12/12/2024
BOOM💥💥💥
ABBA KABIR YUSUF YAYI GARAMBAWUL
Gwamnan Jihar Kano Engr Abba Kabir Yusuf ya Sauke sakataren Gwamnatin jihar Kano Alhaji baffa bichi daga Mukamunsa.
Haka Kuma Shima Shugaban Ma'aikatan Fadar Gwamnatin jihar ta Kano Alhaji Wada sagagi ya rasa Mukamunsa a Wannan Garanbawul da Gwamnan Yayi
Sauran Wadanda S**a rasa Mukamansu sun hada da Hon, Ibrahim Jibril Fagge, da Hajiya Ladidi Ibrahim Garko, da Kuma Baba Halilu Dantiye, sai Shehu Aliyu Yammedi, da Kuma, Abbas Sani Abbas.
Cikin Wata Sanarwa da Mai Magana da Yawun Gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa ya Fitar da Yammacin Wannan Rana Yace Tuni aka Sauya wa Wasu kwanishinoni Zuwa Wasu Ma'aikatu Ciki harda Mataimakin Gwamnan Jihar Kano Kwamarade aminu Abdussalam Gwarzo inda aka Tura Shi Zuwa Ma'aikatar Ilimi Mai zurfi.
Sauran Sune ,Hon. Mohammad Tajo Usman Wanda aka Tura Shi Zuwa Ma'aikatar Kananan Hukumomi da Masarautu, Yayin da aka Tura Dr. Yusuf Ibrahim Kofar Mata Zuwa Ma'aikatar kimiya da fasaha
Sauran Sune Hon. Amina Abdullahi Wadda Yanzu Zata Koma Ma'aikatar Kula da Mata Yayin da. Hon. Nasiru Sule Garo, aka Mayar Dashi Zuwa Ma'aikatar Mahalli.
Mikiya Hausa Times ta rawaito Cewa Hon. Ibrahim Namadi Yanzu zai Koma Ma'aikatar Sufuri sai, Hon. Umar Haruna Doguwa Wanda ya Koma Ma'aikatar Kula da albarkatun Ruwa
Hon. Ali Haruna Makoda ya Koma Ma'aikatar Ilimi sai Hon. Aisha Lawal Saji Wadda ta Koma Ma'aikatar yawon Bude ido da al'adu Yayin da Hon. Muhammad Diggol ya Koma Ma'aikatar Duba ayyukan Gwamnati.
~MR😎SD