Gwoza Press

Gwoza Press Mun buɗe wnn page ne a madadin Gwoza Media Forum kuma saboda turo da abubuwa daya shafi Harka....

AN GUDANAR DA MUZAHARAR QUDS A GWOZA.A yau Juma'ah 13-03-2026 Yan'uwa Musulmai Almajiran Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) na ...
13/03/2026

AN GUDANAR DA MUZAHARAR QUDS A GWOZA.

A yau Juma'ah 13-03-2026 Yan'uwa Musulmai Almajiran Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) na Da'irar Gwoza sun gudanar da Jerin Gwanon lumana na Quds kamar yadda sauran Al'Umman Musulman Duniya sukeyi, wannan muzaharar an gudanar da shine domin nuna goyon baya ga Al'ummar Palastinawa bisa zaluncin da ake nuna musu shekaru dayawa, Kamar yadda Imam Khumaini (QS) ya assasa Jummar karshen Ramadan ya zamo ranar Tunawa da Al'ummar Palastinawa da kuma Masallacin Quds,

Alhamdulillah anyi Muzahara lapiyah kuma an tashi lapiyah, Ga wasu Hotona daga gun Muzaharar.






13_03_2026

Mojtaba Khamenei ya gaji mahaifinsa a matsayin jagoran addinin Iran.An nada dan marigayin a wannan mukami yayin da ake d...
08/03/2026

Mojtaba Khamenei ya gaji mahaifinsa a matsayin jagoran addinin Iran.

An nada dan marigayin a wannan mukami yayin da ake dab da cika kwanaki 10 da barkewar yaki a tsakanin Iran da Amurka da Isra‘ila wanda ya tsayar da harkoki a yankin Gabas ta Tsakiya.

- DW Hausa

Qur'an day na bikin yar uwa Maryam Ahmad Grema. HML Sister Maryam. Allah ya basu zaman lafiya da zuri'a dayyiba.Photo Cr...
16/01/2026

Qur'an day na bikin yar uwa Maryam Ahmad Grema. HML Sister Maryam. Allah ya basu zaman lafiya da zuri'a dayyiba.

Photo Credit- Al_Qarrar.

DALIBAN HAUZAH ILMIYYA SUN ZIYARCI JAGORA (H)Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)‘Yan uwa daliban Hauzah Ilmiyyah, d...
15/10/2025

DALIBAN HAUZAH ILMIYYA SUN ZIYARCI JAGORA (H)

Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)

‘Yan uwa daliban Hauzah Ilmiyyah, daga kasashen Iran, Iraq, Lebanon, Nijar da Mali sun gana da Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a gidansa da ke Abuja, a yammacin Talata, 20 ga Rabi’ul Thani, 1447 (14/10/2025).

Da yake jawabi ga maziyartan, Jagoran ya bayyana manufar ganawar, inda ya ce, don a tunatar da juna ne akan muhimmancin abinda s**a saka a gaba, ta yadda su kansu za su daura damara su dauki karatun da muhimmanci. “Ku san cewa kuna yin wannan (karatun) ne a matsayin sadaukarwa a madadin dukkanin al’umma.”

Jagora ya tunatar da su muhimmancin tsayuwa da karantar da mutane ilimi, ba kawai wa’azi irin yadda yanzu ake yayin masu wa’azi daban-daban a kasar nan suna yi a sigar hayaniya ba. Yace: “A zauna a yi karatu, a dauko littafi daga bango zuwa bango a karanta kowace kalma sanka-sanka a bi ta da bayani a wuce a sauke, sannan a dauko wani a sake sawa daga bango zuwa bango.”

Shaikh Zakzaky ya bayyana musu cewa, yana da kyau yin ma mutanen gari wa’azi. “Wa’azin da zai iya hada kan al’umma da fahimtar al’umma Musulmi a matsayin abu guda, wannan yana da kyau, ba wanda zai rarraba su ba.” Ya jaddada cewa: “ Amma karantarwa shi ne ‘ahammus shay’i.”

