DARMA TV

DARMA TV This TV channel is all about Web2, Web3, entertainment, content creation, news, and current affairs in English and Hausa.

08/06/2026

Wacce sana'a ce da mutane suke raina ta amma kuma ana samun kuษ—i da ita ba laifi sosai?

30/05/2026

๐ˆ๐Ÿ ๐ฒ๐จ๐ฎ ๐ซ๐ž๐š๐ฅ๐ฅ๐ฒ ๐ง๐ž๐ž๐ ๐ฆ๐จ๐ง๐ž๐ฒ, ๐๐จ๐ง'๐ญ ๐ฃ๐จ๐ข๐ง ๐ฉ๐จ๐ฅ๐ข๐ญ๐ข๐œ๐ฌ.
๐ˆ๐Ÿ ๐ฒ๐จ๐ฎ ๐ฐ๐š๐ง๐ญ ๐ญ๐จ ๐›๐ž๐œ๐จ๐ฆ๐ž ๐š ๐›๐ข๐ฅ๐ฅ๐ข๐จ๐ง๐š๐ข๐ซ๐ž ๐ฃ๐ฎ๐ฌ๐ญ ๐ ๐จ ๐ข๐ง๐ญ๐จ ๐›๐ฎ๐ฌ๐ข๐ง๐ž๐ฌ๐ฌ.
๐ˆ๐Ÿ ๐ฒ๐จ๐ฎ ๐ ๐จ ๐ข๐ง๐ญ๐จ ๐›๐ฎ๐ฌ๐ข๐ง๐ž๐ฌ๐ฌ ๐›๐ฒ ๐€๐ฅ๐ฅ๐š๐ก'๐ฌ ๐ฐ๐ข๐ฅ๐ฅ, ๐ฒ๐จ๐ฎ'๐ฅ๐ฅ ๐ฌ๐ฎ๐ซ๐ฏ๐ข๐ฏ๐ž ๐š๐ง๐ ๐š๐ฅ๐ฅ ๐ฒ๐จ๐ฎ๐ซ ๐ฐ๐ข๐ฌ๐ก๐ž๐ฌ ๐ฐ๐ข๐ฅ๐ฅ ๐›๐ž ๐ ๐ซ๐š๐ง๐ญ๐ž๐.
๐“๐ก๐ž๐ซ๐ž'๐ฌ ๐ง๐จ ๐ซ๐ž๐š๐ฅ ๐ฆ๐จ๐ง๐ž๐ฒ ๐ข๐ง ๐ฉ๐จ๐ฅ๐ข๐ญ๐ข๐œ๐ฌ.
๐€๐ง๐ฒ๐จ๐ง๐ž ๐ฐ๐ก๐จ ๐›๐ž๐œ๐จ๐ฆ๐ž๐ฌ ๐š ๐›๐ข๐ฅ๐ฅ๐ข๐จ๐ง๐š๐ข๐ซ๐ž ๐ข๐ง ๐ฉ๐จ๐ฅ๐ข๐ญ๐ข๐œ๐ฌ ๐ฎ๐ฌ๐ฎ๐š๐ฅ๐ฅ๐ฒ ๐ฃ๐ฎ๐ฌ๐ญ ๐ฌ๐ญ๐ž๐š๐ฅ๐ฌ ๐ฉ๐ฎ๐›๐ฅ๐ข๐œ ๐ฐ๐ž๐š๐ฅ๐ญ๐ก ๐š๐ง๐ ๐ฉ๐ซ๐จ๐ฉ๐ž๐ซ๐ญ๐ข๐ž๐ฌ.
