29/04/2026
Darasi na uku acikin littafin Kitabut tauhid 03:
بسم الله الرحمن الرحيم
بَابُ مَنْ حَقَّقَ التَّوْحِيدَ دَخَلَ الْجَنَّةَ بِغَيْرِ حِسَابٍ
Babin dake magana kan wanda ya tabbatar da Tauhidi (ya tsarkake shi) zai shiga Aljanna ba tare da hisabi ba.
وَقَوْلُ اللهِ تَعَالَى: {إِنَّ إِبْرَاهِيمَ كَانَ أُمَّةً قَانِتًا لِلَّهِ حَنِيفًا وَلَمْ يَكُ مِنَ الْمُشْرِكِينَ}
Kuma fadar Allah Madaukakin Sarki: "Lallai Annabi Ibrahim ya kasance jagora (abin koyi), mai kankan da kai ga Allah, mai karkata zuwa ga gaskiya, kuma bai kasance daga cikin mushirikai ba."
وَقَالَ: {وَالَّذِينَ هُمْ بِرَبِّهِمْ لَا يُشْرِكُونَ}
Kuma (Allah) ya ce: "Kuma wadanda su ne, ba sa hada Ubangijinsu da kowa (ba sa yin shirka)."
عَنْ حُصَيْنِ بْنِ عَبْدِ الرَّحْمَنِ قَالَ: كُنْتُ عِنْدَ سَعِيدِ بْنِ جُبَيْرٍ فَقَالَ: أَيُّكُمْ رَأَى الْكَوْكَبَ الَّذِي انْقَضَّ الْبَارِحَةَ؟
Daga Husain dan Abdurrahman ya ce: Na kasance a wurin Sa’id dan Jubair, sai ya ce: "Wane ne a cikinku ya ga tauraron da ya fado jiya da daddare?"
فَقُلْتُ: أَنَا، ثُمَّ قُلْتُ: أَمَا إِنِّي لَمْ أَكُنْ فِي صَلَاةٍ، وَلَكِنِّي لُدِغْتُ.
Sai na ce: "Ni ne," sannan na ce: "Amma dai (ina so ku sani) ba wai ina sallah ba ne (shiyasa na gani), sai dai wani abu ne ya harbe ni."
قَالَ: فَمَا صَنَعْتَ؟ قُلْتُ: ارْتَقَيْتُ. قَالَ: فَمَا حَمَلَكَ عَلَى ذَلِكَ؟
Ya ce: "To me ka yi?" Na ce: "Na nemi a yi mini rukya." Ya ce: "Me ya sa ka yi hakan (wane dalili kake da shi)?"
قُلْتُ: حَدِيثٌ حَدَّثَنَاهُ الشَّعْبِيُّ. قَالَ: وَمَا حَدَّثَكُمْ؟
Na ce: Wani hadisi ne da Ash-sha’abi ya ba mu labari. Ya ce: "Me ya ba ku labari?"
قُلْتُ: حَدَّثَنَا عَنْ بُرَيْدَةَ بْنِ الْحُصَيْبِ أَنَّهُ قَالَ: (لَا رُقْيَةَ إِلَّا مِنْ عَيْنٍ أَوْ حُمَةٍ).
Na ce: Ya ba mu labari daga Buraida dan Al-Husayb cewa ya ce: "Babu rukya (mafi amfani) sai don ta kambun ido da kambun baka (muguwar magana) ko kuma harbin wani abu mai dafi."
قَالَ: قَدْ أَحْسَنَ مَنْ انْتَهَى إِلَى مَا سَمِعَ، وَلَكِنْ حَدَّثَنَا ابْنُ عَبَّاسٍ عَنِ النَّبِيِّ ﷺ أَنَّهُ قَالَ:
Ya ce: "Lallai wanda ya tsaya ga abin da ya ji (na ilimi) ya kyauta. Sai dai Ibn Abbas ya ba mu labari daga Annabi SAW cewa ya ce:"
عُرِضَتْ عَلَيَّ الْأُمَمُ، فَرَأَيْتُ النَّبِيَّ وَمَعَهُ الرُّهَيْطُ، وَالنَّبِيَّ وَمَعَهُ الرَّجُلُ وَالرَّجُلَانِ، وَالنَّبِيَّ وَلَيْسَ مَعَهُ أَحَدٌ.
"An nuna mini al'ummomi; sai na ga wani Annabi yana tare da wasu mutane kalilan (ba su kai goma ba), da wani Annabi tare da mutum daya ko biyu, da ma wani Annabin da babu kowa tare da shi."
إِذْ رُفِعَ لِي سَوَادٌ عَظِيمٌ فَظَنَنْتُ أَنَّهُمْ أُمَّتِي، فَقِيلَ لِي: هَذَا مُوسَى وَقَوْمُهُ.