Jagoya ya ce, mutum ba zai karantar da ilimi ba, har sai in ya yi karatu, shi kuma karatun ana sadaukarwa ne a dauki lokaci a yi shi. Inda ya bukaci da su zama misalin kendir, wanda yake kona kansa don ya haska waje. “Abinda ya kamata ma’abota karatu su kasance kenan, su kona kansu don wasu su samu hasken ilimi.”

Ya kuma jaddada musu hadafin karatun a matsayin karatu don a karantar, inda ya ba da misali da yadda Malaman Zaure a kasar Hausa kan sadaukar su yi karatu mai zurfi don su karantar da sauran al’umma.

Jagora ya gargadi daliban ilimin akan tsayawa kyam akan tafarkin addini, ba tare da karkata ga azzalumai ba. Ya ce: “Abinda (wasu) suke ta kokarin su nuna mana shi ne, a zauna lafiya da hukuma. Mu ba mu ce ba za mu zauna lafiya da hukuma ba, amma a wane unwanin? A unwanin muna yaransu? Haihata! Haihata minnaz zilla! Haihata!”

Ya bayyana cewa, amma idan zama lafiya da su din a muna matsayin daidai da su ne, suna ganin mu ma ‘entity’ ne, suna bukatarmu, har suna neman abu a wajenmu, to Masha Allah, ka ga cigaba ne wannan. “Amma ka je a wulakance, kamar masu zuwa rarakan nan, har da cewa wai su ba a san da su ba, ba a yi da su, alhali suna da yawa suna da kaza, amma ba a wakiltansu…. To kaskanci ne wannan.”

Shaikh Zakzaky ya ce, abinda yanzu ake ta kitsa ma mutane kenan, su zauna lafiya da azzalumai. “Ban ki ba, idan mutum ya ga shi yanzu ba zai iya tsayawa kyam ya yi gwagwarmaya ba, ya koma waje daya ya ce koyarwa zan yi. Ba zan zarge shi ba.”

Ya ce: “Amma ya koyar din ne kawai, kada ya bude bakinsa ya ce masu gwagwarmaya laifi suke yi. Tunda shi ba zai iya ba, ya ja bakinsa ya tsuke, ya shiga lungu ya koyar. Ba zai iya wannan ba? To ya yi wannan din, amma kar ya zo ya ce, wadannan da suke wannan abin su bari.”

Ya kara da cewa: “Kowa ya yi nasa. Sadaukarwa ne, in ba za ka sadaukar ba, wani zai yi. An fahimta ai.”

Jagora ya ce, masu ganin cewa zama da mahukunta lafiya shi ne ‘aula’. Sai in ce, da haka nan ne, da Imam Husaini (AS) ya zauna lafiya da Yazidu, da ba a cire masa kai ba. Kuma na san ba za ka fi shi ganin maslahar al’ummar nan ba. Yace: “Yanzu irin wannan da’awar, su suna ganin kamar mu ne muke jefa kanmu a cikin wahala, mu muka ja ma kanmu.”

Don haka ya jaddada kira ga daliban ilimin akan lallai su san hadafin da ya kai su karatun. Wanda yace, hakan muhimmin abu ne. Ya yi musu nasiha akan su tsayu da karban karatu ne daga Malaman da suke karatu a wajajensu, amma su bar musu Fikirorinsu matukar ba ya dace da Fikirar da suke kai ne ba. “Da yake akwai masu Tunani daban daban a Hauzozi, a yi karatun kawai. Luga ne, ya iya Luga, ya koya maka Luga. Fiqihu ne ya iya, ya koyar. Usul ne ya iya, ya koyar. Amma ra’ayinka daban nasa daban, ya rike ra’ayinsa ka rike naka. Allahumma sai dai in ra’ayin naku iri daya ne, amma ba ka je ne a canza maka tunani ba. Yana da muhimmanci ka san diban karatun za ka yi don ka amfana, wani ya amfana da kai.” Ya jaddada.