๐๐จ๐ฅ๐ข๐ญ๐ข๐œ๐ฌ ๐ข๐ฌ ๐ฆ๐ž๐š๐ง๐ญ ๐ญ๐จ ๐›๐ž ๐š ๐ฐ๐š๐ฒ ๐Ÿ๐จ๐ซ ๐ฉ๐ž๐จ๐ฉ๐ฅ๐ž ๐ญ๐จ ๐ž๐š๐ซ๐ง ๐ญ๐ก๐ž๐ข๐ซ ๐ฉ๐ฅ๐š๐œ๐ž ๐ข๐ง ๐ฉ๐š๐ซ๐š๐๐ข๐ฌ๐ž ๐›๐ฒ ๐ฅ๐จ๐ฏ๐ข๐ง๐ , ๐œ๐š๐ซ๐ข๐ง๐  ๐š๐ง๐ ๐ฌ๐ก๐จ๐ฐ๐ข๐ง๐  ๐ฌ๐ฒ๐ฆ๐ฉ๐š๐ญ๐ก๐ฒ ๐ญ๐จ ๐ญ๐ก๐ž๐ข๐ซ ๐ฅ๐จ๐ฏ๐ž๐ ๐จ๐ง๐ž๐ฌ ๐š๐ง๐ ๐ญ๐จ ๐จ๐ญ๐ก๐ž๐ซ๐ฌ.
๐ˆ๐ญ'๐ฌ ๐š๐ฅ๐ฌ๐จ ๐š ๐ฐ๐š๐ฒ ๐Ÿ๐จ๐ซ ๐ฉ๐ž๐จ๐ฉ๐ฅ๐ž ๐ญ๐จ ๐ฌ๐ž๐ซ๐ฏ๐ž ๐š๐ง๐ ๐ฉ๐ซ๐จ๐ญ๐ž๐œ๐ญ ๐ฉ๐ž๐จ๐ฉ๐ฅ๐ž ๐Ÿ๐ซ๐จ๐ฆ ๐ก๐š๐ซ๐ฆ ๐š๐ง๐ ๐ ๐ฎ๐ข๐๐ž ๐ญ๐ก๐ž๐ฆ ๐ญ๐จ ๐ญ๐ก๐ž ๐ซ๐ข๐ ๐ก๐ญ ๐ฉ๐š๐ญ๐ก ๐›๐ฒ ๐ฉ๐ซ๐จ๐ฆ๐จ๐ญ๐ข๐ง๐  ๐ญ๐ก๐ž๐ข๐ซ ๐ฌ๐จ๐œ๐ข๐š๐ฅ ๐ฐ๐ž๐ฅ๐ฅ-๐›๐ž๐ข๐ง๐ .
๐๐จ๐ฅ๐ข๐ญ๐ข๐œ๐ฌ ๐ข๐ฌ ๐ง๐จ๐ญ ๐š ๐ฐ๐š๐ฒ ๐Ÿ๐จ๐ซ ๐ฉ๐ž๐จ๐ฉ๐ฅ๐ž ๐ญ๐จ ๐ฌ๐ญ๐ž๐š๐ฅ ๐จ๐ญ๐ก๐ž๐ซ๐ฌ' ๐ฐ๐ž๐š๐ฅ๐ญ๐ก ๐š๐ง๐ ๐ฉ๐ซ๐จ๐ฉ๐ž๐ซ๐ญ๐ข๐ž๐ฌ ๐ฃ๐ฎ๐ฌ๐ญ ๐ญ๐จ ๐ฌ๐ก๐š๐ซ๐ž ๐ข๐ญ ๐ฐ๐ข๐ญ๐ก ๐ญ๐ก๐ž๐ข๐ซ ๐Ÿ๐š๐ฆ๐ข๐ฅ๐ข๐ž๐ฌ ๐š๐ง๐ ๐Ÿ๐ซ๐ข๐ž๐ง๐๐ฌ.
๐–๐ซ๐ข๐ญ๐ญ๐ž๐ง ๐›๐ฒ:
๐ˆ๐ฌ๐š๐ก ๐˜๐š๐ก๐š๐ฒ๐š ๐†๐ข๐ฅ๐ข๐ฆ๐š.

