
29/12/2024
GWAMNA ABBA KABIR YUSUF YA ZIYARCI GWAMNA UMAR NAMADI DON TA’AZIYYA A JIHAR JIGAWA
A karo na biyu cikin wannan mako, Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya kai ziyara zuwa garin Kafin Hausa a Jihar Jigawa, domin gabatar da ta’aziyya ga takwaransa, Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi. Wannan ziyara ta biyo bayan rasuwar mahaifiyar Gwamnan Jigawa, Hajiya Maryam Abdullahi, da babban dansa, Abdulwahab, waɗanda s**a rasu cikin wannan mako.
A yayin ziyarar, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jagoranci addu’o’i na musamman tare da yin fatan Allah Ubangiji ya jikansu, ya gafarta musu kura-kurai, ya kuma sanya su cikin rahamarSa da Aljanna Firdausi.