"Kwatsam sai aka ɗaga mini wani babban taron (mutane da yawa), sai na zata al'ummata ce, sai aka ce mini: 'Wannan Musa ne da mutanensa'."
فَنَظَرْتُ فَإِذَا سَوَادٌ عَظِيمٌ، فَقِيلَ لِي: هَذِهِ أُمَّتُكَ، وَمَعَهُمْ سَبْعُونَ أَلْفًا يَدْخُلُونَ الْجَنَّةَ بِغَيْرِ حِسَابٍ وَلَا عَذَابٍ.
"Sai na sake dubawa sai na ga wani babban taro mai yawan gaske, sai aka ce mini: 'Wannan ita ce al'ummarka, kuma tare da su akwai mutum dubu saba'in (70,000) da za su shiga Aljanna ba tare da hisabi ba, kuma ba tare da azaba ba'."
ثُمَّ نَهَضَ فَدَخَلَ مَنْزِلَهُ، فَخَاضَ النَّاسُ فِي أُولَئِكَ، فَقَالَ بَعْضُهُمْ: فَلَعَلَّهُمْ الَّذِينَ صَحِبُوا رَسُولَ اللهِ ﷺ.
Sannan (Annabi) ya tashi ya shiga gidansa. Sai mutane s**a shiga tattaunawa a kan wadannan mutanen (dubu saba'in ɗin). Wasu s**a ce: "Wataƙila su ne waɗanda s**a yi abota da Manzon Allah SAW."
وَقَالَ بَعْضُهُمْ: فَلَعَلَّهُمْ الَّذِينَ وُلِدُوا فِي الْإِسْلَامِ فَلَمْ يُشْرِكُوا بِاللهِ شَيْئًا.
Wasu kuma s**a ce: "Wataƙila su ne waɗanda aka haifa a cikin Musulunci kuma ba su taɓa yin shirka da Allah ba."
فَخَرَجَ عَلَيْهِمْ رَسُولُ اللهِ ﷺ فَأَخْبَرُوهُ فَقَالَ: هُمُ الَّذِينَ لَا يَسْتَرْقُونَ، وَلَا يَكْتَوُونَ، وَلَا يَتَطَيَّرُونَ، وَعَلَى رَبِّهِمْ يَتَوَكَّلُونَ.
Sai Manzon Allah SAW ya fito gare su, s**a gaya masa (abun da suke tattaunawa), sai ya ce: "Su ne waɗanda:
Ba sa neman a yi musu rukya (domin tsantsar tawakkali).
Ba sa yin Tsakiya da wuta (ƙuna).
Ba sa yin camfi.
Kuma ga Ubangijinsu ne kaɗai suke dogara.
فَقَامَ عُكَّاشَةُ بْنُ مِحْصَنٍ فَقَالَ: ادْعُ اللهَ أَنْ يَجْعَلَنِي مِنْهُمْ، فَقَالَ: أَنْتَ مِنْهُمْ.
Sai Ukasha dan Mihsan ya tashi ya ce: "Ka roƙar mini Allah ya sanya ni daga cikinsu." Sai Annabi ya ce: "Kana daga cikinsu."
ثُمَّ قَامَ رَجُلٌ آخَرُ فَقَالَ: ادْعُ اللهَ أَنْ يَجْعَلَنِي مِنْهُمْ، فَقَالَ: سَبَقَكَ بِهَا عُكَّاشَةُ.
Sannan wani mutumin ya tashi ya ce: "Ka roƙar mini Allah ya sanya ni daga cikinsu." Sai ya ce: "Ukasha ya riga ka."
فِيْهِ الْمَسَائِل
(Akwai Mas'alolin da ke cikin babin):
الأُولَى: مَعْرِفَةُ مَرَاتِبِ النَّاسِ فِي التَّوْحِيدِ.
Na ɗaya:Sanin matsayin mutane mabambanta a kan Tauhidi.
الثَّانِيَةُ: مَا مَعْنَى تَحْقِيقِهِ.
Na biyu:Menene ma’anar "Tahqiq" (tabbatar da/tsarkake) Tauhidi.
الثَّالِثَةُ: ثَنَاؤُهُ سُبْحَانَهُ عَلَى إِبْرَاهِيمَ بِكَوْنِهِ لَمْ يَكُ مِنَ الْمُشْرِكِينَ.
Na uku:Yabon da Allah ya yi wa Annabi Ibrahim na cewa bai kasance daga cikin mushirikai ba.
الرَّابِعَةُ: ثَنَاؤُهُ عَلَى سَادَاتِ الْأَوْلِيَاءِ بِسَلَامَتِهِمْ مِنَ الشِّرْكِ.
Na huɗu:Yabon manyan bayin Allah kan kubutarsu daga shirka.
الْخَامِسَةُ: كَوْنُ تَرْكِ الرُّقْيَةِ وَالْكَيِّ مِنْ تَحْقِيقِ التَّوْحِيدِ.
