17/06/2025
Shugabannin G7 Sun Bayyana Goyon Bayan Su Ga Isra’ila, Suna Neman Tsagaita Wuta Da Iran
Shugabannin ƙasashen G7 sun fitar da wata sanarwar hadin gwiwa inda s**a nuna cikakken goyon bayansu ga Isra’ila a yayin da rikici da Iran ke kara tsananta.
A cikin sanarwar, sun jaddada cewa Isra’ila na da ‘yancin kare kanta daga kowanne hari da ke barazana ga tsaron ƙasarta.
Haka kuma, shugabannin sun yi kira da a kare rayukan fararen hula, tare da bukatar a dakile rikicin gaba ɗaya a Gabas ta Tsakiya — ciki har da tsagaita wuta a Gaza domin hana rikicin yaduwa.
Sanarwar na zuwa ne a daidai lokacin da Isra’ila da Iran ke musayar hare-haren makamai masu ƙarfi, lamarin da ke haifar da fargabar barkewar sabon yaƙi a yankin.
Rahotanni sun nuna cewa, Shugaban Amurka Donald Trump, wanda ya halarci taron G7 a Kanada, ya yanke shawarar barin taron da wuri saboda yadda al’amura ke dagulewa a Gabas ta Tsakiya.
MKK Hameex TV