GIDAN YANCI

GIDAN YANCI THIS PAGE WAS CREATED FOR HELPING YOU KNOW WHAT GOING ON AROUND THE GLOB.

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne yayin wani taro da masu ruwa da tsaki na jihar ranar Laraba.Abb...
01/08/2024

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne yayin wani taro da masu ruwa da tsaki na jihar ranar Laraba.

Abba Kabir ya kuma yi gargaɗin cewa gwamnati ba za ta lamunci tayar da hargitsi yayin zanga-zangar ba.

Cikin Lumana An Fito Zanģa-Zañga A Birnin Dutse Jihar Jigawa
01/08/2024

Cikin Lumana An Fito Zanģa-Zañga A Birnin Dutse Jihar Jigawa

Idan Har Gwamnati Ba Ta Yi Abinda Ya Dace Ba, Nima Ina Cikin Masu Fita Zanga-zanga, Cewar Fitaccen Mawaƙi Naziru Sarkin ...
01/08/2024

Idan Har Gwamnati Ba Ta Yi Abinda Ya Dace Ba, Nima Ina Cikin Masu Fita Zanga-zanga, Cewar Fitaccen Mawaƙi Naziru Sarkin Waka

Matasa sun Tare Hanyar Nasarawa a Birnin Kano.
01/08/2024

Matasa sun Tare Hanyar Nasarawa a Birnin Kano.

Masu zanga zangar tsadar rayuwa sun fito a Abuja babban birnin Najeriya duk da matakan tsaron da aka dauka. Nan gaba kad...
01/08/2024

Masu zanga zangar tsadar rayuwa sun fito a Abuja babban birnin Najeriya duk da matakan tsaron da aka dauka. Nan gaba kadan kai tsaye zamu kawo muku abinda ke faruwa.

Gwamnatin Najeriya na nuna damuwa kan rashin isassun kuɗin aikin ƙidayar jama'aClem AgbaClem Agba/TwitterCopyright: Clem...
07/03/2023

Gwamnatin Najeriya na nuna damuwa kan rashin isassun kuɗin aikin ƙidayar jama'a
Clem Agba

Clem Agba/TwitterCopyright: Clem Agba/Twitter
Ƙaramin ministan kasafin kuɗi da tsare-tsare na Najeriya Clem Agba, ya bayyana damuwa kan tasirin da rashin isassun kuɗi da matsalar tsaro da kuma bambance-bambancen al'adu za su yi wa aikin ƙidayar jama'a da za a yi a ƙasar cikin wannan shakara.

An dai tsara gudanar da ƙidayar ne tsakanin ranakun 29 ga watan Maris zuwa biyu ga watan Afrilun wannan shekara.

Mista Agba ya bayyana hakan ne ranar Litinin a wata ganawa da ya yi da ƙungiyoyi masu zaman kansu da da sauran masu ruwa-da-tsaki a Abuja da nufin tattauna ɓangarorin da za su iya kawo tarnaƙi ga aikin ƙidayar.

Ministan ya ƙara da cewa gwamnati ta fitar da fiye da kashi 60 na kuɗaɗen da ake buƙata domin aikin, inda ya ƙara da cewa yanzu ana jiran masu ruwa-da-tsaki da ƙungiyoyi masu zaman kansu da su bayar da nasu kason.

Ganawar dai ita ce ta biyu da jami'an hukumar ƙidaya ta ƙasar ke yi da ƙungiyoyin da za su taimaka wajen gudanar da shirin a shirye-shiryen gabatar daƙidayar jama'ar.

Ɗaya daga cikin maƙasudin ganawar shi ne yadda za a samara kudin gabatar da ƙidayar, inda hukumar ya yi alƙawarin gudanar da komai a bayyane.

Duk da cewa an samu matsalolin tsaro a lokacin aikin gwajin da aka yi a wasu ƙananna hukumomin ƙasar, shugaban hukumar ƙidayar ya kawar da fargabar da wasu ke yi na cewa ba za a yi aikin a wasu sasan ƙasar nan.

INEC ta cire sunan Doguwa daga jerin zaɓaɓɓun 'yan majalisun tarayyaAlhasan Ado DoguwaFacebookCopyright: FacebookHukumar...
07/03/2023

INEC ta cire sunan Doguwa daga jerin zaɓaɓɓun 'yan majalisun tarayya
Alhasan Ado Doguwa

FacebookCopyright: Facebook

Hukumar zaɓen Najeriya ta cire sunan shugaban masu rinjaye na majalisar wakilan Najeriya Alhassan Ado Doguwa daga cikin jerin sunayen zaɓaɓɓeun 'yan majalisar wakilan ƙasar da s**a yi nasara a zaɓen da aka gudanar cikin watan Fabrairu.

Hukumar zaɓen ƙasar ce dai tun da farko ta ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen ɗan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar mazaɓar Doguwa da Tudunwada a jihar Kano da ke arewacin Najeriya.

