Kwankwasiyya United FC

Kwankwasiyya United FC A.G.D Hausa 24, Broadcasting & Media Productions, Facebook, YouTube, Tiktok. Whatapp: 07044055570

" Ni, Abdulbasi Ilyasu (Goro), ina mika sakon godiya tare da duk wanda yayiwa Hon. Aminu Sulaiman Goro Addu'ar samun lfy...
17/10/2025

" Ni, Abdulbasi Ilyasu (Goro), ina mika sakon godiya tare da duk wanda yayiwa Hon. Aminu Sulaiman Goro Addu'ar samun lfy.

Muna Addu'ar Allah Ubangiji ya inganta lfy, Hon. Aminu Sulaiman Goro - Abdulbasi Ilyasu Goro.

Sponsored.

Rahotanni sun tabbatar da cewa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barau FC, ita ce ta bukaci a buga wasan ba tare da magoya baya b...
14/10/2025

Rahotanni sun tabbatar da cewa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barau FC, ita ce ta bukaci a buga wasan ba tare da magoya baya ba.

Anasa ran akalla mutane 150 ne ake da bukata a wasan, wadanda jamian tsaro ne sai 'yan jarida.

Za'a buga wasan ne a Ranar Lahadi a filin wasana Sani Abacha dake ƙofar mata.

Me za ku ce?

Hon. Yusuf Ali Maigado, ya baiyyana hakan ne a shafinsa na facebook." Wannan ita ce ribar siyasa a guri na, a yi duk mai...
14/10/2025

Hon. Yusuf Ali Maigado, ya baiyyana hakan ne a shafinsa na facebook.

" Wannan ita ce ribar siyasa a guri na, a yi duk mai yiwuwa a samawa matasa makoma.

Muna alfahari da ku kwankwasiyya product and also maigado product - Hon. Yusuf Ali Maigado.

13/10/2025

Shugaban Kano Pro-Pa Hon. Dr. Habibu Sale Mohammed Mailemo Ph.D, sun kai ziyarar duba aikin ƙansilolin a ƙaramar hukumar Ƙaraye, wanda gwamnan Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya sahalewa.

Majalisar dokokin ta ƙasa ta bayar da shawarar a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na gwamnoni a watan Nuwambar 2026, k*...
13/10/2025

Majalisar dokokin ta ƙasa ta bayar da shawarar a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na gwamnoni a watan Nuwambar 2026, k**ar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Saboda Wasu dalilai na aiki masu karfi, mun dage wannan tattaunawa zuwa mako mai zuwa dft za'ayi mana afuwa. 🙏
11/10/2025

Saboda Wasu dalilai na aiki masu karfi, mun dage wannan tattaunawa zuwa mako mai zuwa dft za'ayi mana afuwa. 🙏

Wasu irin tambayiyi kuke so muyi a wannan makabalar ?

Lamarin ya faru ne da yammacin yau Asabar, inda rahotanni s**a bayyana jirgin da ke ɗauke da tawagar 'yan wasan ya yi sa...
11/10/2025

Lamarin ya faru ne da yammacin yau Asabar, inda rahotanni s**a bayyana jirgin da ke ɗauke da tawagar 'yan wasan ya yi saukar gaggawa a ƙasar Angola, saboda fashewar gilashin taga.

Rahotanni sun ce, yanzu haka tawagar ta Super Eagle's na kasar Angola, domin jiran wani jirgin daga kasar nan yazo ya dauke su zuwa gida Najeriya.

Super Eagle's na shirin buga wasa da kasar Benin a ranar Talata, a wasan share fagen shiga gasar cin kofin duniya.

" Sen.Barau I. Jibrin, ya bawa mutum dubu goma tallafin naira dubu ashirin a kowannen su.
09/10/2025

" Sen.Barau I. Jibrin, ya bawa mutum dubu goma tallafin naira dubu ashirin a kowannen su.