Na biyar:Barin neman rukya da Yin tsakiya da wuta na daga cikar Tauhidi.
السَّادِسَةُ: كَوْنُ الْجَامِعِ لِتِلْكَ الْخِصَالِ هُوَ التَّوَكُّلُ.
Na shida:Kasancewar abin da ya tara waɗannan dabi’un shi ne dogara ga Allah Tawakkali.
السَّابِعَةُ: عُمْقُ عِلْمِ الصَّحَابَةِ بِمَعْرِفَتِهِمْ أَنَّهُمْ لَمْ يَنَالُوا ذَلِكَ إِلَّا بِعَمَلٍ.
Na bakwai:Zurfin ilimin Sahabbai da s**a gane cewa ba a samun wannan matsayi sai da aiki.
الثَّامِنَةُ: حِرْصُهُمْ عَلَى الْخَيْرِ.
Na takwas:Kwadayin Sahabbai wajen neman alheri.
التَّاسِعَةُ: فَضِيلَةُ هَذِهِ الْأُمَّةِ بِالْكَمِّيَّةِ وَالْكَيْفِيَّةِ.
Na Tara:Falalar wannan al'umma ta fuskar yawa da kuma inganci.
الْعَاشِرَةُ: فَضِيلَةُ أَصْحَابِ مُوسَى.
Na Goma:Falalar mabiyan Annabi Musa.
الْحَادِيَةَ عَشْرَةَ: عَرْضُ الْأُمَمِ عَلَيْهِ ﷺ.
Na sha daya:Nuna wa Annabi SAW dukkan al'ummomi.
الثَّانِيَةَ عَشْرَةَ: أَنَّ كُلَّ أُمَّةٍ تُحْشَرُ وَحْدَهَا مَعَ نَبِيِّهَا.
Na sha biyu:Kowace al’umma za a tashe ta ne tare da Annabinta.
الثَّالِثَةَ عَشْرَةَ: قِلَّةُ مَنِ اسْتَجَابَ لِلْأَنْبِيَاءِ.
Na sha uku: Ƙarancin mutanen da s**a amsa kiran Annabawa.
الرَّابِعَةَ عَشْرَةَ: أَنَّ مَنْ لَمْ يُجِبْهُ أَحَدٌ يَأْتِي وَحْدَهُ.
Na sha huɗu:Annabin da kowa bai bi shi ba, zai zo shi kaɗai ranar kiyama.
الْخَامِسَةَ عَشْرَةَ: ثَمْرَةُ هَذَا الْعِلْمِ وَهُوَ عَدَمُ الِاغْتِرَارِ بِالْكَثْرَةِ وَعَدَمُ الزُّهْدِ فِي الْقِلَّةِ.
Na sha biyar:Amfanin wannan ilimin shi ne: rashin ruɗuwa da yawa, da kuma rashin raina abu saboda ƙarancinsa.
السَّادِسَةَ عَشْرَةَ: الرُّخْصَةُ فِي الرُّقْيَةِ فِي الْعَيْنِ وَالْحُمَةِ.
Na sha shida: Sauƙi/Halaccin yin rukya saboda harbi ko mugun gani.
السَّابِعَةَ عَشْرَةَ: عُمْقُ عِلْمِ السَّلَفِ لِقَوْلِهِ (قَدْ أَحْسَنَ مَنِ انْتَهَى إِلَى مَا سَمِعَ).
Na sha bakwai:Zurfin ilimin magabata wajen faɗin cewa "wanda ya tsaya ga abin da ya ji ya kyauta".
الثَّامِنَةَ عَشْرَةَ: بُعْدُ السَّلَفِ عَنْ مَدْحِ الْإِنْسَانِ بِمَا لَيْسَ فِيهِ.
Na sha takwas:Nisantar magabata daga yabon mutum da abin da ba shi da shi.
التَّاسِعَةَ عَشْرَةَ: قَوْلُهُ (أَنْتَ مِنْهُمْ) عَلَمٌ مِنْ أَعْلَامِ النُّبُوَّةِ.
Na sha tara:Fadin Annabi "Kana cikinsu" wata babbar aya ce ta annabta (domin Ukasha ya mutu a kan haka).
الْعِشْرُونَ: فَضِيلَةُ عُكَّاشَةَ.
Na Ashirin:Falalar Ukasha (Allah ya yarda da shi).
الْحَادِيَةُ وَالْعِشْرُونَ: اسْتِعْمَالُ الْمَعَارِيضِ.
Na ashirin da daya:Yin amfani da hikima wajen magana don kauce wa abin da ba a so.
الثَّانِيَةُ وَالْعِشْرُونَ: حُسْنُ خُلُقِهِ ﷺ.
Na ashirin da biyu:Kyawun ɗabi'un Manzon Allah SAW.
والله أعلم.
Allah ne mafi sani.
Follow me for more share like comment 🙏✅