21/09/2025
SABON SHIRI DAGA Dan Afirka...
Akwai waɗanda s**a yi tsokaci da cewa wasu fa ba sa gane Hausarmu, ko kuma kalamanmu suna yin tsauri ga fahimtar wasu, ba su cika fahimta ba — waɗannan fa ana maganar irin mutanen gida ne da ba su yi zurfi a karatu ba.
To in sha Allahu za mu fara gabatar da wani sabon shiri domin irinsu su ma, mai suna “AUNA FAHIMTA”. Tambayoyi ne da amsoshi akan girma da ɗaukakar Afirka, ɓoyayyun shirye-shirye da makirce-makircen maƙiya akan Afirka, dokokin da ke dawo da mu baya, wayar da kanmu da dai sauran abubuwan da za su ke zuwa a ciki masu matuƙar muhimmanci.
Zai dinga zuwa kullum sau ɗaya ko biyu in sha Allah — ya danganta dai da sauƙin kammalawa da muka samu. Kuma in sha Allah, za a fa’idantu da wannan shiri sosai. Kuma bidiyoyin ba za su dinga wuce tsawon minti 3 ba.
Akwai wasu shirye-shiryen ma da za su biyo baya a hankali...
Shi wannan shirin da muke gabatarwa na yanzu da kuka sani yanzu sunansa “Taskar Dan’afirka”, kuma zai ci gaba da zuwa sau biyu ko uku a kowanne sati in sha Allah.
Allah ya ci gaba da ɗaga darajar nahiyarmu ta Afirka! ✊