13/06/2025
Dan sanyin safiya Komi ta isa asibitin da take aiki ta mika takardar barin aiki cikin farin ciki da annushuwa, ta sanar da abokanta cewa lokaci yayi da yak**ata ta bar nan ta tafi sabuwar rayuwa tare da mijinta da kuma ‘yayanta uku.
Abu na gaba da tayi shine halartar makarantar ‘yayanta, inda tasa s**ayi ban kwana da malamai da kuma abokan karatunsu. Malamai da dalibai sun yi bacin cikin rabuwar da ‘yayanta wadanda akayi ta daukar hotuna da taya su murnar za su bar kasar su India za su koma England.
Kafin wannan lokaci, Mijin Komi, shine Dr. Pratik Joshi, wanda ya samu aiki shekaru shida a birnin London, tsawon wannan shekarun ya na zaune a London shi kadai ba tare da iyalansa ba. Yayi ta fadi tashi domin a ba shi damar dawo da iyalansa London. A karshe ya samu nasarar amincewa daga hukumomin ksar Birtaniya, inda ya haka kuaddensa ya siyawa iyalan tikitin tafiya Turai.
Da sanyin safiyar ranar alhamis 12 ga wantan June yarasa uku da matarsa da shi kansa s**a hau jirgin Air India mai lamba 171, suna murmushi. Daga kan kujerar da yake zaune a cikin jirgi kusa da window, Dr. Pratik Joshi ya daga wayarsa ya dauki hoton Selfie suna murmushi shi da iyalansa. Daga nan sai ya tura hoton zuwa ga group din dangin da s**a bari a India, a karkashin hoton ya rubuta “Mun nufi masaukinmu na gaba”
A she wannan shine murmushin karshe, dakiku talatin da bakwai da faruwar haka, jirgin Air India ya tashi. Minti biyu da tashinsa ya rikito kasa ya k**a da wuta, Komi da ‘yayanta Uku da mijinta Dr. Pratik Joshi sunyi bankwana da duniya.
Akwai darasi a rayuwar nan, mu shiryawa mutuwa a kowanne irin lokaci za ta izuwa. Ko a halin farin ciki ko a na bakin ciki. Allah yasa mu cika da imani.
Alkalamin - Nasir Nid