TIME OUT HAUSA

TIME OUT HAUSA Labarai | Shirye - shirye | Wasanni | Nishadi
(3)

Ɗan Majalisar Wakilai na Kano, Sagir Koki ya bar jam'iyyar NNPP Ɗan majalisar wakilai mai wakiltar daga mazabar Birnin K...
12/11/2025

Ɗan Majalisar Wakilai na Kano, Sagir Koki ya bar jam'iyyar NNPP

Ɗan majalisar wakilai mai wakiltar daga mazabar Birnin Kano, Injiniya Sagir Ibrahim Koki, ya sanar da focrwar sa daga jam'iyyar NNPP mai mulki a jihar.

A wata wasika mai ɗauke da kwanan wata 11 ga Nuwamba, 2025, Koki ya bayyana cewa rikicin shugabanci da ke kara tsananta a cikin jam’iyyar ne ya sa ya ɗauki wannan mataki.

A wasiƙar da aka aika wa shugaban jam'iyyar na mazaɓar Zaitawa da ke cikin Ƙaramar Hukumar Birnin Kano, Koki ya ce ya yanke wannan shawara ne bisa haƙƙinsa na doka da ya ba shi ‘yancin zaɓin jam'iyyar da zai shiga.

Ya bayyana cewa rikicin cikin gida da ke tsakanin shugabannin jam’iyyar a matakin ƙasa ya sanya ya ji cewa da wuya ya ci gaba da zama a jam'iyyar.

Ku zo mu tattauna!Shin me ya sa mafi yawancin gidajen abincin da s**a shahara, maza ne suke yi musu girki? Shin hakan na...
09/11/2025

Ku zo mu tattauna!

Shin me ya sa mafi yawancin gidajen abincin da s**a shahara, maza ne suke yi musu girki?

Shin hakan na nufin maza sun fi mata iya girki kenan?

Ko kuwa dai akwai wani ɓoyayyen dalili?

Wakilin ma'aikatar harkokin wajen Saudiyya Amb. Ahmed Sule tare da shugaban Hukumar jin daɗin Alhazai ta kasa Farfesa Ab...
09/11/2025

Wakilin ma'aikatar harkokin wajen Saudiyya Amb. Ahmed Sule tare da shugaban Hukumar jin daɗin Alhazai ta kasa Farfesa Abdullah Saleh Usman Pakistan, tare da mataimakin Ministan aikin Hajjin ƙasar Saudiyya Abdulfatah Mashat da mai taimaka masa Dr. Badr Al-Sulami, sun rattaɓa hannu kan sabuwar yarjejeniyar aikin Hajjin bana a yau Lahadi a birnin Jeddah.

Su Wa Za Ka Fi Bawa Maki Bisa Ķoƙarin Rike Aikin Su Da Amana?1. EFCC2. DSS3. Army4. Airforce5. Navy6. Police7. Civil Def...
09/11/2025

Su Wa Za Ka Fi Bawa Maki Bisa Ķoƙarin Rike Aikin Su Da Amana?

1. EFCC
2. DSS
3. Army
4. Airforce
5. Navy
6. Police
7. Civil Defence
8. Correctional Service
9. Immigration
10. VIO
11. Customs

Babbar kotun kolin Guinée Conakry ta yi watsi da takardun neman takarar shugaban kasa na a kalla mutane 30, tare da amin...
09/11/2025

Babbar kotun kolin Guinée Conakry ta yi watsi da takardun neman takarar shugaban kasa na a kalla mutane 30, tare da amincewa da na 'yan takara 9 ciki har da shugaban gwamnatin mulkin sojan kasar Mamadi Doumbouya

Matsalar Tsaro: Birtaniya ta gargadi ƴan ƙasar ta da su gujewa zuwa jihohi 21 a Najeriya Ofishin Harkokin Waje na Birtan...
09/11/2025

Matsalar Tsaro: Birtaniya ta gargadi ƴan ƙasar ta da su gujewa zuwa jihohi 21 a Najeriya



Ofishin Harkokin Waje na Birtaniya (FCDO) ya shawarci ‘yan Birtaniya da su guji tafiya zuwa jihohi 21 a Najeriya saboda karuwar rashin tsaro.

TheCable ta rawaito cewa sanarwar ta ce sace-sace da laifukan tashin hankali, da rikicin kabilanci suna yaduwa a fadin kasar nan.

A arewa maso gabas, Birtaniya ta ce kada a yi tafiya zuwa Borno, Yobe, Adamawa da Gombe, yayin da Bauchi za a iya zuwa ne kawai idan ya zama wajibi.

A arewa maso yamma, an gargaɗi yan ƙasar yin tafiya zuwa Katsina da Zamfara yayin da Kaduna, Kebbi, Jigawa da Sokoto za a iya zuwa idan ya zama wajibi.

A kudu maso gabas, an yi gargadi kan tafiya zuwa Abia da Anambra da Imo da wasu sassa na Delta, Bayelsa da Rivers. A Legas, an yi gargadi kan yawan laifuka musamman a bangaren mainland.

Birnin Abuja ma ya jawo damuwa saboda tashin hankali da zanga-zanga.

Bikin al’adu na jami’ar Bayero Kano na 2025. Bikin da aka gudanar a ranar Asabar, an shirya shi ne domin nuna al’adu, ha...
09/11/2025

Bikin al’adu na jami’ar Bayero Kano na 2025.

Bikin da aka gudanar a ranar Asabar, an shirya shi ne domin nuna al’adu, haɗin kai da ɗabi’u a tsakanin mabambantan ƙabilu a jami’ar ta Bayero.

Mabiya addinin Sikh na Indiya sun nufi Pakistan a iyakar kasashen biyu da ke Wagah, a jajibirin bikin ranar haihuwar Gur...
04/11/2025

Mabiya addinin Sikh na Indiya sun nufi Pakistan a iyakar kasashen biyu da ke Wagah, a jajibirin bikin ranar haihuwar Guru Nanak, wanda ya kafa addinin Sikh. (Bilkisu)

RAN MAZA YA ƁACI: Muna Jiran Amurka Da Ta Harbo Duk Abin Da Za Ta Harbo, Amma Babu Wani Makami Ko Guda Ɗaya Da Za Mu Bar...
04/11/2025

RAN MAZA YA ƁACI: Muna Jiran Amurka Da Ta Harbo Duk Abin Da Za Ta Harbo, Amma Babu Wani Makami Ko Guda Ɗaya Da Za Mu Bari Ya Wuce Sararin Samaniyarmu Ya Shiga Nijeriya Ba Tare Da Mun Kakkaɓi Shi Ba. Kuma Muna Shirye Mu Yi Yaƙi Da Amurka Matuƙar Ta Yi Gangancin Kai Wa Ƴan'uwanmu Nijeriya Hari, Cewar Shugaban Ƙasar Jamhuriyyar Nijar Gen Tchiani

Me za ku ce?

Cikin Hotuna : Yadda tawagar sojojin Najeriya ta ziyarci Makarantar Kwamandoji ta Mountain Commando da Cibiyar Horar da ...
04/11/2025

Cikin Hotuna : Yadda tawagar sojojin Najeriya ta ziyarci Makarantar Kwamandoji ta Mountain Commando da Cibiyar Horar da Sojoji da ke birnin Isparta na yammacin Turkiyya a ranar Talatar nan.

TRT Hausa.

Address

Ring Road
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when TIME OUT HAUSA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share