Taskira H Online TV

Taskira H Online TV Taskira H Online TV, Kafa ce da ke kawo muku sahihan labarai daga sassa daban-daban na duniya, za ku iya turo mana labarin domin sanar da al'umma kai tsaye!
(1)

Babbar Kotun tarayya da ke Gombe ta soke tikitin Farfesa Isa Ali Pantami na takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, ta...
24/09/2026

Babbar Kotun tarayya da ke Gombe ta soke tikitin Farfesa Isa Ali Pantami na takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, tare da umartar jam’iyyar da ta sake gudanar da zaɓen fidda gwani a jihar.

Jaridar Daily Trust ta ambato mai shari’a Amina Aliyu Mohammed ce ta yanke hukuncin ranar Alhamis, a ƙarar da Usman Aliyu Garry ya shigar yana ƙalubalantar fitowar Pantami a matsayin ɗan takarar PDP.

Garry ya yi zargin cewa ba a gudanar da zaɓen fidda gwani yadda ya kamata ba, bayan da PDP ta bayyana Pantami a matsayin ɗan takararta tilo a ranar 26 ga Yuni, 2026.

Pantami ya koma PDP ne bayan ya fice daga APC, wadda ta tsayar da Jamilu Gwamna a matsayin ɗan takararta na maslaha.

Sai dai kotun ta umarci PDP da ta sake gudanar da zaɓen fidda gwani bisa ƙa’idojin jam’iyyar da tanadin dokokin zaɓe.

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96Ministan Ya...
24/09/2026

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al'umma, Mohammed Idris, ya ce Nijeriya da Saudiyya suna zurfafa hulɗar su fiye da yadda take a baya, inda ake samun ƙarin haɗin gwiwa a fannonin noma, makamashi, zuba jari, sufurin jiragen sama, fasahar kuɗi (fintech) da kasuwanci.

Idris ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Abuja, a wurin wata liyafar cika shekara 96 na Ranar Kasa ta Masarautar Saudiyya.

Ya ce: "A yau, hulɗar mu ta shiga wani sabon mataki na tattalin arziki da dabaru. Nijeriya da Saudiyya suna da damarmaki na zurfafa haɗin gwiwa a fannonin noma, makamashi, zuba jari, sufurin jiragen sama, fasahar kuɗi da kasuwanci.

"Waɗannan su ne fannonin da za su kawo amfani ga ƙasashen biyu tare da ƙarfafa hulɗar tattalin arzikin mu."

Ministan ya ce an gina daɗaɗɗiyar hulɗar da ke tsakanin ƙasashen biyu ne bisa tarihi, addini, hulɗa tsakanin al'umma, da manyan buƙatu na bai-ɗaya, yana mai cewa 'yan Nijeriya sun daɗe suna tafiya zuwa Saudiyya domin aikin hajji, karatu, kasuwanci da sauran dalilai.

Ya ce Nijeriya na iya koyi daga gogewar bunƙasar da Saudiyya ta samu, yayin da Gwamnatin Tarayya ke aiwatar da gyare-gyaren tattalin arziki a ƙarƙashin Ajandar Sabunta Fata ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

"Gwamnatin na ci gaba da aiwatar da gyare-gyaren da nufin ƙarfafa tattalin arziki, inganta yanayin zuba jari, faɗaɗa ababen more rayuwa, da samar da ƙarin damarmaki ga 'yan Najeriya," inji Ministan.

Ya ƙara da cewa Gwamnatin Tarayya na zuba jari a tituna da hanyoyin jirgin ƙasa, tana inganta samar da wutar lantarki, tana kuma aiwatar da gyare-gyare a ɓangaren man fetur da iskar gas, tare da bai wa noma, masana'antu, fasahar dijital da tattalin arzikin ƙirkire-ƙirkire ƙarin kulawa.

Idris ya ce Nijeriya tana ƙoƙarin jawo ƙarin zuba jari na dogon lokaci ta hanyar samar da tsare-tsare bayyanannu ga masu zuba jari, yana mai cewa gyare-gyaren da aka yi kwanan nan a ɓangaren man fetur na teku an tsara su ne domin buɗe sababbin damarmakin zuba jari tare da ƙarfafa halartar 'yan Najeriya.

"Muna maraba da masu zuba jari da 'yan kasuwa daga Saudiyya da ke sha'awar Nijeriya. Akwai dama mai yawa ta haɗin gwiwa a fannonin noma da samar da abinci, makamashi, ababen more rayuwa, haƙar ma'adinai, fasaha da sauran fannonin samar da kayayyaki," inji shi.

Ministan ya yaba wa Ofishin Jakadancin Saudiyya kan ƙoƙarin su na ƙarfafa huldar da ke tsakanin ƙasashen biyu, tare da bayyana ƙwarin gwiwa cewa hulɗar za ta ci gaba da ƙaruwa ta hanyar ƙarin kasuwanci, zuba jari, musayar ra'ayoyi da haɗin gwiwa.

Ya taya gwamnati da al'ummar Saudiyya murna kan bikin cika shekara 96 na Ranar Ƙasar su, yana mai fatan Masarautar ta ci gaba da samun zaman lafiya da wadata.

Daga cikin manyan baƙi da s**a halarci taron akwai Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas; Jakadan Masarautar Saudiyya a Nijeriya, Yousef bin Mohammed Al-Balawi; Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo; Ministan Kasafin Kuɗi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Sanata Abubakar Atiku Bagudu; tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasa, Aisha Buhari, da wasu jami'an diflomasiyya da manyan 'yan kasuwa.

