11/12/2025
SAHABA IKON ALLAAH!
Cikin ƙaddarawar Ubangiji an kammala ginin Masjid Sahaabah Ɓangaren mata.wanda wani bawan Allaah ya dauki nauyin ginawa.Wanda In shaa Allaah Gobe Jumu'ah Shaykhanah Shaykh Muhammad Bin Uthman Zai jagoranci Sallar Jumu'ah a Masallacin nasa tare da buɗe wannan ɓangare.
Ɓangaren yana saman Masjid Sahaba ne,wanda Ɓangaren ya ƙunshi bandakuna da wajen alwala da yalwataccen wajen Sallah.
Muna Addu'ar Allaah ta'alah yadda muke nuna wannan farin ciki na kammaluwar Ɓangaren mata,mu nuna farin cikinmu mara misaltuwa na ginin katafaren Masjid Sahaba (Inshaa Allaah).
Wanda ya ɗauki Nauyin wannan aiki kuma Ubangiji ya biya masa buƙatunsa,ya Gina masa gida a Aljannah.
Allaah ya ƙarawa Shaykhanah Shaykh Muhammad Bin Uthman lafiya da tsawon rai mai Amfani mai Albarka. Tare da Na'ibinsa Sheikh Auwal Akilu Zakirai Auwal Akilu Abdullahi Zakirai.
Allaahumma Aameen!
NB:An samar da wannan hoto da taimakon fasahar Zamani ta AI