RG online tv

RG online tv Gaskiya da Gaskiya

An yi bikin bude wasannin Ma'aikatan jami'o'in Najeriya, da jami'ar Bayero ke karbar bakunci.Bikin bude wasannin gasar, ...
26/05/2025

An yi bikin bude wasannin Ma'aikatan jami'o'in Najeriya, da jami'ar Bayero ke karbar bakunci.

Bikin bude wasannin gasar, ya gudana a ranar Asabar a filin wasa na sabuwar Jami'ar Bayero, da wakilai, yan wasa da masu horarwa na jami'o'in kasar nan sama da dubu s**a halarta.

Ana sanar za a shafe mako guda a na fafatawa a wasanni daban-daban, kuma akalla jami'o'in Najeriya 35 zasu fafata a tsakaninsu.

Haka zalika a wasan kwallon kafa wanda shi ne mabudin gasar Jami'ar Bayero ta buga kunnan doki da jami'ar Gusau da ke jihar Zamfara.

DA ƊUMI-ƊUMI: 'Yan Sandan Kano Sun Tabbatar Da Rasuwar DPO'n RanoRundunar 'yan sandan jihar Kano ta tabbatar da rasuwar ...
26/05/2025

DA ƊUMI-ƊUMI: 'Yan Sandan Kano Sun Tabbatar Da Rasuwar DPO'n Rano

Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta tabbatar da rasuwar DPO'n Rano bayan wasu fusatattun matasa sun farwa Ofishin 'yan sandan bisa zarginsa da harbin wani matashi.

Kakakin rundunar 'yan sandan, Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da rasuwarsa a wata sanarwar da ya fitar a daren Litinin.

Ya ce tuni an k**a mutane 27 da ake zargi da hannu a cikin lamarin, tare da tabbatar da dawo da zaman lafiya a yankin na Rano.

Innalillahi Wa'inna Ilaihirrajiun. Shugaban kaffar yada labarai ta RG online tv and radio station Usman Alasan Ruwan God...
23/03/2025

Innalillahi Wa'inna Ilaihirrajiun.

Shugaban kaffar yada labarai ta RG online tv and radio station Usman Alasan Ruwan Godiya yana mika sakon ta'aziyya ga gwamnan jihar Katsina Mal. Dikko Umaru Radda bisa rasuwar Mahaifiyar sa.

Tare da rokon Allah ya gafarta mata ya bama yan uwa da abokan arziki hakurin wannan rashi, Allah kuma ya gafarta mata dukkan musulmin da s**a rasu alfarmar wannan wata da muke ciki Amin.

Tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari Ya Karɓi Bakuncin Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai A Gidansa Dak...
07/03/2025

Tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari Ya Karɓi Bakuncin Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai A Gidansa Dake Kaduna, Yau Juma'a

Labarin Siyasa Jam’iyyar APC ta ƙasa ta naɗa Dr. Ibrahim Shehu Shema CON, a matsayin shugaban kwamitin tantance zaɓen gw...
07/03/2025

Labarin Siyasa

Jam’iyyar APC ta ƙasa ta naɗa Dr. Ibrahim Shehu Shema CON, a matsayin shugaban kwamitin tantance zaɓen gwamnan jihar Anambra a 2025.

Muna taya shugabanmu murna

Inna LillaHi Wa Inna IlaiHi RajiunAl'ummar garin Tafoki na bukatar ɗaukin gaggawa tare da addu'o'inku, ƴan bindiga sun s...
25/02/2025

Inna LillaHi Wa Inna IlaiHi Rajiun

Al'ummar garin Tafoki na bukatar ɗaukin gaggawa tare da addu'o'inku, ƴan bindiga sun sa su tsakiya yanzun haka

A kabaran dake shigo Wa Katsina Daily News yanzun cikin daran nan a yankin garin Tafoki ta ƙaramar hukumar Faskari abin ba daɗi

Ga abin da wani dan garin Sani Yahaya Maido ya wallafa

"Tafaru takare daukin da muke ta Nema Tafoki yau barayi Sama da mashin 500 sun kewayemu yanzu suna cin karesu ba habbaka
😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭"

Wani mazauni garin da ta tabbatar wa Katsina Daily News faruwar lamarin, ya ce yanzun haka ƴan bindigar sun fita garin, sai dai sun kashe rayuwa da kwasar mutane tare da kore dabbobi, daga cikin wadanda s**a rasa ran nasu har da kanin Sani Yahaya Maidomar

Waiwaye; Ko kun san cewa NRC ta Bashir Tofa ita ta lashe zaben shugaban kasa na June 12 1993 a jihar Katsina? Sai dai du...
21/02/2025

Waiwaye; Ko kun san cewa NRC ta Bashir Tofa ita ta lashe zaben shugaban kasa na June 12 1993 a jihar Katsina?