14/10/2025

SHI NE HAKIKANIN MU!  Ahmad ga sallamar mu_________gareka Yaa Commander!!!🙌🥀❣️😍
14/10/2025

SHI NE HAKIKANIN MU!
Ahmad ga sallamar mu_________gareka Yaa Commander!!!🙌🥀❣️😍

Shahidi Ahmad Zakzaky: Makwafin Matasa Wajen Sadaukarwa-Aisha Kazimiyyah Wato na lura idan kace za ka yi magana akan wan...
13/10/2025

Shahidi Ahmad Zakzaky: Makwafin Matasa Wajen Sadaukarwa

-Aisha Kazimiyyah

Wato na lura idan kace za ka yi magana akan wannan bawan Allah, sai ka rude, shiga cikin al'amarinsa akwai rudarwa, kawai sai dai shiru sai uhum, amma ba dai mutum ba.

Tabbas Shahidi Ahmad Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) wani babban misali ne na sadaukarwa da jajircewa musamman ga matasa a Harkar Musulunci karkashin jagorancin mahaifinsa, Sayyid Ibrahim Zakzaky. Zan ɗanyi tsokaci a kan Shahid Ahmad Zakzaky a matsayin Makwafin Matasa da kuma yadda ya sadaukar da rayuwarsa wajen taimakon Sayyid Zakzaky, tare da nuna wa matasa nauyinsu da kuma taimaka musu wajen saukewa ɗin.

Shahidi Ahmad Zakzaky (H) ba ma sa shi a lissafin don ya kasance kawai ɗan Jagora ba, a'a muna zama ne don mu lissafo shi a zaman da yayi na wani Makwafi (wani abin koyi da misali) na haƙiƙa ga daukacin matasan Harkar da ma sauran matasa masu neman adalci da canji.

Rayuwarsa gajeriya ce, amma mai cike da albarka da sadaukarwar da ta nuna wa matasa matsayinsu da kuma nauyin da ke kansu wajen goyon bayan gaskiya da kuma hidimar Addini. Taimakon Shahidi Ahmad ga Sayyid Zakzaky (H) ya wuce na yaro ga mahaifi. Ya kasance taimako ne na Mabiyi ga Jagoransa a tafarkin Ubangiji.

A aikin Shahidi Ahmad, na kan sama nai ta irin wasu tunani, ganin yadda ya karantu sosai a fannin (Chemical Engineering) kuma a kasar China. Amma duk da haka, ya yi amfani da damarsa da lokacinsa wajen taimakon Sayyid Zakzaky a dukkan harkokin al'umma. Yakan dawo, ya rungumi aikin da ke gaban Harkar Musulunci da hannu biyu, ya ajiye damuwar duniya a gefe ya samar da mafita.

A Jagorancin Matasa da Harkokin Tsaro ya sa muke ce masa kwamanda. Yana daga cikin manyan kokarinsa na kafa rundunar matasa mai suna Mu'assasatu Abul Fadlul Abbas (A.S.) Wannan ba wai ya nuna karfin tunaninsa da hangen nesansa ba ne, har ma ya nuna yadda yake daukar nauyin kare Jagora da kuma harkar.

Ya shiga cikin sahun gaba a bangaren tsaro na Harkar Musulunci, inda ya nuna jajircewa da sadaukarwa a fili, wanda an shaidi hakan. Babban darasi na sadaukarwarsa shi ne shahadarsa. A ranar Qudus (Juma'a ta karshe ta watan Ramadan) a shekara ta 2014, yayin wata zanga-zanga ta lumana a Zaria domin goyon bayan al'ummar Falasdinu, sojoji sun bude musu wuta tare da wasu 'yan uwansa biyu (Mahmud da Hameed), da kuma wasu 'yan uwa fiye da 30, sun yi shahada a wannan rana.

Wannan Shahada a fili, a lokacin da yake aikin Addini na goyon bayan al'ummar da aka zalunta, ta tabbatar da cewa ya sadaukar da rayuwarsa gaba daya domin tafarkin Abba (H), wanda ke kira zuwa ga adalci da karin kai (resistance).

Wani abin burgewa shi ne, nunawa Matasa nauyinsu da taimaka musu wajen saukewa. Domin Rayuwa da shahadar Shahid Ahmad sun isar da muhimman darussa guda biyu ga matasa:

1- Ayyana Nauyin Matasa (Tarbiyya da Jagoranci). Ilimi da Aiki Tare: Ya nuna cewa matasa su yi karatu mai zurfi na addini da na zamani, amma kuma su gane cewa ilimin nasu hidima ce ga Addini. Ya ajiye makomarsa ta rayuwar duniya gefe don hidimar Jagoransa, yana mai nuna cewa makomar matashi tana cikin bautar Allah da tallafa wa Jagoranci.