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Urwat Zubairu Jibril
25/05/2026

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Urwat Zubairu Jibril

Mutane sun yi hawaye lokacin da wannan bawan Allah yake ba da labarin yadda halittarsa ta koma haka. Innalillah wa'inna ...
25/05/2026

Mutane sun yi hawaye lokacin da wannan bawan Allah yake ba da labarin yadda halittarsa ta koma haka. Innalillah wa'inna ilaihi rajiun!

ฦ˜iyayya gaskiya ce, tun yana yaro ฦ™anin mahaifinsa ya masa wannan illa da mugunta kamar yadda kuke gani saboda mahaifinsa ba ya nan kuma mahaifiyarsa ta fita!

Ba kowa ya tsaya ya ฦ™arasa jin labarin ba saboda yadda bawan Allahn yake ba da labarin abin ba daษ—in ji malam, rashin imanin ya kai inda ya kai. ฦŠaukar sa ya yi ya fita da shi ya watsa masa ruwan batir ษ—in a kansa da kuma bakinsa kuma ya dawo da shi cikin gidansu ya ajiye. Kamar yadda shi ya yake faษ—a da bakinsa!

In har ba ka ษ—auki darasi da ฦดan'uwan Annabi Yusuf ba to lallai ba za ka ษ—auki darasi ba. Allah ne fa ya faษ—a a littafinSA. Shi ya sa wannan labarin bawan Allahn bai ban mamaki sosai ba, ษ—an'adam ba abin da ba zai iya ba a kan ฦ™iyayya.

Maฦ™iyi abin gudu ne, ka yi nesa da shi, ba a zama da shi, wanda bai ฦ™aunar ka zai iya maka komai na cutarwa a rayuwa. Haka kawai wani ko wata za ta cutar da ฦดaฦดanku saboda kyawunsu ko hassada ko wani abu daban. Ko makaranta yara s**a tafi ku tabbata suna hannu mai aminci daga zuwansu zuwa dawowansu. Wannan zamani cike yake da abubuwan mamaki da mugaye!

Ya buฦ™aci addu'a daga wajen ฦดan'uwa a kan Allah ya ฦ™ara masa lafiya sannan ya masa sakayya a kan wannan ฦ™anin mahaifin nasa.

Allah ka ba shi lafiya, ka kare mu daga zama da mutane marasa imani.

Nigerian news hausa

Yanzu yanzu: INNA LILLAHI WA-INNA ILAIHIR RAJIUN..๐Ÿ˜ญYanzu na ke samun labarin Allah ya yi wa Jaruma Wasila Isma'il rasuwa...
24/05/2026

Yanzu yanzu: INNA LILLAHI WA-INNA ILAIHIR RAJIUN..๐Ÿ˜ญ

Yanzu na ke samun labarin Allah ya yi wa Jaruma Wasila Isma'il rasuwa๐Ÿ˜ญ

17/05/2026

Illar harshe

17/05/2026
Tambihi Akan adduar malam fantami akan PDP
17/05/2026

Tambihi Akan adduar malam fantami akan PDP

YAU CE RANAR HAWAN JINI TA DUNIYA | To ko me hawan jini ke nufi?Hawan jini matsala ce da a yau ta zama ruwan dare a ciki...
17/05/2026

YAU CE RANAR HAWAN JINI TA DUNIYA | To ko me hawan jini ke nufi?

Hawan jini matsala ce da a yau ta zama ruwan dare a cikin al'umma, duk da irin haษ—arin da hawan jinin ke da shi ga lafiya. Hawan jini matsala ce da ake tabbatar da ita da magwajin hawan jini. Magwajin hawan jini yana auna hawa ko saukar batsewar jini a cikin jijiyoyin jini. A yayin da magwajin hawan jini ya nuna batsewar jini ta hau a cikin jijiyoyin jini hakan na nufin ฦ™arin wahalar harba jini zuwa jijiyoyin jini ga zuciya. Haka nan, idan jini ya hau, haษ—arin fashewa ko bullin siraran jijiyoyin jini zai ฦ™aru musamman a cikin ฦ™waฦ™walwa. Saboda haka ne, hawan jini yake gaba-gaba wajen haddasa shanyewar ษ“arin jiki.

ฦ˜ungiyar Kula da Hawan Jini ta Duniya ce ta ware duk ranar 17 ga watan Mayun kowace shekara domin wayar da kan al'ummar duniya kan hawan jini, matakan kariya, muhimmancin gwaji don gano hawan jini tun da wuri da kuma shawo kansa idan an tabbatar da shi.

Taken ranar na bana shi ne: "shawo kan hawan jininka tare" Ma'ana, rana ce da ya kamata ka je a gwada jininka da magwajin hawan jini, idan jinin ya hau, sai a ษ—auki matakan shawo kansa don yin rayuwa mai tsayi.

