
24/07/2025
'Dan kasuwar wanda ya kasance 'Dan Gwagwarmaya, mai rajin Kwankwasiyya ya bukaci shugaban Karamar hukumar Dawakin Tofa, Hon. Anas Mukhtar Bello Dan Maliki akan ya taimaka ya karasa musu asbitin sha ka tafi da ake yi musu a Gwanji.
Shamsu yace: "Gwanji nada tarin Jama'a, mafi yawansuma sun wahaltawa Jam'iyyar NNPP, wadanda suke bukatar Wannan Asibiti.
Ya Kara da cewa: "Kowa yasan yadda Ciyaman Dan Maliki yake yin ayyukan raya kasa da cigaban Alumma a Dawakin Tofa, wannan yasa muma muke fatan azo ayi mana wannan asibi na sha ka tafi domin bada agajin Gaggawa ga mutanen Garin.