15/07/2026
HANYOYI 3 NA FARA KASUWANCI BA TARE DA BABBAN JARI BA
Yawancin mu muna tunanin sai mun tara N500,000 sannan zamu fara kasuwanci. Wannan tunanin ne yake hanamu arziki.
Ga hanyoyi 3 da zaka iya farawa yau da kullum:
1. Kasuwancin Tsakani (Dillanci): Ka nemo mai kayan sawa ko takalma a Kasuwar Sabon Gari. Ka dauki hotuna ka dora a Status. Duk wanda ya saya, ka je ka saya ka kai masa, ka cire ribarka.
2. Sana'a da Ilimi: Idan ka iya rubutu, gyaran waya, ko design, ka fara tallata shi a Facebook. Babu shago da ake bukata.
3. Hadin Gwiwa: Ka hada jari da abokinka amintacce. Shi ya bada kudi, kai ka bada kwazo.
Babu ƙaramin kasuwanci, akwai ƙaramin tunani ne kawai.
Wanne daga cikin 3 dinnan zaka iya farawa? Rubuta a comment in ja-gorance ka.