19/04/2025
🚨| Yadda ake binciken neman aure.
ℹ Wata yar uwa tace aurena uku, duka ba sa'a, kuma ana bincike, amma sai daga baya aga wasu halaye na boye. Don Allah ya ake binciken neman aure?
Da sunan Allah - Da farko dai yana da kyau mu sani cewa akwai nau'ikan halayen da duk kyan bincike ko zurfinsa ba za'a iya gane su ba. Sai a hankali. Amma duk da haka, zan kokarta wajen bada haske akan abin. Da yawan mu over-excitement na aure shine yake rufe mana ido mu kasa yin abinda ya dace. Misali, muna saurin judging mutane da ido, saboda munga wata suffa da batayi k**a ta abin zargi ba. Sannan mutum mai abin duniya ba'a cika son ma ayi masa bincike ba, sai kaji ana cewa "Kar a matsa bincike, kowa akaiwa bincike ba zai sha ba". Shikenan sai a bar magana. Wasu iyayen ma musamman iyaye mata idan aka cika matsawa manemi sai kaji uwa tana cewa "Bakin ciki akewa Talatu saboda anga ta samu mai-arzuki". Shikenan kowa sai ya janye jiki. Sannan na karshe, ba mutanen kirki da amana ake sakawa suyi binciken ba yawanci, ko kuma su wadanda ake tambaya basa fadin gaskiya. Kafin mu shiga cikin bayanan, yana da kyau mu sani cewa, binciken aure abu ne babba, kuma Manzon Allah SAW yace, Amanace wadda duk wanda aka tambaya akan wani wajibi ne ya fadi gaskiya, kuma boye gaskiya a wannan sigar haramun ne a musulunci.
Ya ake Bincike? Zan raba bincike gidan uku.
1. Binciken kafin fara mu'amala (Namiji da Mace)
Yana da matukar mahimmanci kafin a nemi auren mutum, a fara preliminary investigation akan sa/ta. Irin wannan binciken za'a kasa shi gida uku (3)
1.1. Mahaifa/Tushe
Mahaifar mutum shine inda aka haife shi, kuma ba lalle ne ace mutum yana zaune a mahaifar sa ba. Zai iya canja waje. Binciken mahaifa ya kunshi bincike akan iyayen sa/ta, yarintarsa, tarbiyyarsa, tarbiyyar kannen sa, yadda yayi mu'amala da mutane, abokansa da sauran su. Kuma ana tambayar dattijai, matasa da kuma sa'anninsa. Sannan ana priotizing tambayar mata saboda zantuka sun fi circulating tsakanin su. Kuma yana da kyau a bayyana wa wanda ake tambaya cewa makasudun tambayar akan neman aure ne.
1.2. Unguwa
Unguwar mutum itace mazauninsa. Mazauni shima yana canjawa, duk inda mutum ya taba zama wajibi ne a je don aji me yasa yabar inda yake/take da. Sannan aji me mutum yake. Sannan yana da kyau a wannan gabar a zirfafa tambaya a masallatan inda yake zaune idan namiji ne. Idan babu wani record nasa a masallaci to ba mutumin kirki bane. Shima kuma za'a iya shigar da dattijai, matasa da yara. Sannan yana da kyau a zirfafa bincike tsakanin abokansa na hira, da abokan yawo.
1.3. Wajen aiki/Sana'a
Wajen sana'a ko aiki wajene da ake samun dunbun bayanai. To amma sai an kula, domin gurine kuma na makiya. Mutum zai iya bada bayanin karya don ya lalata mutum. Don haka sai an kula. Idan yana da abokai, a nemi wasun su, a kuma roki su bayyana gaskiya, ayi musu togaciya da Allah don su bayyana gaskiya.
1.4. Makaranta
Akwai dunbun bayanai a makaranta. Za'a iya zuwa wajen principal, ko Class Rep, Ko lecturer, ko abokan karatun don jin yadda mutum ya gudanar da rayuwarsa a cikin makaranta. Idan akace ba sosai yake zuwa ba, ko ba sosai take zuwa ba, sai a bincika aji meye dalili.
1.5. Mahaifan mutum
Yawanci masu bincike sukan manta da cewa iyayen mai nema suma they are central to binciken mai neman. Saboda ana iya samun fitinannun iyaye ko iyaye masu mummunan tarihi ko wata mummunar al'adah ko dabi'a. Ko kuma ace ma basa zaman lafiya da mutane, ko kuma a gida akwai matsalar rabuwar kai da sauran su. So ba'a overlooking. Kamar yadda mai neman yake shan bincike haka suma iyayensa. Saboda ba miji ko mata kadai ake aura ba lokacin aure, suma iyaye k**ar ka aure sune domin zaman yana shafar kowane bangare.
Idan komai yayi yadda ake so, sai a bashi izini ya ci gaba da nema.