Jami'in tattara sakamakon zaɓen Farfesa Ibrahim Adamu Yakasai ya bayyana cewa Doguwa na jam'iyyar APC ya samu ƙuri'a 39,732, inda abokin takararsa na jam'iyyar NNPP Yushau Salisu Abdullahi ya samu ƙuri'a 34,798.

To sai dai a jerin sunayen zaɓaɓɓun 'yan majalisun da hukumar zaɓen ta fitar a shafinta na Twitter, babu sunan Alhassan Ado Doguwa a cikin jerin 'yan majalisun.

INEC ɗin ta ce an tilasta wa jami'in tattara sakamakon zaɓen wajen bayyana sakamakon da ya bai wa Doguwa nasara a zaɓen da aka gudanar.

Gwamnatin Yobe ta ɗage haramcin hawa babura a wasu yankunan jihar bayan shekara 11Okada RidersGwamna Mai Mala Buni na ji...
06/03/2023

Gwamnatin Yobe ta ɗage haramcin hawa babura a wasu yankunan jihar bayan shekara 11
Okada Riders

Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe, ya sanar da ɗage haramcin amfani da babura a faɗin ƙananan hukumomi bakwai na jihar.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai bai wa gwamnan shawara kan harkokin tsaro Birgediya-Janar Dahiru Abdulsalam ya fitar wadda kuma aka raba wa manema labarai a Damaturu a yau Litinin.

A cewarsa, baburan za su yi aiki daga karfe 6 na safe zuwa 6 na yamma a kowace rana. Ya ce baburan ba za su ɗauki mutum fiye da ɗaya ba ko yin achaba.

Ya kuma yi kira ga dukkan waɗanda ke da babura a ƙananan hukumomin da abin ya shafa, da su tabbatar da cewa sun yi musu rajista.

Gwamnatin jihar ta kuma bai wa masu baburan umarnin cewa su yi aiki a iya ƙananan hukumomi da suke ba tare da shiga wasu wurare ba, inda ta ce duk wanda aka samu da laifin take umarnin, zai fuskanci hukuncin da ya kamata.

A shekara ta 2012 ne dai lokacin gwamnatin Ibrahim Gaidam, aka sanya haramci kan amfani da babura a faɗin jihar ko achaba da nufin dakile yunkurin amfani da su wajen aikata muggan ayyuka, musamman lokacin da rikicin Boko Haram ya yi kamari a jihar.

Sai dai gwamna Mai Mala Buni ya ɗage haramcin a kan wasu ƙananan hukumomi 10 cikin 17 na jihar a watan Janairun 2022.

Ana ci gaba da fuskantar ƙarancin man fetur a sassan Najeriya da damaPetrol ScarcityGetty ImagesCopyright: Getty ImagesA...
06/03/2023

Ana ci gaba da fuskantar ƙarancin man fetur a sassan Najeriya da dama

Petrol Scarcity
Getty ImagesCopyright: Getty Images
A Najeriya, 'yan ƙasar na ci gaba da nuna takaicinsu dangane da matsalar ƙarancin mai da ta ki ta ki cinyewa a sassa da dama, ciki har da Abuja, babban birnin ƙasar.

Mahukunta na danganta matsalar da dakatar da zirga-zirga da aka yi a lokacin zaɓen shugaban ƙasar da aka kammala a makon jiya.

Amma wasu kungiyoyin farar-hula na zargin cewa matsalar cin hanci da sakacin gwamnati ne s**a haddasa matsalar.

Gwamnati dai ta daɗe tana alwashin magance matsalar amma babu abin da ya sauya a birane da kauyakun ƙasar.

Abin da ke ɗaure kan `yan ƙasar game da wannan ƙarancin man shi ne iƙirarin da gwamnatin ke yi cewa a kowane wata tana kashe naira biliyan ɗari huɗu a kan tallafin man fetur.

Amma Mallam Awwal Musa Rafsanjani, wakilin kungiyar da ke yaki da rashawa ta Transparency International a Najeriya ya yi zargin akwai rashin gaskiya a cikin lamarin saboda wasu ne ke sama da faɗi da dukiyar kasa kuma an kasa hukuntasu.

Sai dai hukumar da ke kula da sarrafawa da tacewa da sufurin man fetur ta Najeriya, cikin wata sanarwar da ta fitar ta ce dakatar da zirga-zirgar da aka yi a lokacin zaben shugaban kasa da aka kamala a makon jiya, shi ne babban dalilin da ya janyo jinkirin wajen kai man wasu sassan kasar.

Amma masanin ya ce wannan ba hujja bane saboda tun kafin lokacin zaɓe ake samun matsalar ƙarancin man fetur.

Gwamnatin shugaba Buhari dai na tutiya da dokar man da aka zartar a zamaninta, tana saka dokar a cikin gadon da za ta bar wa `yan Najeriya, amma masu lura da al`amura na cewa wannan matsala ta rashin man fetur idan ba a magance ta ba, tana iya dusashe nasarori da dama da gwamnatin ke alfahari ta samu.

