13/09/2025
Yana tafiya tare da matarsa a mota, suna ta cacar baki, har ta kai g yana cin mutuncinta, yana zaginta
Suna cikin wannan hali, sai ga Jami'an kula da T**i da kuma kiyaye haɗura sun tare su.
Jami'i: Me yasa kake gudu fiye da 200km/hr..?
Miji: A'a Yallabai, a 100km/hr nake tafiya!
Mata: Sam yallabai a 200 yake tafiya, ni shedata ce
Miji: Ya kalli matar a fusace ya jijjiga kai.
Jami'i: Ina takardun motarka..?
Miji: Ya ɗan yi dube-dube. Na baro su a gida!
Mata: Yallabai asalin motar bata da takardu!
Miji: Ya kalleta ya doka mata harara!
Jami'i: Baka ɗaura 'seat belt' ba!
Miji: Yallabai da ka tsayar da ni ne na cire.
Mata: Wallahi tun da muka taho baka ɗaura ba.
Miji: Ya kalli matar ya buga mata tsawa, ki rufe baki
Jami'i: Haka dama yake miki tsawa..!?
Mata: A'a yallabai, in yana cikin mayene yake yin hk
Jami'i: Abokina ashe a buge kake kuma kake tuƙi!?
Miji: Kar ka yadda, ƙarya take.
Mata: Duk da baka saci wannan motar ba da mun tafi gida asirinmu a rufe!
Jami'i: Au abokina motar ma sato ta ka yi...!
Miji: A'a! A'a!! Wallahi kar ka yadda da ita. In kika sake magana sai na sake ki saki uku.
Jami'i: Duk lokacin da kuka samu sabani sai ya ce zai sake ki..!?
Mata: Yallabai ya bari a yi auren ma tukunna b***e y fara zancen saki.
Idan kaine mijin ya zakayii 🤣???