Saboda bincike ya nuna cewa fiye da kaso sittin cikin ษ—ari (60%) na masu hawan jini suna nan a tsakankanin al'umma amma ba a kai ga gano su ba, sadoda rashin zuwa asibiti domin binciken lafiya akai-akai. Wannan ya sa hawan jini ke yi wa masu fama da shi 'kisan mummuฦ™e' kafin a gano shi.

Wani abun mamaki ga hawan jini shi ne jinin zai iya hawa sosai-sosai amma ba tare da mutum ya ji wata alama a jikinsa ba, wannan ya sa sau da yawa ba a gano hawan jinin har sai ya fara lahani ga zuciya, ฦ™oda da sauran sassan jiki. Saboda wannan dalili ne ake yi wa hawan jini take da cuta 'mai kisan mummuฦ™e'.

Daga cikin matakan rage hawan jini ba tare da shan magungunan hawan jini ba akwai:

1) Sanin lambobin gwajin jininka a magwajin hawan jini.

2) Zaษ“ar abincin da ke daga tsirrai ko ciyayi.

3) Rage cin gishiri zuwa ฦ™asa da cikin mitsitsin cokalin shayi, wato ฦ™asa da giram biyar (5 gram) a kowace rana.

4) Cin sinadarin 'potassium' wanda ganyayyaki da 'ya'yan itatuwa ke ษ—auke da shi.

5) Rage teษ“a/ ฦ™iba.

6) Motsa jiki/atisaye akai-akai.

7) ฦ˜aurace wa giya da dangoginta.

8) ฦ˜aurace wa shan taba-sigari da dangoginta.

Bugu da ฦ™ari, atisaye na da muhimmancin gasken-gaske ga lafiyar zuciya, jijiyoyin jini da huhu kamar haka:

a) ฦ˜arfafa tsokar zuciya da kuma lausasa jijiyoyin jini yadda zuciya za ta harba isashshen jini zuwa dukkan sassan jiki a sauฦ™aฦ™e kuma cikin ฦ™anฦ™anin lokaci.

b) Buษ—e sassan huhu don ษ—aukar isashshiyar iskar oksijin zuwa cikin jini.

c) Share kiste daga jijiyoyin jini.

d) Daidaita ruwan jiki da sauran sinadarai, da dai sauaransu.

Sai dai, ษ—abi'ar nan ta fara atisaye ko motsa jiki gabagaษ—i ba tare da tuntuษ“ar masana ba na da haษ—arin gaske musamman ga masu hawan jini, ciwon zuciya ko ciwon siga. Saboda atisaye ana auna shi ne tamkar yadda ake auna magani a asibiti bayan an yi la'akari da:

1) Lambobin gwajin hawan jini

2) Shekaru

3) ฦ˜arfin bugun zuciya

4) ฦ˜arfin ษ—aukar iskar oksijin

Bayan anyi amfani da waษ—annan alฦ™aluma ne za a fitar da tsararre kuma ฦ™ayyadajjen atisaye na musamman wanda zai wa zuciya, jijiyoyin jini da huhu amfani ba tare da haifar da wata illa ba.


Kuma ga kowane mai hawan jini, za ai amfani da alฦ™alumansa ne kawai domin fitar masa da adadin atisayen da zuciyarsa da huhunsa za su iya ษ—auka. Wannan zai magance faษ—uwa katsam ko ma mutuwa yayin atisaye/motsa jiki.

Daga ฦ™arshe ya kamata kowa ya san matsayinsa game da gwajin hawan jini a yau! Sannan a tuntuษ“i likitocin fisiyo kafin fara atisaye domin tsara atisayen da zai amfani jiki sannan a kauce wa matsalar bugun zuciya

ยฉPhysiothe

17/05/2026

Shin akwai Aya ko Hadisi da ya halatta ko haramta buruji ko falaki da ake yi kafin a zabi matar aure? Saikaji su ce gidan 9 dss?

Address

Kano
23477

Telephone

+2348032577322

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when DARMA TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to DARMA TV:

Share