INA ZA KA SAMU KUDIN DA ZA KA SIYA MANA   GIDA DA MOTA SANNNAN KA KAI MU LANDAN.KAR KI DAMU YANZU TA JUYO MANA, JAM,IYUN...
06/03/2023

INA ZA KA SAMU KUDIN DA ZA KA SIYA MANA GIDA DA MOTA SANNNAN KA KAI MU LANDAN.

KAR KI DAMU YANZU TA JUYO MANA, JAM,IYUN LP DA PDP ZA SU JE KOTU.

ZABEN NAJERIYA YA GAZA CIMMA TSAMMANIN AL,UMMAR KASAR,AMERIKA.BidenSama da mako guda bayan gudanar da zaɓen shugaban ƙas...
06/03/2023

ZABEN NAJERIYA YA GAZA CIMMA TSAMMANIN AL,UMMAR KASAR,AMERIKA.

Biden

Sama da mako guda bayan gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya, Amurka ta ce zaɓen ya ya gaza cimma yadda 'yan ƙasar s**a yi tsammani.

Hukumar zaɓen ƙasar ta ayyana Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC a matsayin wadda ya lashe zaɓen da adadin ƙuri'u 8,794,726, tazarar ƙuri'a kusan miliyan biyu tsakaninsa da Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP.

Atiku mai shekara 76, ya samu ƙuri'a 6,984,520, yayin da Peter Obi na LP - wanda a ƙasa da shekara guda ya tara matasan mabiya- ya bayar da mamaki a takarar inda ya samu ƙuri'a 6,101,533.

To sai dai Atiku da Obi dukkansu sun yi zargin maguɗi a zaɓen, inda s**a sha alwashin ƙalubalantar nasarar Tinubu a kotu.

A wata sanarwa da Amurkan da fitar ta hannun jakadiyar ƙasar a Najeriya Mary Beth Leonard, ta ce 'yan Najeriya da dama sun fusata game da sakamakon, inda wasu s**a riƙa murna kan nasarar da s**a samu.

Sanarwar ta ƙara da cewa “A bayyane take cewa tsarin zaɓen Najeriya da aka gudanarar ranar 25 ga watan Fabrairu ya gaza cimma yadda 'yan ƙasar s**a yi tsammani,''

“Kamar yadda na sha faɗa a baya gabanin zaɓen, Najeriya ta cimma abubuwa masu yawa a tsawon shekaru sama da 20 da ta yi bayan komawa tafarkin dimoraɗiyya, kuma ci gaban da aka samu a fannin zaɓukan ƙasar na daga cikin nasarorin da ƙasar ta cimma''

“Yan Najeriya sun nuna sadaukarwarsu ga dimokraɗiyya ranar 25 ga watan fabrairu, to sai dai da yawa sun nuna fusata, yayin da wasu da dama s**a nuna murna bayan nasarar da s**a samu''.

Hukumar kula da kafofin yaɗa labaran Najeriya ta haramta sanya batutuwan addini da na ƙabilanci a shirye-shiryen siyasaN...
06/03/2023

Hukumar kula da kafofin yaɗa labaran Najeriya ta haramta sanya batutuwan addini da na ƙabilanci a shirye-shiryen siyasa

NBC
NBCCopyright: NBC
Hukumar kula da kafofin yaɗa labarai ta Najeriya ta ce ta lura da yadda ake sanya abubuwan da s**a shafi addini da ƙabilanci da kuma kalaman tunzura jama'a a shirye-shiryen siyasa da yaƙin neman zaɓe a yayin da ake fuskantar zaɓen gwamnoni a ƙasar.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce yin hakan ba zai zame wa ƙasar alkairi ba.

Hukumar ta ce doka ta tanadar da cewa dole kafofin yaɗa labarai su taimaka wajen jaddada hadin kan ƙasa tare da taimaka wa wajen inganta dimokradiyya.

Haka kuma sanarwar ta yi kira ga kafofin yaɗa labaran ƙasar da su yi amfani da kafofin nasu wajen daƙile wannan aƙida, da kuma kalaman tunzura jama'a da za su iya kawo barazana ga haɗin kai da dimokraɗiyyar ƙasar.

A cewar sanawar duk da cewa ana ƙarfafa wa kafofin yaɗa labarai gwiwwa wajen bai wa 'yan ƙasa damar bayyana ra'ayoyinsu, waɗanda ba kalaman ƙiyayya ko na cin zarafin juna ko na tunzura jama'a ba, ya kamata kafofin yaɗa labaran su san cewa za su yi hakan ne kawai ta hanyar da ta dace.

Article share tools

Address

Nasarawa LGA
Kano
700001

Telephone

+2349031770890

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when GIDAN YANCI posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to GIDAN YANCI:

Share