Sai dai duk da Tofa dan Kano ne, amma bai ci jihar Kano da Jigawa ba a lokacin

Ga yadda zaben shugaban kasa na June 12 1993 da aka tsakanin Bashir Tofa na NRC da Abiola na SDP a wasu jihohin ƙasar nan

Abuja (FCT)
Tofa 18,313
Abiola 19,968

Abia
Tofa 151,227
Abiola 105,273

Adamawa
Tofa 167,239
Abiola 140,875

Akwa Ibom
Tofa 199,342
Abiola 214,787

Anambra
Tofa 159,258
Abiola 212,024

Bauchi
Tofa 524,836
Abiola 339,339

Benue
Tofa 186,302
Abiola 264,830

Borno
Tofa 128,684
Abiola 153,496

Cross River
Tofa 153,452
Abiola 189,303

Delta
Tofa 145,001
Abiola 327,277

Edo
Tofa 103,572
Abiola 205,407

Enugu
Tofa 284,050
Abiola 263,101

Imo
Tofa 195,836
Abiola 159,350

Jigawa
Tofa 89,836
Abiola 138,552

Kaduna
Tofa 356,860
Abiola 389,713

Kano
Tofa 154,809
Abiola 169,619

Katsina
Tofa 271,077
Abiola 171,162

Kebbi
Tofa 144,808
Abiola 70,219

Kogi
Tofa 265,732
Abiola 222,760

Kwara
Tofa 80,209
Abiola 272,270

Lagos
Tofa 149,432
Abiola 883,865

Niger
Tofa 221,437
Abiola 136,350

Ogun
Tofa 59,246
Abiola 425,725

Ondo
Tofa 162,994
Abiola 883,024

Osun
Tofa 72,068
Abiola 365,266

Oyo
Tofa 105,788
Abiola 536,011

Plateau
Tofa 259,394
Abiola 417,565

Rivers
Tofa 640,973
Abiola 370,578

Sokoto
Tofa 372,250
Abiola 97,726

Taraba
Tofa 64,001
Abiola 101,887

Yobe
Tofa 64,061
Abiola 11,887

Abiola na SDP shi ne ya lashe zaben da shugaban kasa na zamanin IBB ya kashe zaben, sai dai a jiya Alhamis IBB ya ce ya yi ladamar yin hakan inda ya ce da yana da dama a yanzun da ya ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben

  Wata mummunar gobara ta afkawa kauyen Zago da ke karamar hukumar Dambatta a jihar Kano a ranar Laraba, inda ta yi sana...
06/02/2025



Wata mummunar gobara ta afkawa kauyen Zago da ke karamar hukumar Dambatta a jihar Kano a ranar Laraba, inda ta yi sanadin konewar dabbobi, gidaje, da rumbunan abinci.

Wani ganau mai suna Laminu Sani ya tabbatar wa Arewa Radio faruwar al’amarin, inda ya ce har yanzu ba a san musabbabin tashin gobarar ba.

Laminu Umar ya kara da cewa gobarar wadda ta fara bayan karfe 9 na safiyar jiya Laraba ta kai karfe 4 na yamma tana ci saboda rashin kyawun hanya ga Jami’an kashe gobara da kuma rashin ruwa.

Dagacin kauyen Yunusa Isma’il shi ma ya tabbatar da faruwar al’amarin, inda ya yi kira ga Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya kai dauki cikin gaggawa ga wadanda gobarar ta shafa.

Allah Ya karɓi rayuwar Alula-Ɗanhaya ɗan asalin garin Funtua mai tallar magani yana wasa da keke rasuwa a yauKamar yadda...
06/02/2025

Allah Ya karɓi rayuwar Alula-Ɗanhaya ɗan asalin garin Funtua mai tallar magani yana wasa da keke rasuwa a yau

Kamar yadda Katsina Daily News ta samu marigayin ya rasu a daran jiya wayewar garin yau, a unguwarsu dake Nasarawa cikin garin Funtua jihar Katsina, za kuma a yi zanaidarsa da wajen misalin goma na safiyar nan.

