Mr.perfection novels

Mr.perfection novels BOOKπŸ“š
STROY WRITER βœ’πŸ“™
MUSLIM πŸ‘€β€
20🌹❀

*MA'UM*πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•   *stroy and written*              *By*_*sani Muhammad lawan*_         SMLAWAN AKA MR             perfect...
12/02/2025

*MA'UM*
πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•

*stroy and written*
*By*
_*sani Muhammad lawan*_
SMLAWAN AKA MR
perfection

_ALLAH YASAKAWA IYAYEN MU DA MAFIFICIN ALHERI_

*✨TAURARIN MARUBUTA WRITER'S ASSOCIATION✨*

*T.M.W.A.✍️*

✨✨✨✨✨
πŸ’ͺ😊

*TUNANI MAI ZURFI KAFIN RUBUTU SHINE TAKEN MU, RUBUTU MAI FAD'AKARWA DOMIN AL'UMMA,AL'K'ALAMIN MU ABIN AL'FAHARINMU, RUBUTU BAIWA CE GA WANDA ALLAH YA BAWA,TAKENMU SHINE HASKAWA A CIKIN AL'UMMA DA FIKIRAR DA ALLAH YA MANA, TAURARU A DUNIYAR MARUBUTA.*

✨✨✨✨✨
πŸ’ͺ😊

Bismillahi rahmanirraheem

page 2

*[The history]*
.......Ihu take tare da neman taimako ba abinda bakin ta yake fadi sai meena meena

...........Asalin labarin
Mal Usman dan asalin garin barno ne wanda kasuwanci yakawoshi garin Kano tare da matarsa aisha batare da yasan kowa ba tun zuwanshi Allah yahadashi da malam abdullahi Wanda yake dan asalin garin Kano malam Abdullahi irin fulanin nanne da bangaren uwa da matarsa bilkisu wacce take bafula tanar gombe tun zuwan malam usman garin Kano allah yahadashi da mal Abdullahi inda s**a fara abota har ta koma yan uwantaka haka bangaren matansu ma haka suke kamar yan uwa bilkisu tarike aisha kamar kanwarta dasuke uwa daya uba daya har wasu cikin makwafta ma basusan ba yan uwa bane suna zaune cikin unguwa daya taxarar gidajen su bashida yawa suna taimakon junansu sosai da sosai malam Abdullahi yana da yara biyu umar shine babba tazarar shekarar 12 ce tsakanisa da kanwarsa naima shikuma malam usman yana da yara 4 mata 3 saikuma namiji guda daya khadija ce babba wacce shekara biyu ne tsakanin ta da umar saikuma hauwa datake biye mata wacce ita kuma umar yabata shekara 3 saikuma namiji wanda akayiwa malam Abdullahi takwara anacemasa abdul sai bayan shekara aka Haifi maryam wacce itakuma sati 3 ne tsakaninsu da shatu wacce kayiwa umma takwara haka yaran s**a taso cikin soyayyar juna baka tababa banbance tsakaninsu a haka rayuwa taita tafiya a cikin wayanan a hali guda biyu tun maryam nada shekara biyu umar yakejin yarinyar a cikin ranshi fiye da yanda yakejin shatu tun tana shekara biyar Umar yasan yanason maryam wani irin so yakeji yana mata mai zauna mutum sanda takai shekara Goma lokacin kowa yagani Umar yana matukar Sonta kuma shima lokacin ya fito da soyayyarsa gareta haka maryam tatashi da soyayyar umar a cikin zuciyarta *MAUM* shine sunan sunan da kawayenta ke kiranta sunan yayiwa umar dadi hakan yasa shima yamaida inkiyarshi *MAUM* soyayya ake gudanarwa mai tsafta bangaren rayuwa maryam tana da sanyi hali sosai da sosai bada hayaniya ko kadan haka shima ma umar bashida hayaniya sosai akwai miskilanci kasancewar umar shine babba a wajen mahaifiyarshi hakan yasa takesa umar tayata ayyukan gidan umar yanason yin girki sosai da sosai idan yayi girki kowa jindadin shi yake a gidan har wani lokacin abba yakance masa malam umar ko dai abincin ka a girki yake hakan yasa ummanshi ta hanashi girkin domin bata jindadi anacewa anan abincinshi yake sanda umar yagama secondary school yahuce school of hygiene yayi diploma dinshi bangaren health bayan ya kammala ne yajuya catering inda yayi certificate anan sanda umar yagama school of hygiene tabbas inda yayi maka girki zakace irin akasar turawan nanne bayan gama certificate dinsa yakoma kasuwanci tare da iyayensa a lokacin khadija da hauwa duk sunyi aure soyayya kam kara guda na take tsakanin umar da maryam wacce take bawa kowa shaawa shakuwa kam ba a magana
Cigaban labari.........!!

