17/09/2026
A karo na uku, Majalisar Wakilan Amurka ta sake kada kuri’ar neman kawo ƙarshen shiga tsakani a yaƙin da ake yi da Iran, matakin da zai takaita ikon Shugaba Donald Trump na ci gaba da kai hare-haren soji ba tare da amincewar majalisar ba.
Sakamakon kuri’ar da aka kada ranar Talata ya nuna gaba da maki 220 a kan 204, inda ‘yan jam’iyyar Republican guda bakwai s**a juyawa jam’iyyarsu baya domin goyon bayan matakin.
Wannan ne karon da majalisar ke daukar irin wannan mataki bayan makamantan kuri'un da aka kada a watannin Yuni da Yuli na wannan shekarar.
To sai dai kash, har yanzu ba a san ko Majalisar Dattawa za ta amince da kudurin ba, musamman ganin yadda a baya sanatocin Republican s**a sauya matsayinsu bayan s**a fuskanci s**a daga Shugaba Trump.
Duk da irin rarrabuwar kawunan da yaƙin ke haifarwa tsakanin ‘yan siyasa, Trump ya ci gaba da kare matakin Amurka na shiga rikicin, yana mai ikirarin cewa hare-haren sun raunana ƙarfin sojin kasar ta Iran.