AMC AREWA

AMC AREWA Domin samun sahihan labarai masu inganci cikin gaggawa, ku ci gaba da bibiyar shafinmu na AMC AREWA. Mun gode da goyon bayanku.

25/08/2026

Menene Amfanin wadan nan 'yan Ta'addan A najeriya

24/08/2026

An Gurfanar da wa danda Ake zargi da Kashe Malama Ummulkhari

Gwamnan Kano, ya yi maraba da shawarar Ƙungiyar Malaman Addinin Musulunci ta mara Tinubu baya a zaɓen shekarar 2027.Gwam...
24/08/2026

Gwamnan Kano, ya yi maraba da shawarar Ƙungiyar Malaman Addinin Musulunci ta mara Tinubu baya a zaɓen shekarar 2027.

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi maraba da shawarar Ƙungiyar Malaman Addinin Musulunci ta mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya a yunƙurinsa na sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2027.

An bayyana wannan matsayar ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ranar Lahadi.

Yusuf ya bayyana wannan goyon bayan a matsayin wani muhimmin ci gaba, yana mai cewa hakan ya nuna yadda malaman addinin Musulunci, limamai da shugabannin addini s**a tantance manufofi da shirye-shiryen gwamnatin Tinubu.

Ya ce wannan mataki ya nuna irin amincewar da ƙungiyar take da ita kan alkiblar da Gwamnatin Tarayya ta dosa, da kuma ƙudurinta na tallafa wa tsare-tsaren da ake ganin za su amfani ƙasar.

Ƙungiyar Malaman Addinin Musulunci ta ƙunshi malaman addinin Musulunci, limamai da shugabannin addini daga sassa daban-daban na ƙasar.

NDC ta musanta baiwa La’ah tikitin takarar gwamnan Kaduna.Jam’iyyar NDC ta musanta cewa ta bai wa Danjuma La’ah tikitin ...
24/08/2026

NDC ta musanta baiwa La’ah tikitin takarar gwamnan Kaduna.

Jam’iyyar NDC ta musanta cewa ta bai wa Danjuma La’ah tikitin tsayawa takarar gwamnan Jihar Kaduna a zaɓen gwamna na shekarar 2027.

Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa mai kula da Arewa, Alhaji Sidi Abdul Bomi ne, ya bayyana hakan a wata tattaunawar waya da manema labarai a ƙarshen mako. Ya yi watsi da wani takardar tikitin takarar gwamna da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta mai ɗauke da sunan La’ah, yana mai cewa ƙarya ce.

Wannan batu yazo ne a daidai lokacin da ake takaddama kan tikitin takarar gwamna na jam’iyyar a Jihar Kaduna, inda ake danganta Mohammed Abbas da La’ah da ikirarin samun takarar jam’iyyar daban-daban.

Bomi ya ce takardar da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta ba daga jam’iyyar ta fito ba, don haka bai kamata a dogara da ita a matsayin hujjar cewa La’ah ne ɗan takarar gwamna na NDC ba.

Barcelona Ta Doke Elche Da Ci 5-0 A Farkon La LigaBarcelona ta fara kare kambunta na La Liga da gagarumar nasara, bayan ...
23/08/2026

Barcelona Ta Doke Elche Da Ci 5-0 A Farkon La Liga

Barcelona ta fara kare kambunta na La Liga da gagarumar nasara, bayan ta doke Elche da ci 5-0 a ranar Lahadi.

Raphinha da Fermin Lopez ne s**a zura kwallaye biyu-biyu, yayin da Karim Adeyemi ya kara daya a wasansa na farko da Barcelona,Anthony Gordon kuma ya taimaka wajen samar da kwallaye biyu bayan shigarsa daga benci.

Raphinha, wanda ya taka leda a matsayin lamba tara, ya fara cin kwallo daga bugun fanareti a minti na 14 bayan Victor Chust ya yi masa keta a cikin fili. Daga bisani ya taimaka wa Adeyemi ya zura ta biyu kafin a tafi hutun rabin lokaci.

A zagaye na biyu, Gordon ya taimaka wa Raphinha ya zura kwallonsa ta biyu, sannan ya sake taimakawa Fermin Lopez ya ci ta hudu. Lopez ya kara zura ta biyu daga baya, inda Barcelona ta kammala wasan da nasara mai ci 5-0.

Za mu koyar da malamai irin huɗubobin da za su gabatar wa mabiya domin fahimtar muhimmancin sake zaɓen Shugaba Bola Ahme...
23/08/2026

Za mu koyar da malamai irin huɗubobin da za su gabatar wa mabiya domin fahimtar muhimmancin sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027 matsayin sa na musulmi ~ Shaikh Saleh Pakistan

Da Dumi-Duminsa: Saudiya Turkiya Da Pakistan Sun Gayyaci Iran Shiga Hadakar Tsaron Makka Don Yakar Kasar Isra'ilaAn gayy...
23/08/2026

Da Dumi-Duminsa: Saudiya Turkiya Da Pakistan Sun Gayyaci Iran Shiga Hadakar Tsaron Makka Don Yakar Kasar Isra'ila

An gayyaci Iran ta shiga ƙungiyar tsaron Makka
Rahotanni sun ce Iran ta samu gayyata daga Saudi Arabia, Turkiyya da Pakistan domin shiga sabon yarjejeniyar tsaron haɗin gwiwa ta Makka, wadda ƙasashen uku s**a kafa a baya-bayan nan.