*comment and share fisabilillah*

_Please follow_πŸ‘‡πŸ‘‡

*whatsapp group*

https://chat.whatsapp.com/DRdQmNLHoqmDle4kdM3Thr

*WhatsApp channel*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb5SXd98fewwEByet33d

*MA'UM* πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•       *Story and written*                  *By**_Sani Muhammad Lawan_*       SMLAWAN AKA MR            P...
11/02/2025

*MA'UM*
πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•πŸ’•

*Story and written*
*By*
*_Sani Muhammad Lawan_*
SMLAWAN AKA MR
Perpection

TSOKACIN FARKO!!!
*_LABARIN SOYAYYAR UMAR DA MARYAM WANAN LABARIN SOYAYYA NE DAYA ZO MUKU DA SABON SALO WANAN KIRKIRAREN LABARI NE BAN RUBUTA SHI DOMIN CIN ZARAFIN WANI KO WATA BA IDAN KUMA YAYI KARO/SHIGE KO KALA DA WANI BARI NA RAYUWARKA INA DAGA HANNU BIYU INANEMAN AFUWARKA_*

*_SADAUKARWA!!!_*
_NA SADAUKAR DA WANAN LABARIN SOYAYYAR ZUWA GA MAHAIFIYATA (zahrau kabir bature) ALLAH YAFARANTA MIKI YA SAKA MIKI DA GIDAN ALJANNA SANAN NAKARA SADAUKAR DASHI GA YAYATA YAR UWATA (Fatima Muhammad lawan) ALLAH YA HASKAKA RAYUWA SANAN NAKARA SADAUKAR DASHI GA DIMBIN MAKARANTA LABARAN HAUSA MAZA DA MATA ALLAH YABIYA MUKU BUKATUN KU YAFARANTA RAYUWARKU_

_ALLAH YASAKAWA IYAYEN MU DA MAFIFINCIN ALHERI_

TSOKACI NA BIYU!!!
*KAMAR YANDA NAFADA ABAYA WANAN LABARIN SOYAYYA NE DA YAZO MUKU DA SABON SALO AKWAI ABUBUWA DA ZASUYI MUKU DADI LABARIN SOYAYYA NE MAI TABA ZUCIYA ZAKU KARU DA ABUBUWA DA DAMA SANAN DA AKWAI* *ABUBUWANDA BAZASUYI MUKU DADI BA TO INASO KUYI AMFANI DAABUBUWAN DASUKAYI* *MUKU DADI WAJEN ADALCI GARENI SANAN KUYI WATSI DA ABUBUWANDA BADAIDAI BA KASANCEWA TA NA DAN ADAM AJIZI KUMA WANAN SHINE LITTAFI NA NAFARKO DUKDA BASHI NE LABARI NAFARKO BA*

*GODIYA*
_INA KARA MIKA GODIYA TA GA ALLAH SUBAHANAHU WATA ALA DAYABANI DAMAR RUBUTA WANAN LABARINDUMBIN GAISUWA TARE DA TARIN SOYAYYA GA DAN UWANA AMMAR HARUNA MUHAMMAD_

