22/06/2024
JIHAR KANO A YAU
Haqiqa al'amuran dake faruwa kuma ke cigaba da kakawo a Jihar Kano abin bakin ciki da takaici ne.
Wannan wayannan hanyoyi da ake bi, hanyoyi ne wayanda zasu cigaba da kawo mana tasgaro da koma baya a matsayin Jihar mu datayi shura a fannin kasuwanci, zaman lafiya da ilimin addini hadida mulkin masarautu a fadin na hiyar africa.
Tsaron Lafiya da dukiyoyi a Jihar Kano abin yana so ya huce gona da iri, kamar yarda Rahotonni suke fitowa na tashe tashen hankula da fadan daba dama shaye-shaye da fataucin muyagun kwayoyi ke neman samun gin din zama a Jihar mu.
A saboda haka muna kira da kwarkwarar murya da gwamnatin Tarayyar Najeriya data barranta kanta daga dukkan abubuwan dake faruwa a Jihar nan.
A kuma tabbatar da cewa doka da order tayi aiki akan kowa.
Cigaban Jihar Mu, zaman Lafiyar Mu Da dawwamuwar arzikin mu shine mafi a'ala Agaremu fiye da komai.
Muna Rokon Allah daya bamu Lafiya da Zama Lafiya.
Allah Kuma Ya tsare mana mutuncin mu, Imanin Mu dakuma addinin mu Ameen.