Ilimi da Rayuwa

Ilimi da Rayuwa A platform dedicated to sharing knowledge, personal development, education, entrepreneurship, health

Ƙarin Kuɗin NECO Ya Jefa Makomar Ilimi Cikin BarazanaIlimi da Rayuwa Editor Khadija sunusi Gwadabe Ƙudirin ƙara kuɗin ri...
14/07/2026

Ƙarin Kuɗin NECO Ya Jefa Makomar Ilimi Cikin Barazana
Ilimi da Rayuwa
Editor Khadija sunusi Gwadabe

Ƙudirin ƙara kuɗin rijistar jarabawar NECO Senior Secondary Certificate Examination (SSCE) zuwa Naira 50,000 daga shekarar 2027 ya haifar da cece-kuce a Najeriya, inda masu ruwa da tsaki ke nuna damuwa kan tasirin da hakan zai iya yi ga makomar ilimi. International Human Rights Commission – Relief Fund Trust (IHRC-RFT), Reshen Najeriya, ta bayyana cewa wannan ƙarin na iya hana dubban ɗalibai, musamman 'ya'yan iyalai masu ƙaramin ƙarfi, damar rubuta jarabawar kammala sakandare, lamarin da zai ƙara yawan yaran da za su daina karatu.

Kungiyar ta jaddada cewa ilimi haƙƙi ne na kowane ɗan Adam, kuma gwamnati na da alhakin tabbatar da cewa kowane yaro ya samu damar yin karatu ba tare da cikas ba. Ta kuma yi gargadin cewa ƙarin kuɗin jarabawa a wannan lokaci na tsadar rayuwa na iya ƙara matsalolin rashin ilimi, talauci da rashin tsaro, domin masana sun daɗe suna bayyana cewa ilimi na daga cikin manyan hanyoyin gina al'umma mai zaman lafiya.

Saboda haka, IHRC-RFT ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da Ma'aikatar Ilimi da su sake nazarin wannan shiri tare da janye shi, tare da mayar da hankali kan manufofin da za su faɗaɗa damar samun ilimi ga kowa. A cewar kungiyar, saka hannun jari a ilimi ba kawai zai amfani ɗalibai ba ne, har ma zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arziki, rage aikata laifuffuka da gina makoma mai kyau ga Najeriya.

MAGANCE MATSALAR ALMAJIRCI: NCAOOSCE TA BAYYANA SABBIN MATAKAN INGANTA ILIMIN YARA MARASA ZUWA MAKARANTA A NAJERIYADaga ...
22/06/2026

MAGANCE MATSALAR ALMAJIRCI: NCAOOSCE TA BAYYANA SABBIN MATAKAN INGANTA ILIMIN YARA MARASA ZUWA MAKARANTA A NAJERIYA

Daga Shafin Ilimi da Rayuwa
Editor Khadija sunusi Gwadabe

Babban Sakataren Hukumar Kula da Ilimin Almajirai da Yara Marasa Zuwa Makaranta ta Ƙasa (NCAOOSCE), Dakta Muhammad Sani Idris, ya bayyana irin ƙoƙarin da hukumar ke yi wajen magance matsalar ilimin Almajirci da kuma rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a faɗin Najeriya. Ya ce hukumar na aiwatar da tsare-tsare da shirye-shirye da ke da nufin tabbatar da cewa kowane yaro ya samu damar samun ingantaccen ilimi ba tare da wata tangarda ba.

A cewarsa, ɗaya daga cikin manyan manufofin hukumar ita ce haɗa ilimin addini da na zamani domin samar da cikakken tsarin koyarwa da zai amfanar da yara. Ya bayyana cewa tsarin Almajirci ya daɗe yana taka muhimmiyar rawa wajen koyar da ilimin addinin Musulunci, amma akwai buƙatar sabunta shi domin ya dace da sauye-sauyen zamani da kuma buƙatun ci gaban ƙasa.

Dakta Muhammad Sani Idris ya ƙara da cewa hukumar na aiki tare da gwamnatocin jihohi, hukumomin ilimi, ƙungiyoyi masu zaman kansu da sauran masu ruwa da tsaki wajen samar da hanyoyin da za su taimaka wa yara marasa zuwa makaranta su koma makarantu. Haka kuma, ana ƙoƙarin samar da horo da ƙwarewar sana’o’i ga yara domin su samu damar dogaro da kansu a nan gaba.

Masana ilimi na ganin cewa nasarar wannan yunƙuri za ta taimaka matuƙa wajen rage matsalolin jahilci, talauci da zaman banza a cikin al’umma.
Ana sa ran cikakkiyar tattaunawar da Dakta Muhammad Sani Idris ya yi za ta yi ƙarin bayani kan matakan da ake ɗauka da kuma makomar ilimin Almajirci a Najeriya, wanda ke da muhimmanci wajen gina al’umma mai ilimi da ci gaba.

Address

Sagagi
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Ilimi da Rayuwa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share