Cansal Media

Cansal Media News media

Ita wannan kafa ta yada labarai ce zallah Wanda ya shafi Al'umma da siyasa domin kawo muku sahihan labari.

Gwamnatin jihar Kano ta nesanta kanta daga dukkan wasu masu hannu a faɗace-faɗacen daba da masu ɗaukar nauyinsu, tare da...
01/06/2026

Gwamnatin jihar Kano ta nesanta kanta daga dukkan wasu masu hannu a faɗace-faɗacen daba da masu ɗaukar nauyinsu, tare da shan alwashin tabbatar da ɗaukar matakin shariʼa kan duk wanda aka samu da hannu a lamarin.

Arewa Updates ta rawaito cewa, Kwamishinan Shariʼ na Kano Abdulkarim Kabir Maude SAN ne ya bayyana hakan a wani faifan bidiyo da ya fitar.

Ya ce, Gwamnatin Kano ba ta tare da duk wanda ya ke tada fiitina ko ya ke sanyawa a yi faɗan daba.

Ya ci gaba da cewa, a shirye gwamnati take wajen yin aiki ba sani ba sabo ga duk wanda aka k**a da hannu a ayyyukan ƴan daba da ke addabar jihar.

Maude ya ce, tunda ya shigo ofis Gwamna bai taɓa ba shi umarnin a saki wani mai laifi ko wani da ake zargi ba.

Ya ce, koda yaushe Gwamna na ba da goyon bayan a yi shariʼa ba sani ba sabo.

A ƙarshe ya ce, za su murƙushe duk wani matsin lamba da wani zai yi don ganin an yi sassauci wajen yaƙi da matsalar.

28/05/2026

Wasu daga cikin Rayuwar Yadda tsohon Firaministan Najeriya Abubakar Tafawa Balewa ya yi rayuwa cikin gudun duniya ba tare da handame kuɗaɗen gwamnati ba.

Souses by:- RFI Hausa international

Kwankwaso na shirin ayyana Aminu Abdussalam a matsayin ɗan takarar gwamna na NDC a KanoRahotanni daga wasu majiyoyi masu...
28/05/2026

Kwankwaso na shirin ayyana Aminu Abdussalam a matsayin ɗan takarar gwamna na NDC a Kano

Rahotanni daga wasu majiyoyi masu tushe sun bayyana cewa jagoran Ɗariƙar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, na shirin bayyana tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Comrade Aminu Abdussalam, a matsayin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar NDC a jihar Kano.

An cimma wannan matsaya ne bayan tattaunawa ta sirri da aka gudanar a tsakanin jiga-jigan tafiyar Kwankwasiyya da abokan siyasa na kusa da Kwankwaso.

Sai dai rahotanni sun ce daga ƙarshe Kwankwaso ya amince da Abdussalam a matsayin wanda zai baiwa takarar.

Rahotannin sun ƙara da cewa Kwankwaso ya yi wa Gawuna tayin kujerar mataimakin gwamna ko kuma tikitin takarar Sanatan Kano ta Tsakiya, amma ana ganin Gawuna ya ƙi amincewa da tayin tare da jaddada biyayya da ci gaba da aiki domin nasarar jam’iyyar.

Majiyoyi sun ce Gawuna ya shaida wa Kwankwaso cewa ya shiga tafiyar Kwankwasiyya ne ba tare da wani sharadi ba, saboda haka rashin samun tikitin gwamna ba zai sa ya fice daga tafiyar ba.

An kuma rawaito cewa ƙin amincewar Gawuna da tayin ne ya jinkirta sanar da Aminu Abdussalam a hukumance, yayin da wasu masu ruwa da tsaki ke matsa lamba kan a sake duba cancantar Gawuna saboda ƙarfin siyasarsa.

Wasu daga cikin masu goyon bayan Gawuna sun bayyana cewa ya k**ata ɗan takarar da zai fafata da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fito daga Kano ta Tsakiya, kasancewar yankin ne ke da mafi yawan ƙuri’u a jihar.

Sai dai masu goyon bayan Aminu Abdussalam suna ganin tsohon mataimakin gwamnan ya nuna cikakkiyar biyayya, jajircewa da sadaukarwa wajen bunƙasa tafiyar Kwankwasiyya.

