
08/10/2025
Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International, ta bukaci gwamnati ta gudanar da bincike cikin gaggawa kan kashe-kashe da cin zarafin bil’adama da ke faruwa a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya. Kungiyar ta ce rashin daukar matakin da ya dace daga gwamnati ya bar yankin cikin halin rashin doka da oda, inda duka gwamnati da wasu kungiyoyin da ba na gwamnati ba ke aikata laifuka masu tsanani, wanda ya jawo mutuwar akalla mutane dubu daya da dari takwas da arba’in da hudu tsakanin watan Janairu shekarar 2021 zuwa Yuni shekarar 2023.
Daraktan Amnesty International a Najeriya Isa Sanusi, ne ya bayyana haka yayin kaddamar da rahoton kungiyar mai taken Shekaru Goma na Rashin Hukunci Hare-hare da Kashe-kashe Ba bisa Ka’ida ba a Kudu maso Gabas a Jahar Enugu. Rahoton ya bayyana yadda ake yin kisa, azabtarwa, da bacewa ba tare da dalili ba, da kuma tsare mutane ba bisa doka ba, daga hannun ‘yan bindiga, kungiyoyin sa-kai, da ‘yan daba.
Kungiyar ta bayyana cewa tun bayan yadda hukumomin tsaro s**a danne zanga-zangar goyon bayan kafa kasar Biafra a shekarar 2015, yankin ya fada cikin mummunar halin zubar da jini da ya haifar da tsoro da rashin kwanciyar hankali. Rahoton ya bayyana yadda aka kashe fiye da mutane 400 a jihar Imo tsakanin shekarar 2019 da 2021, tare da lalata ofisoshin ‘yan sanda da na vigilante.
Amnesty ta kara da cewa ta rubuta wasiku ga gwamnoni na yankin Kudu maso Gabas don neman bayani kan matakan da suke dauka, amma babu wanda ya amsa. Kungiyar ta ce wannan shiru ya nuna rashin jajircewar gwamnoni wajen kawo karshen kisan da ya durkusar da rayuwar jama’a da tattalin arzikin yankin. Ta bukaci gwamnati ta dauki mataki cikin gaggawa don tabbatar da adalci ga wadanda abin ya shafa da kuma dawo da zaman lafiya a yankin.
Ruwan Dare Tv