Magoya bayan Gawuna/Garo dana Sen. Barau I.Jibrin, na cigaba da musayar yawu a kafafen sada zumunta na zamani akan wanda...
09/10/2025

Magoya bayan Gawuna/Garo dana Sen. Barau I.Jibrin, na cigaba da musayar yawu a kafafen sada zumunta na zamani akan wanda zai yiwa Jam'iyyar APCn Kano takarar Gwamnan a 2027.

Wannan na zuwa ne, bayan kalaman Baffa Babba Dan Agundi da yayi na cewa, "In dai kuri'a kake nema a baka ita a sadaka, a zuba maka ita a sadaka to Billahillazi sai Gawuna Garo" - Hon. Baffa Babba Danagundi.

Me za ku ce?

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alh. Atiku Abubakar, ya yi tir da ci gaba da tsare shugaban ƙungiyar IPOB,  Nnamdi Kanu...
09/10/2025

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alh. Atiku Abubakar, ya yi tir da ci gaba da tsare shugaban ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu.

Atiku ya bayyana hakan ne a matsayin rauni a kan lamirin ƙasar nan da kuma abin da ke bata sunan bin doka da oda.

A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Atiku ya zargi gwamnatin tarayya da rashin mutunta umarnin kotu da ta bayar don bayar da belin Kanu, yana mai cewa hakan cin zarafi ne da kuma take hakkin shari’a.

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023 ya bayyana cikakken goyon bayansa ga kamfen ɗin da ɗan gwagwarmayar siyasa, Omoyele Sowore, ke jagoranta, wanda ke kira da a saki Kanu nan take ko kuma a gurfanar da shi a gaban kotu bisa ƙa’ida.

Tun bayan k**a shi a shekarar 2021, Nnamdi Kanu yana tsare a hannun Hukumar Tsaro ta DSS inda ake zarginsa da cin amanar ƙasa tare da tada hankaluna.

Hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da hana cin hanci da rashawa ta jihar Kano a Najeriya wato PCACC, ta ce ta fara gudanar da ...
09/10/2025

Hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da hana cin hanci da rashawa ta jihar Kano a Najeriya wato PCACC, ta ce ta fara gudanar da cikakken bincike kan zargin karkatar da wasu kudade fiye da naira bilyan hudu da tsohuwar gwamnatin jihar Dr Abdullahi Umar Ganduje ta yi.

Shugaban hukumar, Saidu Yahaya ya ce binciken da hukumar tasu ta fara gudanarwa ya biyo bayan wani ƙorafi ne da aka kai musu game da batun kuɗaɗen na naira sama da biliyan huɗu da ake zargin tsohuwar gwamnatin Ganduje ta karkatar

"A taƙaice, muna gudanar da bincike a kan wasu kuɗaɗe da aka ɗauka daga gwamnatin jahar Kano aka je aka saka a cikin Dala Inland Dry Port." in ji shi

"Wannan kudin ya kai sama da naira biliyan huɗu, kuma an ɗauke su ne a lokacin mulkin Abdullahi Ganduje.

Yayin da BBC ta nemi jin ta bakin malam Muhammad Garba, tsohon kwamishinan yaɗa labarai na jahar kuma tashon shugaban ma'aikatan tsohon gwamnan Dr Abdullahi Ganduje game da wannan bincike da aka fara, sai ya ce

"Nasan cewa maganar tana kotu to kuma idan magana tana kotu, ban san irin binciken da za ayi ba,."

"Da na tuntuɓi mai girma tsohon gwamna, Ganduje,wannan binciken ba wani abu ba ne na damuwa, dama ai an saba ana gudanar da irin wannan bincike a wurare daban-daban." In ji Muhammad Garba.

BBC Hausa

09/10/2025

" Abubuwa da yawa da ake samun su a Arewacin Najeriya, ai sai mu godewa Allah da muka samu Sen. Barau I. Jibrin, yadda yake da kyakyawar mu'amala da shugaban Kasa - Hon. Mu'azzam Madaki dan Jam'iyyar APC.

Address

Rijiyar Lemo Kwanar Yan Tifa, Fagge Local Government
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kwankwasiyya United FC posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share