#

Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya amince  da baiwa dukan ma'aikatan Kano na kananan hukumomi 44 dake mataki na 1...
26/05/2026

Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya amince da baiwa dukan ma'aikatan Kano na kananan hukumomi 44 dake mataki na 1 zuwa mataki na 14 a aiki kyautar naira dubu ashirin, don basu damar gudanar da bukukuwan sallah cikin walwala da iyalansu.

Wannan na zuwa ne Jim kadan bayan da Gwamnatin ta biyan albashin ma'aikata na wannan watan na mayu.

Sanarwar hakan na kunshe ne cikin wata takarda da aka rabawa manema Labarai, Mai dauke da sa hannun Musa Tanko Muhammad, jami'in yada labarai a ofishin Sakataren Gwamnatin kano

Gwamnatin Jihar Kano ta k**a wasu jabun magunguna da kuɗinsu ya haura Naira miliyan 200. Wannan na cikin sanarwar da Ami...
24/05/2026

Gwamnatin Jihar Kano ta k**a wasu jabun magunguna da kuɗinsu ya haura Naira miliyan 200.

Wannan na cikin sanarwar da Amir Abdullahi Kima, mamba a Kwamitin Kar-takwa na Yaƙi da Fatauci da Safarar Miyagun Kwayoyi, Muggan Mak**ai da Ƙananan Yara da Gwamnatin Kano ta kafa ya fitar.

Sanarwar ta ce jami’an Civil Defence, dana hukumar NDLEA, da ’yan sanda sai jami'an Immigration ne s**a haɗa hannu wajen gudanar da samamen ƙarƙashin jagorancin shugaban kwamitin, Major A. A. Usman mai ritaya.

Yayin sumamen an gano jabun magungunan a cikin wani kango inda ake adana su cikin matsanancin zafi ba tare da kulawa mai kyau ba, sannan ba su da sahalewar Hukumar NAFDAC.

Sanarwar ta ce gwamnatin Jihar Kano za ta ci gaba da haɗa hannu da hukumomin tsaro da hukumomin lafiya domin yaƙi da masu safarar jabun magunguna tare da hukunta duk wanda aka samu da hannu a wannan aiki.

Alhaji Dauda Adamu Abdullahi Rarara kuma mawakin jam'iyar APC ya roƙi alʼumma su yi amfani da damarsu wajen taimakawa ma...
24/05/2026

Alhaji Dauda Adamu Abdullahi Rarara kuma mawakin jam'iyar APC ya roƙi alʼumma su yi amfani da damarsu wajen taimakawa masu ƙaramin ƙarfin da ke kusa da su.

23/05/2026

Sarkin kano Alhaji Aminu Ado bayero zai gudanar da hawan sallah a kano

Bayan shafe shekaru biyu ba ai shagalin hawan a kano ba.

23/05/2026

Bayanin Zargin alawar da Hon, Alasan Ado Goguwa yake sha

Tare jafar jafar dan jarida a Nigerian

Kimanim gero buhu guda aka dama a gasar shan koko ta duniya a unguwar Tikuntawa da ke ƙaramar hukumar Birni.Wasu matasa ...
23/05/2026

Kimanim gero buhu guda aka dama a gasar shan koko ta duniya a unguwar Tikuntawa da ke ƙaramar hukumar Birni.

Wasu matasa sun gabatar da wannan gasa domin bunƙasa al’adun Hausawa da kuma inganta abincin gargajiya.

Haka kuma, sun yi kira ga Majalisar Ɗinkin Duniya da ta ware rana ta musamman domin Ranar Shan Koko ta Duniya.

22/05/2026

Masarautar Kano da ke gidan Nasarawa ƙarƙashin Sarki Alhaji Aminu Ado Bayero ta sanar da shirinta na gudanar da bukukuwan hawan Babbar Sallah.

wannan na cikin wasikun sanarwa da sakataren Sarkin Kano na Masarautar, Malam Abdullahi Haruna Kwaru ya aikewa jami’an tsaron ƴan sanda da DSS na jihar.

Takardun sun ce majalisar masarautar ta amince da gudanar da bukukuwan hawan na bana tare da tsara ranakun da za a gudanar da su.

Sun bayyana cewa bukukuwan hawan na daga cikin al’adun masarautar da ke bai wa Sarki damar zagaya gari tare da masu sarauta domin gaisawa da al’umma.

Takardun sun kuma bukaci jami’an tsaro da sauran hukumomi su bayar da hadin kai domin gudanar da bukukuwan cikin lumana.

Address

Chiranchi Qts Kano
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Cansal Media posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share