Yarjejeniyar ta Makka ta tanadi ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro da soji tsakanin ƙasashen da s**a rattaba hannu, tare da manufar kare juna daga barazanar tsaro.

Idan har gayyatar Iran ta tabbata, shigar Tehran cikin wannan tsarin tsaro zai iya zama babban sauyi a tsarin siyasa da tsaron Gabas ta Tsakiya, musamman ganin cewa Iran da Saudi Arabia sun kasance masu hamayya a wasu batutuwan yankin.

Kaduna Ta Kara Kasafin Noma Zuwa N100bn A 2026 Saboda Karin Kason FAACGwamnatin Jihar Kaduna ta ce karin kudaden da jiha...
23/08/2026

Kaduna Ta Kara Kasafin Noma Zuwa N100bn A 2026 Saboda Karin Kason FAAC

Gwamnatin Jihar Kaduna ta ce karin kudaden da jihar ke samu daga Asusun Tarayya karkashin Shugaba Bola Tinubu ya taimaka wajen bunkasa ababen more rayuwa, biyan Naira biliyan 18 na bashin fansho da giratuti, da kuma kara kasafin noma daga Naira biliyan 1.4 a 2023 zuwa sama da Naira biliyan 100 a 2026.

Kwamishinan Yada Labarai da Al’adu na jihar, Ahmed Maiyaki, ya ce gwamnatin Gwamna Uba Sani ta gaji bashin fansho da giratuti na kusan Naira biliyan 24, amma zuwa yanzu ta biya kusan Naira biliyan 18.

Ya ce ana gudanar da ayyukan tituna 115 a kananan hukumomi 23 na jihar, wadanda s**a shafi sama da kilomita 1,400. Ya kuma ce karin kudaden noma sun ba gwamnati damar samar da taki, ban ruwa da tallafawa manoma.

Maiyaki ya ce gwamnati ta kuma ware sama da Naira biliyan 264 ga bangaren ilimi a kasafin 2026, tare da gina makarantu da gyaran dakunan karatu. Ya kara da cewa motocin CNG 100 da aka samar sun yi jigilar mutane kusan miliyan hudu cikin shekara guda, inda s**a ce sun rage musu kudin sufuri da kimanin Naira biliyan 4.

Gwamnatin Kano Ta Mika Makarantar Rano Ga Kwamitin Kafa Federal PolytechnicGwamnatin Jihar Kano ta mika makarantar Schoo...
23/08/2026

Gwamnatin Kano Ta Mika Makarantar Rano Ga Kwamitin Kafa Federal Polytechnic

Gwamnatin Jihar Kano ta mika makarantar School of Rural Technology and Entrepreneurship Development da ke Rano ga kwamitin da ke kula da shirin kafa Federal Polytechnic a Rano.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan yayin bikin mika makarantar, inda ya gana da mambobin kwamitin tare da duba wuraren da aka tanada domin gina Polytechnic ɗin.

Gwamnan ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta samar da dukkan goyon bayan da ake bukata domin ganin an kafa makarantar cikin nasara.

Ya kuma ce za a inganta kayan aiki da yanayin koyo a sabon wurin makarantar da ke karamar hukumar Sumaila.

Mambobin kwamitin sun yabawa gwamnatin jihar tare da nuna cewa makarantar za ta kara damar samun ilimin fasaha da sana’o’i ga matasa a Kano da sauran sassan Najeriya.

Malaman Addinin Musulunci 500 Sun Amince da Tinubu Ya Sake Tsayawa Takara a 2027Mai ba Shugaban Ƙasa Bola Tinubu shawara...
23/08/2026

Malaman Addinin Musulunci 500 Sun Amince da Tinubu Ya Sake Tsayawa Takara a 2027

Mai ba Shugaban Ƙasa Bola Tinubu shawara kan harkokin siyasa da sauran al’amura, Ibrahim Masari, ya ce kusan malaman addinin Musulunci da shugabannin addini 500 sun amince da Shugaba Tinubu ya sake neman wa’adin mulki a zaɓen 2027.

Masari ya bayyana hakan ne bayan halartar taron Northern Muslim Intellectual Forum da aka gudanar a Dutse, Jihar Jigawa.

Taron ya haɗa malamai, masana da shugabannin addini daga jihohin Arewa 19 da Babban Birnin Tarayya Abuja,acewar sanarwar, mahalarta taron sun tattauna matsalolin tsaro, tattalin arziki da ci gaban yankin Arewa.

Daga cikin waɗanda s**a halarci taron akwai gwamnonin Jigawa, Kano, Yobe, Sokoto da Kaduna, da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin.

Sanarwar ta ce mahalarta, waɗanda s**a kai kusan 500, sun amince baki ɗaya da Tinubu ya sake tsayawa takara a 2027, tare da kira ga ’yan Najeriya, musamman ’yan Arewa, da su mara masa baya da sauran ‘yan takarar APC.

Address

NO15c B U K Road KANO
Kano
700001

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when AMC AREWA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share