Babban Ministan tsaron Najeriya Janar Christopher Musa (Ritaya) Ya ba da shawarar a sanya horon aikin soji ya zama tilas...
24/09/2026

Babban Ministan tsaron Najeriya Janar Christopher Musa (Ritaya) Ya ba da shawarar a sanya horon aikin soji ya zama tilas ga ƴan ƙasar, Domin su fahimci yadda sojoji ke sadaukar da rayukan su wajen fuskantar ƙalubalen tsaro.

Shin ya kuke ganin wannan shawara?

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce matakan da gwamnatinsa ta ɗauka wajen sake fasalin bangaren man fetur da gas sun f...
24/09/2026

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce matakan da gwamnatinsa ta ɗauka wajen sake fasalin bangaren man fetur da gas sun fara haifar da ɗa mai ido.

Shugaba Tinubu ya bayyana kamfanonin AMNI International da TotalEnergies sun yanke shawarar zuba Dala miliyan 800 wajen bunƙasa iskar gas na Ima, wanda aka gano tun 1973.

Shugaban ya ƙara da cewa aikin zai samar da ayyukan yi da damarmaki ga ’yan Najeriya da al’ummomin da aikin zai gudana a cikinsu.

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Mallam Nasir Ahmad El-Rufai, Ya ce ba ya jin haushin abokan sa, abokan aiki da mutanen da y...
24/09/2026

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Mallam Nasir Ahmad El-Rufai, Ya ce ba ya jin haushin abokan sa, abokan aiki da mutanen da ya taɓa taimakawa da s**a yi shiru kan halin da yake ciki a yanzu.

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Ganduje, ya yi kira ga ’yan Najeriya da su ci gaba da jajircewa wajen gina ƙa...
23/09/2026

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Ganduje, ya yi kira ga ’yan Najeriya da su ci gaba da jajircewa wajen gina ƙasa da kuma tabbatar da dorewar dimokuraɗiyya.

Ganduje, wanda shi ne Babban Majiɓincin Ƙungiyar Tsofaffin Mataimakan Gwamnonin Najeriya (FFDGN), ya yi wannan kiran ne a ranar Laraba a Abuja, yayin da ya kai ziyarar ban girma ga shugabannin ƙungiyar.

Ya bayyana gamsuwarsa da ayyukan ƙungiyar, yana mai cewa tana samar da wani dandali da ke bai wa mutanen da s**a samu ƙwarewa a harkokin mulki, dimokuraɗiyya da siyasa damar bayar da gudunmawa wajen ci gaban ƙasa.

Ganduje ya kuma buƙaci ’yan Najeriya da su fifita muradun ƙasa, tare da kauce wa fifita muradun ƙabilanci ko na addini wajen gudanar da al’amuran ƙasa.

WATA SABUWA: Inda Ana Yi Wa Wani Sujada, Ya Kamata Ɗan Arewa Ya Yi Wa Shugaba Tinubu, — Inji Dakta Sani Ahmad Zangina
23/09/2026

WATA SABUWA: Inda Ana Yi Wa Wani Sujada, Ya Kamata Ɗan Arewa Ya Yi Wa Shugaba Tinubu, — Inji Dakta Sani Ahmad Zangina

DA ƊUMI-ƊUMIN SA: Alh. Atiku Abubakar, Ya gana da Yazid Aliyu, Yaron da ya yi Alkawarin ɗaukar nauyin karatun shi.Ɗan ta...
23/09/2026

DA ƊUMI-ƊUMIN SA: Alh. Atiku Abubakar, Ya gana da Yazid Aliyu, Yaron da ya yi Alkawarin ɗaukar nauyin karatun shi.

Ɗan takarar Shugaban Ƙasa a Jam'iyar ADC, Atiku Abubakar ya gana da Yazid Aliyu, Yaro mai hakar zinari da bidiyonsa ya yaɗu, wanda daga bisani Atiku Abubakar ya yi Alkawarin ɗaukar nauyin karatun shi.

Ɗan gwagwarmayar Mahadi Shehu, Ya bayyana hakan ne a cikin wata tattaunawar sa da gidan Talabijin na Symfoni. Shin me za...
23/09/2026

Ɗan gwagwarmayar Mahadi Shehu, Ya bayyana hakan ne a cikin wata tattaunawar sa da gidan Talabijin na Symfoni.

Shin me za ku ce?

Gwamnan Katsina ya yabawa sojoji kan dakile yunkurin sace mutane a jihar.Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Radda, ya yabawa d...
23/09/2026

Gwamnan Katsina ya yabawa sojoji kan dakile yunkurin sace mutane a jihar.

Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Radda, ya yabawa dakarun Rundunar Sojin Najeriya da babban kwamandan rundunar soji bisa dakile hare-haren ’yan ta’adda da yunkurinsu na kai hari tare da yin garkuwa da wasu mazauna jihar da dama.

Hakan na zuwa ne yayin da Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Olufemi Oluyede, ya umurci dakarun da kada su yi kasa a gwiwa wajen fatattakar dukkan ’yan ta’addan da ke addabar wasu sassan kasar, tare da sake jaddada alkawarinsa na kula da jin dadin dakarun.

Gwamnan ya kuma yabawa Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da ’yan banga bisa samar da bayanan sirri da s**a taimaka wajen hallaka ’yan ta’adda 18, yayin da aka kwato makamai da dama da kuma dabbobin da aka sace.

Address

Sheikh Ja'afar Mahmud Adam Road, Dorayi
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Taskira H Online TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share