JAUHAR TV

JAUHAR TV 📺 JAUHAR TV🎙️ Labaran Duniya | Siyasa | Tattaunawa da Manya📍 Daga Arewacin Najeriya zuwa duniya 🇳🇬📩 Tuntube mu don Talla / ko Aikatau👇08067329787

Kungiyar Renewed Hope Project 2027,Reshen Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙungiyar, Hon. Ibrahim Sa’id Warawa,...
19/09/2026

Kungiyar Renewed Hope Project 2027,Reshen Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙungiyar, Hon. Ibrahim Sa’id Warawa, ta kai ziyarar girmamawa ga PRO na Jam’iyyar APCn Kano, Hon. Auwalu soja Sani Mainage.

A yayin tattaunawar, ɓangarorin biyu sun yi duba mai zurfi akan muhimman batutuwa da s**a shafi ci gaban Jam’iyyar APC.

Haka zalika, an binciki hanyoyin ƙarfafa haɗin kai da samar da dabarun siyasa na zamani da za su tabbatar da nasarar Mai Girma Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Mai Girma Gwamnan Jihar Kano da ma jam'iyyar APC baki ɗaya a dukkan matakai.

Wannan ziyara na ɗaya daga cikin jerin matakai na tuntuɓa da ƙungiyar ta sa a gaba domin gina gagarumin fage na samun nasara a zaben da ake tunkara a 2027.

Allah Ya haɗa kanmu, Ya ba mu nasara, Ya kuma albarkaci ƙoƙarinmu. Amin.

Sanarwa Daga: Hon. Sadiya Ibrahim Sheka Darakta Janar matakai.Wannan Sada Zumunta:

19/09/2026
Shugaban Matasan APC na Jihar Kano, Hon. Salisu Yahaya Hotoro, Ya Karɓi Bakuncin Kungiyar 'Renewed Hope Project 2027' Ƙa...
19/09/2026

Shugaban Matasan APC na Jihar Kano, Hon. Salisu Yahaya Hotoro, Ya Karɓi Bakuncin Kungiyar 'Renewed Hope Project 2027' Ƙarƙashin Jagorancin Hon. Ibrahim Sa'id Warawa

A jiya, Shugaban Matasan Jam’iyyar APC na Jihar Kano, Hon. Salisu Yahaya Hotoro, ya karɓi bakuncin shugabanni da membobin ƙungiyar fafutukar siyasa ta 'Renewed Hope Project 2027' reshen Jihar Kano a ofishinsa.Ziyarar, wadda aka gudanar ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙungiyar na Jihar Kano, Hon. Ibrahim Sa'id Warawa, ta mayar da hankali ne kan tattauna muhimman batutuwa da s**a shafi ci gaban matasa da kuma hanyoyin ƙarfafa tsarin tafiyar jam'iyyar APC daga matakin gida zuwa na tarayya.

Yayin tattaunawar., on. Salisu Yahaya Hotoro ya nuna gamsuwar sa da irin ayyukan da ƙungiyar ke yi ƙarƙashin jagorancin Hon. Ibrahim Sa'id Warawa wajen wayar da kan al'umma game da manufofin nasara na jam'iyyar APC. Ya kuma jaddada jinjina da mahimmancin haɗin kan matasa wajen tabbatar da nasarar tafiyar a Jihar Kano.

DG MEDIA RENEWED HOPE PROJECT 2027
HON. SADIYA IBRAHIM SHEKA.

Address

NO 257 KANKAROFI KMC
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when JAUHAR TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share