28/05/2024
KEDCO SUN TASHI HAIƘAN SAI SUN KASHE KANO.
Wannan rubutun na duk wani wanda ke zaune a Kano ne. Musamman waɗanda ke da business dake buƙatar wutar Lantarki.
A wannan satin hankalina ya tashi da na samu sahihin labarin cewa duk wata ana baiwa Kano wutar lantarki 300 megawat ne, amma saboda zalunci sai KEDCO su ce ta yi musu yawa megawat 60 ko 70 zasu iya raba wa. sai su zo su rinƙa yi mana mulkin mallaka da ita, a san wa waccan unguwa ta 'yan mintuna, a baiwa wasu ta 'yan awowi, sun ƙi su yarda da mitar Pay As You Go sai dai su rinƙa bi gida gida suna karɓar harajin da aljihunsu kaɗai yake shiga. Kuma abin taƙaicin shi ne, a jikin wutar 60 megawat duk wata sai sun yi mana fashin rana-tsaka sun karɓe mana kuɗaɗen da sun fi na 300 megawat ɗin.
Ya k**ata fa mu farka, businesses a Kano kullum mutuwa suke yi, kamfuna da dama sun tashi sun bar Kano, wasu sun koma Kudu wasu sun koma Ghana. idan muka dubi ƙananan sana'o'inmu irin su Business Centres, da sana'ar ɗinki da sana'ar kafintanci, da sana'o'i irin na niƙa da markaɗe da masu shaguna dake sayar da kayan sanyi dangin ruwa da lemo, da masu sana'ar walda da dai sauran sana'o'i da dama masu amfani da wutar lantarki. Duk an kassara waɗannan sana'o'in.
Business ba zai yiwu da Generator ba, musamman a wannan zamanin na tsadar fetur.
Tun da ga iyayen gidanmu sun koya mana yadda ake jajircewa lallai ya k**ata mu yi koyi. Sarakuna biyu a Kano, kuma kowanne ya zage yana kare haƙƙi da ra'ayin sa bilhaƙƙi da gaskiya, to gaskiya mu ma ya k**ata mu fito mu kare namu haƙƙin ta hanyar yayata wa duniya har sai maganar ta je kunnen waɗanda ya k**ata su ɗauki mataki. Na san zaku ce idan ma mun yi magana a banza, kada mu karaya, kowa ya fito ya yi rubutu akan wannan zaluncin, kada mu ɗaga ƙafa, mu yi ta damun su har sai kowa ya gane zaluncin da suke yi mana. Domin idan bamu yi magana ba, babu wanda zai yi magana a madadin mu.
Abubuwa da yawa na faruwa ga talaka ne saboda shiru ɗinmu ya yi yawa.
Babinlata