*GARGADI!!!*
_KADA WANI KO WATA YASAUYA MUN WANAN LABARIN KO YAYI AMFANI DA WANI BANGARE DAGA CIKI BATARE DA IZINI BA_

*Muje zuwa......✍️*

Bismillahi rahmanirraheem

Page 1

*[The beginning of the Story]*

......kano state Nigeria unguwar sharada tana daya daga cikin manyan ungoyoyi da suke cikin garin Kano, unguwar sharada unguwa ce mai girma da allah ya albarkace su da ruwansha mai dadi kasancewa shekaru kafin yanzu unguwar fadamace hakan yasa suke da wadattacen ruwan sha mai dadi dakuma lambo kasancewar unguwar tanada sanyi da danshi,
Cikin sharada phase2 bangaren masu matsakaicin Karfi cikin wani babban layi wanda ake kira da babbar hanya zaratan samari ne zaune kan Benci suna hira cikin zaratan samarin ido na yasauka kan wani guda Wanda yake daga gefe kamar badashi ake caftar ba sanye yake cikin white sheat da wando na jeans,

hankalinshi na kan babbar hanya da alamu akwai abinda yake jira baki ne amma ba can ba chocolate colour tarin yan mata ne s**a kutsu babbar hanyar sanye do coffee colour din hijabi da alamu daga islamiyya suke duk tarin yan mata da suke kutsuwa hakan bai hana idanu sa gano masa abar kaunarsa ba wacce yazauna jiranta a koda wane lokaci yakan zauna jiranta tafiya take cikin nustuwa dukda suma sauran yan matan a nusten suke tafiya yan mata suna tafiya ne in group kaman yanda suke tafe cikin group su uku daya a cikinsu mai suna haleema ce tace shatu ga yayanki fa yana jiranka wacce a kira da naima ce tace yayan maryam dai tundaga kallo daya zaka kamanninta da Guy din wacce aka Kira da maryam tace eeyh yayana nikadai to daman ai sai ke din cewar shatu dariya halima tayi sanan tace to yayan maryam murmushi maryam din tayi wanda yasa dimple din ta dake bari daya ya loba maryam kyakyawa ce irin kyawawan nan na gaske a haka har s**a karaso inda yake tsaye halima ce tafara gaidashi sanan shatu maryam kam a hankali ta gaidashi cikin salon soyayya amsawa yayi fuskarshi dauke da murmushi wanda ya kara bayyana zallan kyawun sa kyakyawa ne nagaske as I said Bakine irin black beauties dinan Yanada dara daran idanu masu kyau da kwarjini hancinsa mai matsakaicin tsayi ne sanan Yanada kyawawan pink lips kasancewar shima dauke yake da murmushi hakan yabawa dimple dinshi damar bayyana (yaya umar) sunan da na tsinkayo muryar shatu na fada baby andawo yafada amma still idanunsa na kan maryam da murmushi Yaki barin fuskarta eeyh yaya nadawo to akai lada gida bari naraka antin ki ko dariya halima tayi dan duk wanda yake tare da maryam da naima yasan ta waje daya suke fada acewa maryam antin shatu maryam ce tace da naima kanwata sai anjima sanan tabi bayan yaya umar dayayi gaba shatu bata tankaba tayi gaba halima tabi bayansa saida takaraso wajenshi sanan tace my man naam my angel yafada yana kallonta my man kayi kyau ai kullum acikin kyau nake a wajenki allah my man kayi kyau naji amma ai kinfini kyau dariya maryam tayi kafin tace nidinwa nakai ka kyau yayana kedin yaya umar yafada to nayarda maryam tafada tana kumshe dariyar umar dayahade rai kasancewar sunzo hucewa ta wajen wasu maza sukuma sun kurawa maryam din idanu babban abinda yake karawa maryam matsayi a zuciyar umar bata taba musu dashi ba ko da awasa yana fadin abu zatace tayarda a haka har s**a karaso kofar gidan su maryam din wanda ananma s**a tsaya a waje s**a cigaba da hirar su wacce take kara musu shakira saida sika kwashe kimanin Mintuna 20 sanan Umar yace my angel kishiga gida kinga anfara kiran sallah to sheknn yaya me xantawo miki dashi idan zandawo komai ma tafada sanan tashige gida shima masallaci yanufa gida tashiga dauke da sallama umma dake zaune a bakin famfo tana daura alwala ce ta amsa mata tare Dacewa juliyat iyayen soyayya sai yanzu aka shigo murmushi maryam tayi sanan tashige dakinta.!!

*Comment and share fisabilillah πŸ™*

For WhatsApp group πŸ‘‡
https://chat.whatsapp.com/DRdQmNLHoqmDle4kdM3Thr

08181170719
*WhatsApp channel*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb5SXd98fewwEByet33d
*_~Mr.perfection gareku~_*

Address

B. U. K Road
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Mr.perfection novels posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share