ta karɓi kofin gasar a wasan ƙarshe na kakar wasa ta bana.

Kwallon kafa News

🗣️ Endrick game da makomarsa: "Ina farin ciki a nan... Idan dole ne na koma Real Madrid, zan koma, Amma idan dole ne na ...
04/05/2026

🗣️ Endrick game da makomarsa: "Ina farin ciki a nan... Idan dole ne na koma Real Madrid, zan koma, Amma idan dole ne na zauna a Lyon, zan zauna."

"Gaskiya dai, ina son na zauna a nan Lyon. Suna yin duk abin da za su sa ni jin daɗi."

Kwallon kafa News

Abu ne mawuyaci Eduardo Camavinga ya samu shiga tawagar Didier Deschamps ta France a gasar cin kofin duniya mai zuwa, ra...
03/05/2026

Abu ne mawuyaci Eduardo Camavinga ya samu shiga tawagar Didier Deschamps ta France a gasar cin kofin duniya mai zuwa, rahoton Téléfoot.

A halin yanzu ɗan wasan tsakiyar yana bayan waɗannan ƴan tsakiyar cikin jadawalin da ake sa ran zai bayyana:

- Manu Koné
- Aurélien Tchouameni
- Adrien Rabiot
- Warren Zaïre-Emery
- Ngolo Kanté

Kwallon kafa News

Tun lokacin da Lionel Messi ya koma Inter Miami:Ya buga wasanni 100Ya zura kwallaye 86Ya bayar da taimako 44Kwallaye da ...
03/05/2026

Tun lokacin da Lionel Messi ya koma Inter Miami:

Ya buga wasanni 100
Ya zura kwallaye 86
Ya bayar da taimako 44

Kwallaye da taimakawa 130 a wasanni 100 da ya buga.

Kwallon kafa News

Kylian Mbappe shi da shalelen sa Ester Exposito suna cigaba da sararawa a Italiya. 🏖️Kwallon kafa News
03/05/2026

Kylian Mbappe shi da shalelen sa Ester Exposito suna cigaba da sararawa a Italiya. 🏖️

Kwallon kafa News

Address

Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kwallon kafa News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Kwallon kafa News:

Share