Ajingi Radio Online

Ajingi Radio Online Muryar gaskiya da sahihan labarai. Muna kawo maku labarai, siyasa, wasanni, nishadi da al’amuran yau da kullum cikin sauri da inganci.

Ku biyo mu domin samun sabbin bayanai a kowane lokaci.

17/09/2026

Shugaban Afirka ta Kudu ya janye daga ayyukan hukuma saboda rashin lafiya

Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya dakatar da halartar wasu ayyukan jama’a bayan dawowarsa daga taron ƙasashen BRICS da aka gudanar a Indiya.

Fadar shugaban ƙasar ta ce likitocinsa sun ba shi shawarar ya huta domin samun sauƙi.
Ramaphosa, mai shekaru 73, ya dawo daga taron BRICS da aka gudanar a Indiya ranar Litinin.

A halin yanzu, Mataimakin Shugaban ƙasar, Paul Mashatile, shi ma yana murmurewa bayan ya gudanar da wata ƙaramar tiyata.

Hakan ya sa shugabannin ƙasar biyu s**a kasance ba sa gudanar da ayyukan jama'a a wannan lokaci.

Taron BRICS ya ƙunshi ƙasashe irin su Brazil, Rasha, Indiya, China da Afirka ta Kudu, kuma taron na baya-bayan nan ya mayar da hankali kan bunƙasar tattalin arzikin duniya da wasu batutuwan da s**a shafi Gabas ta Tsak

17/09/2026

NLC ta buƙaci Tinubu ya ɗauki mataki kan wahalar da ƴan Najeriya ke ciki

Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya ɗauki matakan gaggawa domin rage wa ƴan Najeriya radadin tashin farashin man fetur.

NLC ta ce ba za a iya yin shiru ba yayin da tashin farashin man fetur ke ƙara jefa al’umma cikin wahala.

Shugaban NLC, Comrade Joe Ajaero, ya bayyana cewa farashin man fetur ya kai kusan ₦1,430 a kowace lita a wasu manyan biranen ƙasar inda ake samun man cikin sauƙi, yayin da farashin ya fi haka a wuraren da man ba ya samuwa cikin sauƙi.

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, Ajaero ya ce tashin farashin man ya yi matuƙar illa ga albashin ma’aikata da kuma rayuwar ƴan Najeriya.

Ya kuma yi gargadin cewa ƙarin kuɗin sufuri da tashin farashin man fetur zai iya ƙara tsadar kayan masarufi da sauran hidimomi, lamarin da zai ƙara rage ƙarfin iyalan Najeriya na iya biyan buƙatunsu.

17/09/2026

INEC ta bayyana dalilin da ya sa Amupitan baya Abuja

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta bayyana cewa Shugabanta, Farfesa Joash Amupitan, SAN, yana wajen Abuja ne saboda wani aiki na hukuma.

INEC ta ce shugaban hukumar yana da damar ba wa wani Kwamishinan Ƙasa ikon gudanar da ayyukan shugaban a lokacin da ba ya nan.

Daraktar Ilmantar da Masu Zaɓe da Hulɗa da Jama’a ta INEC, Victoria Eta-Messi, ce ta bayyana hakan yayin da take amsa tambayoyi kan inda shugaban hukumar yake.

Bayani ya biyo bayan wata sanarwa daga ƙungiyar Obidient Movement, wadda ta nemi INEC ta yi bayani kan rashin Amupitan a Abuja, bayan da Kwamishinar Ƙasa, Farfesa Rhoda Gumus, ta bayyana a matsayin Mukaddashin Shugaban INEC yayin wata ganawa da tawagar Tarayyar Afirka (AU).

INEC ta tabbatar da cewa Amupitan yana wajen Abuja ne bisa wani aiki na hukuma.

16/09/2026

kuzo mu wasa ƙwaƙwalwa

Address

Ajingi Local Government
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Ajingi Radio Online posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share