2. Binciken Bayan an fara Nema (Namiji da Mace)
A wannan gabar za'a ci gaba ne da bincike mutum har zuwa ranar da za'ayi aure. Saboda mutum yana canjawa a dan lokaci kankani. So time to time sai a rika komawa unguwa da wajen san'ar mutum ana jin ta bakin mutane. Sannan za'a iya rokar wani ya saka ido don ya rika bada bayanai akan mutum har zuwa lokacin da za'a gamsu. Shima wannan binciken zan raba shi gida hudu (4):
2.1. Interview tsakanin mai nema da iyaye
Yana da kyau kowane uba, ko uwa, ko yaya, ko waliy ya samu lokaci na musamman ya gana da mai neman. Kuma ba hira kawai ake magana ba anan. Zama za'ayi aci abinci, ayi hira, lokacin sallah yayi, a tashi ayi sallah. Wani tun wajen cin abincin sa zaka gane dabi'unsa. Hakanan yanayin maganarsa da ladabin sa suma Ababan dubawa ne. Sannan idan lokacin sallah yayi za'a lura da canji a yanayinsa. Sannan yana da kyau, ba laifi bane shi mai gayyatar ya saki jiki yayi tambayoyi na hankali. Duk abinda ya dace kuma ya k**ata a sani sai a tambaye shi. Wasu ma sai a rubuta a gabansa yana kallo. Hakan zai sa shi yaji cewa nan ba wajen da zai wasa bane. Sannan su manya suna da kwarjinin da karya bata yuwuwa a gaban su. Kuma ko anyi musu karya sai an gane. Sannan anan ne idan akwai wani special request k**ar su karatu, aiki, ko rashin son zuwa nesa, sai a gabatar da su. Kuma yana da kyau ayi a rubuce idan ana fargaba. A wannan gabar ne idan yace yana da Plaza ko Gida a guri kaza, sai aje wajen a gani da ido. Saboda yanzu makaryata sun yawaita.
2.2. Interview tsakanin masu neman
Wannan kuma tattaunawa ce ta yau da gobe. Yana da kyau kowa ya tanadi tambayoyin sa a paper. A duk lokacin da aka hadu don hira sai a rika tambayar juna. Tambayoyin da ake so ayi sun hada da tambayar karatun addini da na Boko, Sana'a, fasahar mutum wato skills, abokai, fahimtar mutum, aqeedarsa ta addini, ra'ayoyinsa akan abubuwa daban daban na rayuwa, fahimtar sa akan zamantakewar aure, fahimtar sa akan mata, sanin sa akan hakkokin aure, da sauran su. Kar ku rika zama kuna hirar banza, ku yawaita tambayoyi a tsakanin ku. Wallahi Matata shaida ce, list nake yi idan muna hira. Kai, har cewa nayi a karanta min qurni naji. Komai ka tambaya. Haka nan kai tsaye ayi tambaya irin su don Allah kin taba sanin Da namiji, ko ka taba sanin Ya mace. Duk wannan tambayoyi ne masu mahimmacin. Sannan idan kai mai son wasu abubuwa ne k**ar halittar mace, zaka iya tambayar ta. Misali, don Allah meye size din Bra din ki da waist din ki. Ko kuma don Allah zaki iya tashi tsaye na ganki ba a cikin hijab ba. Wannan duk ya halarta a shariah. Ke ma kuma zaki iya masa tambayar da k**e ganin ta dace kiyi kuma ki sani. Saboda aure yana lalacewa idan aka samu akasin abinda ake nema. Gwara ayi gaskiya da gaskiya. A wannan gabar ana fahimtar abubuwa da yawa. Sai a kasa kunne don lura da inconsistency na zance, anan ake gane makaryaci. Kuma wasu bayanan ma sai mutum yana yi yana rubutawa don kar a manta.
2.3. Interview da yan gida
Lokaci zuwa lokaci ka sa a kira maka wasu daga cikin yan gidan don ku gaisa. Misali kanne, ko jikoki. Anan ne zaka lura da original tarbiyyar gida. Idan ma gidan kirkine zaka gani, idan kuma akwai matsala ma zaka gani. Sannan kema zaki iya cewa watarana ya kawo miki yan gidan su ku gaisa. Idan zuwa bazai yuwu ba sai a rika yi ta waya lokaci zuwa lokaci.
2.4. Interview da aboki/kawa
Sannan sometimes ki sa yazo miki da friends din sa kiyi musu abinci suci, sannan ki lura da dabi'unsu da yanayin maganar su. Kai ma haka, ka mata zancen friends din ta mata kuma kace a kawo su ku gaisa. Sanin kalar kawayenta zai baka hint sosai akan ita wacece.
Wannan process din baya tsayawa har sai anyi aure. Saboda aure da yawa an fasa shi saura sati ko ana i gobe. Saboda wani abu da aka gano. Shi yasa ake so a matsa da binciken, kuma ba'a so a tsagaita.
3.0 Waye yake bincike?
Bincike abu ne na sirri, kuma abu ne mai girma, kuma abu mai mahimmanci. Don haka ana bukatar mutum nagari, mai addini, mai waye wa, wanda yasan mutane, wanda yake hulda da jama'a, wanda kuma bazai gajiya ba. Idan aka tura mutum mara wadannan abubuwan, zai iya ganin matsala ma amma baisan matsala bace saboda shima baida isasshiyar tarbiyyar da zai gane matsala idan ya ganta. Anan mahaifi zai iya zuwa da kansa ko ya wakilta wani. Za'a kuma iya dakko mutum na musamman don a biya shi yayi wannan aikin. Misali, zaka iya daukar investigative Lawyer ko Journalist ka biya shi ya maka bincike. Suna da fasaha sosai akan binciken kwakwaf.
To bayan kayi duka wannan, to har a gurin Allah ka fita. Wallahi ko matsala aka samu sai kaga Allah ya shiga cikin ta kuma sai kun samu mafita saboda kunyi abinda Allah yace ayi tun kafin ma azo zaman. Rashin daukar mataki na bincike shi ke sa ayi aure kuma azo ayi ta fuskantar matsaloli, sai daga baya kuma a rika dana-ansani. Zan tsaya anan, abinda na fada na daidai Allah ya bani lada, inda kuma nayi kuskure Allah ya yafe mun. Idan akwai abinda na manta za'a iya karin bayani a kasa. Allah ya bamu sa'a.