Jajircewa da Sadaukarwa, shi ne ya nuna cewa matasa su ne jigon kariya da goyon baya. Ta hanyar kafa rundunar tsaro ta matasa, ya sanya matasa a sahun gaba, ya koyar da su yadda ake jurewa da sadaukar da rai wajen kare Jagora da akida.

2- Taimaka Musu Wajen Sauke Nauyin. Goyon Bayan Mazlumi (The Oppressed): Ya yi shahada a yayin nuna goyon baya ga Falasdinu, wanda shi ne tsarin da Sayyid Zakzaky ya daɗe yana koyarwa. Wannan ya koya wa matasa cewa nauyin su ba wai a cikin gida ka ɗai yake ba, har ma a duniya wajen taimakon dukkan wanda aka zalunta.

Shahadar sa ta zama hujja karara cewa sadaukarwa ga tafarki na gwagwarmayar addini tana da tsada, kuma matasa su shirya bada komai, har da rayukansu. Ya zama mai kwadaitarwa ga matasa da yawa, cewa matsayinsu na matasa a tafarkin Jagora yana da daraja fiye da duk wani abu na duniya.

Shahidi Ahmad Ibrahim Zakzaky ya kasance Gwarzon Matasa wanda ya zana cikakken hoton sadaukarwa, daga bautar ilimi da aiki zuwa jajircewar kariya da kuma bayar da rai. Ya tabbatar da cewa mafi girman gudunmawar da matashi zai bayar ga Jagoransa da Addininsa shine ya rayu da akidar, kuma ya mutu a kai.

Idan Kaji Daɗin Ganin Hoton Commander Ka daure kayi Salaty Hadiyyah Izuwa ga Ruhinsa Mai Tsarki. 🥰 CHECK COMMENTS Domin ...
13/10/2025

Idan Kaji Daɗin Ganin Hoton Commander Ka daure kayi Salaty Hadiyyah Izuwa ga Ruhinsa Mai Tsarki. 🥰 CHECK COMMENTS Domin Ganin Asalin Hoton.👇👇👇

A jiya Lahadi 28/09/2025, Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) ya amshi baƙuncin Gidajan Malamai daga birnin Zazzau da s**...
29/09/2025

A jiya Lahadi 28/09/2025, Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) ya amshi baƙuncin Gidajan Malamai daga birnin Zazzau da s**a haɗa gidan Kona, gidan sarkin Ladanai, gidan Sheikh AbdulQadir Banufe, gidan Alhazawa, gidan marigayi Sheikh Aliyu Mai Yasin wanda Sheikh Muhammad Zakir Shamsuddeen (Young Sheikh) ya wakilta, Gidan Limamin Zabi Gidan Limamin Dogarawa da kuma Malam Sunusi Mai Ashafa, da gidan Sheikh Ibraheem Kakaki.

Malaman sun jajantawa Jagora (H) bisa ga waƙi'ar buhari (L) na shahadar Almajirai da Ƴaƴansa, sannan sunyi Addo'ar Allah ya amshi shahadar su.

Jagora (H) ya yi masu ta'aziyyar wasu malaman da aka rasa ya roki Allah ta'ala ya gafarta masu, sannan ya aika da saƙon gaisuwa ga sauran ƴan'uwa da masoya.







28/09/2025

Barkanmu da Jumma'a!🌺🥰Muna taya al'ummar musulmai murnar bikin Maulidin cika shekaru 1500 da haihuwar Annabi Muhammad. A...
05/09/2025

Barkanmu da Jumma'a!🌺🥰

Muna taya al'ummar musulmai murnar bikin Maulidin cika shekaru 1500 da haihuwar Annabi Muhammad. Allah ya kara mana son Annabi Muhammad(S.A.W.W). Ehlahy.

Address

Kano

Opening Hours

09:00 - 17:00

Telephone

+2348122915559

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Gwoza Press posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Gwoza Press:

Share