DNN Hausa

DNN Hausa DNN News Hausa:- Kafa mai kawo muku Labarai da shirye-shirye masu ƙayatarwa
a zamanance. 08061341152

Tsohon Sanatan Kogi ta Yamma, Dino Melaye, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar PDP, yana mai cewa ya daina hulɗa da jam’...
31/07/2025

Tsohon Sanatan Kogi ta Yamma, Dino Melaye, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar PDP, yana mai cewa ya daina hulɗa da jam’iyyar a dukkan matakai.

Wata wasiƙa da aka sanya kwanan watan ranar 4 ga Yuli, 2025, wacce aka aikawa Shugaban PDP na Gunduma ta 1 da ke Aiyetoro Gbede a Karamar Hukumar Ijumu ta Jihar Kogi, Melaye, ya bayyana rashin jin daɗinsa da yadda jam’iyyar ke tafiya.

Ya ce ya yanke shawarar ficewar bayan dogon nazari kan halin da jam’iyyar ke ciki, inda ya bayyana cewa ba zai iya ci gaba da halartar harkokin jam’iyyar ba, domin hakan ba zai dace dashi ba.

Melaye ya ƙara da cewa PDP ta nuna gazawa wajen jajircewar da ake bukata domin fitar da Najeriya daga halin da ya kira “lalacewar siyasa” da ke addabar a’lumma.

Ministan Ilimi na Najeriya Dr. Tunji Alausa, ya ce gwamnati za ta fara gudanar da gwajin ƙwayoyi na dole da kuma bazata ...
31/07/2025

Ministan Ilimi na Najeriya Dr. Tunji Alausa, ya ce gwamnati za ta fara gudanar da gwajin ƙwayoyi na dole da kuma bazata ga ɗaliban makarantu na gaba da sakandire a faɗin ƙasar.

Wannan matakin ya biyo bayan wata ganawa da ya yi da shugaban hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi na ƙasar (NDLEA), Janar Buba Marwa (mai ritaya), a birnin Abuja a ranar Laraba 30 ga Yuli, inda s**a tattauna hanyoyin dakile amfani da miyagun ƙwayoyi a tsakanin matasa da ɗalibai.

A cewar wani bayani da mai magana da yawun NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar, Ministan ya amince da buƙatar sauya tsarin karatun makarantun sakandire domin saka sabon darasi kan ilimin illolin miyagun ƙwayoyi.

Shin menene ra'ayinku kan wannan mataki?

Wasu al’ummomin ƙasar Ghana sun fito zanga zanga a Accra babban birnin kasar, domin nuna ƙin amincewarsu da zaman ƴan Na...
31/07/2025

Wasu al’ummomin ƙasar Ghana sun fito zanga zanga a Accra babban birnin kasar, domin nuna ƙin amincewarsu da zaman ƴan Najeriya a ƙasar tasu, bisa zargin aikata laifuka da kuma karya dokokin kasuwanci.

Masu zanga-zangar sun mamaye wasu manyan tituna da kasuwanni, musamman kasuwar Circle da ke Accra, inda ake ganin cunkoson ’yan Najeriya da ke gudanar da harkokin kasuwanci iri-iri.

Ƴan ƙasar ta Ghana sun zargi ƴan Najeriya da aikata laifukan kisan kai da harkar karuwanci, tare da mamaye kasuwannin da k**ata ya yi ƴan asalin kasar ne yafi k**ata suci gajiyarsu.

Mai bawa shugaban Najeriya shawara akan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya bukaci ƴan bindigar da ke addabar arewacin ƙasar...
30/07/2025

Mai bawa shugaban Najeriya shawara akan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya bukaci ƴan bindigar da ke addabar arewacin ƙasar da su ajiye mak**ansu su miƙa wuya.

A wata hira da ya yi da BBC Hausa, Ribadu ya ce gwamnatin Tinubu ta samu nasarori a yaƙi da ta’addanci, inda ya bayyana cewa sun kashe fiye da shugabanni 300 na ƙungiyoyin ta’adda, kuma yanzu wasu mutane sun fara komawa gonakinsu cikin kwanciyar hankali.

Sai dai, ya amince cewa har yanzu akwai hare hare a wasu sassan, musamman a Zamfara, Benue, Filato da arewa maso gabas, inda Boko Haram ke ci gaba da haifar da barazana.

Gwamnan jihar Kaduna dake arewacin Najeriya Sanata Uba Sani, ya bayyana cewa zai yi wuya wani gwamna a Najeriya ya ƙi go...
29/07/2025

Gwamnan jihar Kaduna dake arewacin Najeriya Sanata Uba Sani, ya bayyana cewa zai yi wuya wani gwamna a Najeriya ya ƙi goyon bayan sake zaɓen shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu a shekara ta 2027.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wajen buɗe taron kwanaki biyu na tattaunawa tsakanin gwamnati da al’umma, wanda gidauniyar tunawa da Sir Ahmadu Bello (SABMF) ta shirya a Arewa House da ke Kaduna.

Inda ya ce, a tarihi, babu wani shugaban ƙasa da ya nuna cikakken goyon baya ga gwamnoni da gwamnatocin jihohi k**ar yadda dhugaba Bola Ahmed Tinubu ke yi a yanzu.

Gwamna Uba Sani ya ƙara da cewa wannan ce tasa zaiyi wuya a samu wani gwamna a ƙasar da zai tsaya ya ƙalubalanci shugaban ƙasar.

