27/12/2021
TSAKANIN SO DA SOYAYYA // 20
Mata s**an yi kishin mutum in s**a qaunace shi, wasu mazan ma suna da na su kishin, amma an fi liqa wa mata azabar kishi kamar dai yadda muka fadi a baya,to sai dai in qaunar dake tsakanin saurayi da budurwa ta gaskiya ce, koda an yi kishin an rabu kowa ya yi aurensa, in qaddara ta sa sai an sake haduwa, zai yi kyau a yafe wa juna, a tuna da cewa qauna ce asalin haduwar ba qiyayya ba, in irin wannan ya samu, za ka taras akwai shaquwa da ginin iyali na qwarai, sannan akan sami girmama juna, don tun asali akwai tsohuwar soyayyar wani abu ne dai ya gitto, shaidan kuma ya ba shi sa'a ya kurdada tsakanin masoya.
Abin da ya sa nake ganin shaidan ne, kai saurayi na biyu me ya kai ka shiga neman mace bayan addini ya hana ka matuqar wani ya riga ka? Annabi SAW ya horar da sahabbansa a kan yin haquri da duk wata budurwar da ta shaqu da wani saurayi, kuma iyayenta s**a amince da nemansa, in ba dai iyayen yarinyan ne s**a yi rashin girma wajen qin tsayar mata da saurayi guda daya kal ba, s**a bari har zakarun s**a fara neman kashe kawunansu sabo da kishi.
Wani makusancina ya fito gida ashe abokin hamayyansa yana qofar gida da irin sandar fulanin nan yana jiransa, da leqowarsa kuwa ya sa sandannan iya qarfinsa ya sheme shi, sai kwasansa aka yi zuwa asibiti, aka ci sa'a aka samo ransa kafin ya cika, yarinyar kuma ta kafe a kan cewa sam ba ta ba wannan magabcin har abada, haka dai soyayyar ta qare, bayan kishin, sai dai ni ban san ko waye ya fara nemanta ba a cikinsu.
A gefe guda kuma ga wani abokina na kusa da yake neman wata yarinya na tsawon shekara Biyu da rabi, kwatsam sai wancan magabcin ya fado, kuma da yake yana da abin hannunsa nan take ya yi sa'ar yin gaba da zuciyar yarinyar, da sallah ta zo abokina ya aika mata da manyan zakaru, da ta soya a maimakon ta aika wa abokimmu da su sai ta tura wa magabcimmu, mu kuma ta bar mu Ambaki-wofi, ta bi mu da guda-guda ta yi mana suna, sannan ta hada mu ta ba mu suna daya, abin haushin ma haka abokin