
09/06/2025
Adam A. Zango ya gamu da ibtali'in haaɗarin mota
Fitaccen Jarumin Masana'antar shirya Fina-finai ta Kannywood Adam A. Zango, ya gamu da haɗarin mota akan hanyarsu daga Kaduna Zuwa Kano, wanda hakan ya tada hankalin dayawa daga cikin Masoyansa, dakuma mabiyan Jarumin.
Bayyanar saƙon nuna godiya daga Adam A. Zango bisa addu'o'i da ake masa da kuma fatan alkairi, kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Facebook, hakan ya sanyaya zuciyar da yawa daga cikin masoya Jarumin.
Daga Abubakar Shehu Dokoki