Hotunan gonakin wasu manoma dake rayuwa a garin Dungun Mu’azu da ke ƙaramar hukumar sabuwa ta jihar Katsina s**a kasance...
29/07/2025

Hotunan gonakin wasu manoma dake rayuwa a garin Dungun Mu’azu da ke ƙaramar hukumar sabuwa ta jihar Katsina s**a kasance, bayanda s**a wayi gari fa furgici da baƙin cikin, yadda s**a s**a iske gonakin su na masara, dawa da waken suya an lalata su baki ɗaya.

Wata majiya daga cikin manoman Garin, ta ce cikin dare akai musu kutse, inda aka shigo da dabbobi aka take shukokin nasu, wasu gonakin kuma aka sare shukoken da gangan, abinda ya mayar da gonakin nasu k**ar ba a taɓa dasa komai a cikinsu ba.

Manoman sun roƙi gwamnatin jihar Katsina da sauran masu ruwa da tsaki, kada su yi shiru game da wannan al’amari mai ciwo da ya faru, wanda ka iya jefa su cikin yunwa da talauci.

Tsohon sakataren gwamnati Najeriya, Babachir Lawal, ya ce gwamnatin shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu tana yin watsi da y...
28/07/2025

Tsohon sakataren gwamnati Najeriya, Babachir Lawal, ya ce gwamnatin shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu tana yin watsi da yankin Arewa wajen aiwatar da muhimman ayyukan raya ƙasa.

Wata hira da aka yi da shi a Trust TV, Lawal ya ce babu wani aikin gwamnati da ke bayyane a Arewa, yana mai cewa duk mai hangen nesa zai fahimci yankin na fuskantar wariya.

Babachir ya goyi bayan kalaman tsohon ɗan takarar shugabancin ƙasar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, wanda ya ce gwamnatin Tinubu na mayar da hankali ne kan yanki ɗaya, sannan tana barin wasu a baya.

Lawal ya kuma nuna shakku kan makomar APC a Arewa, yana mai cewa jam’iyyar ba za ta iya samun nasara a zaben gaba ba idan har ta ci gaba da wannan salon mulki.

Sai dai Ministan Ayyuka, David Umahi, da mai ba shugaban ƙasar shawara kan kafafen yaɗa labarai, Sunday Dare, sun musanta zargin, inda s**a ce akwai manyan ayyuka fiye da 40 da ake aiwatarwa a Arewa a halin yanzu.

Gwamnatin Najeriya ta tura manyan motocin yaƙi guda shida don yaƙi da ƙalubalen tsaro a jihar Kebbi dake arewa maso yamm...
28/07/2025

Gwamnatin Najeriya ta tura manyan motocin yaƙi guda shida don yaƙi da ƙalubalen tsaro a jihar Kebbi dake arewa maso yammacin ƙasar.

Gwamnatin ta tura manyan motocin da aka fi sani da Armoured Personnel Carriers (APCs) domin yaƙi da ayyukan ta’addanci. Wannan na daga cikin matakan da gwamnatin shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ke ɗauka wajen fuskantar matsalolin tsaro a sassan kasar.

Gwamnan jihar Kebbi Nasir Idris ne ya bayyana hakan lokacin da yake duba motocin a harabar gidan gwamnati da ke Birnin Kebbi, inda yayi godiya ga shugaban ƙasas Bola Ahmed Tinubu da manyan hafsoshin tsaron ƙasar.

Gwamnan ya ce Kebbi, musamman yankin kudancin jihar, na fuskantar hare-hare ƴan bindiga da ke shiga daga jihohin Zamfara da Neja, suna kai farmaki sannan su gudu zuwa maɓoyarsu.

Ya ce tura wadannan motocin zasu taimaka wajen hana su sake kai hare-hare da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

A nasa bangaren, Kwamandan Rundunar 223 Light Tank Battalion da ke Zuru, Laftanar Kanar M. S. Saleh, ya nuna wa gwamnan kayan yaƙi da aka turo, tare da godewa gwamnatin tarayya da ta jihar bisa haɗin kai da tallafi da suke bayarwa domin ganin an shawo kan matsalar tsaro a jihar.

Rundunar ƴan sandan jihar Jigawa ta k**a wasu mutum biyu da take zargi da safarar mak**ai tare da ƙwato bindigogi biyu ƙ...
27/07/2025

Rundunar ƴan sandan jihar Jigawa ta k**a wasu mutum biyu da take zargi da safarar mak**ai tare da ƙwato bindigogi biyu ƙirar gida.

DSP Lawan Shi’isu, mai magana da yawun rundunar, ya ce jami’ai sun k**a Abdussamad Haruna mai shekara 30 a Kazaure yayin da yake ƙoƙarin kai bindigar zuwa jihar Filato.

Haka kuma, an k**a wani Auwalu Yusuf daga Kano tare da wata bindiga a hannunsa.

Kwamishinan ƴan sanda na jihar, CP Dahiru Muhammad, ya yabawa jami’an da s**a gudanar da aikin tare da tabbatar da aniyar rundunar wajen kare lafiya da dukiyoyin jama’a

26/07/2025

Gwmannan jihar Kano Abba Kabir Yusif ya rantsar da sarkin lafiyar Barebari a matsayin sabon shugaban jami'ar Northwest.

A taron yaye ɗaliban jami'ar Northwest University, Kano na shekaru biyar karo na biyu

26/07/2025

Taron yaye ɗaliban Northwest University, Kano na shekaru biyar karo na biyu

26/07/2025

Taron yaye ɗaliban jami'ar Northwest University, Kano na shekaru biyar karo na biyu

Address

Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when DNN Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to DNN Hausa:

Share