Marigayin mai suna Jibrin da aka fi sani da Baba Alula Dan Haya, ya yi suna sosai a kasuwannin ƙauye da na birni, inda yake zuwa kasuwannin yana wasa da keke, ya sarrafa shi ko ba taya, sannan keke duk yadda ya kasance yana iya tuka shi, walau ba iska, ko ba taya ko ma da kafa ɗaya

Allah Ya ji kansa Ya sa ya huta amin

Ƙungiyar Tafiyar Matasa Za Ta Shirya Gagarumar Gasar Wasan Kwallon Kafa A Tsakanin Matasa Tare Da Bada Kyaututtuka A Jih...
12/12/2024

Ƙungiyar Tafiyar Matasa Za Ta Shirya Gagarumar Gasar Wasan Kwallon Kafa A Tsakanin Matasa Tare Da Bada Kyaututtuka A Jihar Katsina

Ƙungiyar Tafiyar Matasa za ta shirya gasar wasan ƙwallon ƙafa tsakanin ƴaƴan ƙungiyar da ke faɗin ƙananan hukumomi 34 na Jihar Katsina. Inda za'a fara gasar wasan ƙwallon daga ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2025, inda za'a yi wasa na ƙarshe na wasan a ranar 1 ga watan Fabrairu.

Shugaban Ƙungiyar Tafiyar Matasa na Jihar Katsina Hon. Abdulrazak Ɗahiru Kaita ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabin shirye-shiryen da tsare-tsaren yadda za'a gudanar da gasar a tsakanin ƙananan hukumomi 34 na Jihar Katsina.

Taron ya gudana a ɗakin taro na Service To Humanity da ke gidan Dawa tare da halartar shugabannin na Jihar Katsina.

A cewar Hon. Abdulrazak Ɗahiru Kaita, za'a gudanar da gasar wasan ƙwallon ƙafa a faɗin ƙananan hukumomi tare da fara zaɓar rukunin mutum 16 wanda sune za'a fafata da su a matakin jiha.

Shugaban Ƙungiyar ya ƙara dacewa, duk ƙungiyar ƙwallon ƙafa da ke son shiga cikin gasar za ta rajistar shiga. Ya yabawa shugabannin Ƙungiyar kan hangen nesan su na fitowa da batun yin gasar wanda zai kawo haɗin kai a tsakanin Matasa.

Sauran waɗanda s**a yi jawabi a lokacin taron, sun bayyana fatan cewa tabbas gasar wasan ƙwallon ƙafa zai kawo cigaba da sanin juna a tsakanin mambobin ƙungiyar.

Saurayina Yace Idan Ban Bashi Kaina Ba Zai Koma Bin Karuwai Da Shaye-shaye, Dan Allah Ƴan Uwa Ku Bani Shawara, Cewar Wat...
25/11/2024

Saurayina Yace Idan Ban Bashi Kaina Ba Zai Koma Bin Karuwai Da Shaye-shaye, Dan Allah Ƴan Uwa Ku Bani Shawara, Cewar Wata Budurwa

Saurayina ne ya ke kawo min wasu tsari akan duk lokacin da yazo gidan mu na amince masa da bukatarsa, to ni kuma naƙi yarda yace indai naƙi wallahi zai bi karuwai a waje ya koma shaye-shaye dama majority ɗin abokan sa shi sukeyi Allah ne dai yasa shi bayayi.

Amma yace tunda naƙi amincewa da shi ba abinda bazai sha ba, kuma karuwai zai koma bi.

Dan Allah ƴan uwa nasan dai bazan amince masa ba, amma ya kuke gani zanyi domin hana shi faɗawa halaka?

Nadoge!

Yin alwala har sau biyar a kullum shi ya sa na ji ba zan iya yin addinin Musulunci ba, duk da na taso cikin Musulunci - ...
01/10/2024

Yin alwala har sau biyar a kullum shi ya sa na ji ba zan iya yin addinin Musulunci ba, duk da na taso cikin Musulunci - Inji Idris Okuneye da aka fi sani da Bobrisky

A wata hira da Jaridar Vanguard ta taba yi da shi a can shekarun baya ya bayyana cewa shi duk da yana gidan Musulunci, amma yanayin rayuwar da ya dakko ba su yi daidai da ta addin musulmai ba

"In kana addinin Musulunci dole ne ka yi alwala sau biyar a duk kullum domin yin sallah, duk lokacin da na yi alwala dole na canza ƙwalliya ta, don haka ka ga a duk rana sai na yi kwalliya sau biyar kenan, shi ya sa bar addinin, na kuma canza suna daga Idris da aka rana mani a Musulunci na koma Olanrewaju, wanda ba kowa ne zai gane cewa ni Musulmi ne ko kirista a sunan ba"

Address

Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when RG online tv posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to RG online tv:

Share

Category