Hauwa Live

Hauwa Live Hauwa live � Your daily dose of happiness

14/09/2026

Babu wanda zai sake zabar Gwamnatin jahar kano inji Dan Bilki.

Abdulmajeed Almustapha Kwamanda

13/09/2026

Martani daga bakin Dan Bilki kwamanda .

Abdulmajeed Almustapha Kwamanda

08/09/2026

Idan da waiya babu wayyo Allah.

27/08/2026

Mai Girma Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, PhD, FNSE, Dan Takar Mataimakin Shugaban Ƙasa na NDC a jiya labara 27 ga watan Agusta, 2026 yayi interview da Kano Live 24 da kuma Hauwa live hirar da a kagu danar da ita a gidansa da ke Maitama, Abuja A yayin hirar, ya tattauna kan muhimman batutuwan ƙasa tare da bayyana ra'ayinsa game da hanyar da ya kamata Najeriya tabi domin cigaba.

22/08/2026

Kungiyar dalibai ’yan asalin Jihar Kano ta kai ziyara ga Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, domin nuna goyon bayanta ga Gwamna Abba Kabir Yusuf a zaɓen 2027.

Atiku ya yaba wa al'ummar jihar Osun kan yadda s**a nuna ƙwazo wajen sake zaɓar Adeleke a matsayin GwamnaÐan takarar Shu...
16/08/2026

Atiku ya yaba wa al'ummar jihar Osun kan yadda s**a nuna ƙwazo wajen sake zaɓar Adeleke a matsayin Gwamna

Ðan takarar Shugaban Ƙasa, na jam'iyyar ADC Atiku Abubakar, ya taya Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, murnar sake zaɓensa a matsayin gwamnan jihar.

A saķon da ya wallafa, Atiku ya bayyana cewa nasarar Adeleke ta nuna zaɓin al’ummar Osun, wanda s**a bayyana ta hanyar jefa ƙuri’a a rumfunan zaɓe.

Ya kuma yaba wa al’ummar jihar bisa yadda s**a nuna ƙwazo tare da shiga zaɓen cikin lumana.

Atiku ya yi wa Gwamna Adeleke fatan samun ƙarin nasara da ci gaba da gudanar da ayyuka ga al’ummar Osun tare da hidimta musu.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya taya Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, murnar lashe zaɓen gwamnan jihar da aka gudana...
16/08/2026

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya taya Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, murnar lashe zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar ranar 15 ga Agusta, 2026.

Siyasarmu TV ta rawaito a wani saƙo da Kwankwaso ya wallafa inda ya bayyana Adeleke a matsayin abokinsa, yana mai cewa nasarar ta sake tabbatar da cewa idan al’umma s**a sauke nauyin da ke kansu na dimokuraɗiyya tare da bayyana ra’ayinsu, muradin jama’a zai yi nasara.

Ya kuma yaba wa al’ummar Osun kan yadda s**a gudanar da aikinsu na dimokuraɗiyya, tare da yabawa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) kan yadda ta gudanar da zaɓen.

Kwankwaso ya ƙara kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su ci gaba da tabbatar da zaɓuka masu inganci, zaman lafiya da gaskiya, tare da taya Adeleke da al’ummar Osun murnar nasarar.

09/08/2026

Warkal ya bayyana cewa lokacin da s**a kafa gwamnati ko kansila basu da shi kuma a haka s**a kafa wannan gwamnati dan haka a zabe maizuwa sai sunka da Abba K Yusuf.

Mun kusa kawo ƙarshen zazzabin cizon sauro a Nijeriya - Gwamnatin Tinubu Ministan lafiya da walwalar jama’a na Nijeriya,...
09/08/2026

Mun kusa kawo ƙarshen zazzabin cizon sauro a Nijeriya - Gwamnatin Tinubu

Ministan lafiya da walwalar jama’a na Nijeriya, Farfesa Muhammad Ali Pate, ya ce gwamnatin Tinubu ta ƙuduri aniyar kawo ƙarshen zazzabin cizon sauro tare da ƙara zuba kuɗaɗe a fannin kiwon lafiya, domin rage dogaro da tallafin ƙasashen waje.

Gidan talabijin na NTA ya ruwaito Pate ya bayyana hakan ne a Abuja yayin da yake karɓar tawagar kwamitin amintattu na Malaria Consortium, wadda ta kai ziyara ma’aikatar domin taya Nijeriya murnar raguwar yawan yara masu ɗauke da kwayar cutar daga kashi 42 cikin 100 a shekarar 2010 zuwa kashi 15 cikin 100 a 2025.

07/08/2026

Hon. Aminu Abdullahi warkal.

Address

Yakasai
Kano
6566

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hauwa Live posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share