Kano a Yau Kano Today

Kano a Yau Kano Today Domin samun Labarai da Dumi Dumi

16/05/2023

Bola Ahmed Tinubu and Rabiu Musa Kwankwaso, who flew the flag of New Nigeria People's Party (NNPP) in the February 25 presidential...

14/11/2022

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta umurci Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) da ta gurfanar da Abdulkareem Abdussalam Zaura (wanda aka fi sani da AA Zaura),…

25/08/2022
DA-DUMI-DUMINSA : akwai yiyuwar a sake yin Inconclusive a jihar Kano a Zabe 2013, Ganduje ya roki Shugaban ‘yan Sanda ya...
23/07/2022

DA-DUMI-DUMINSA : akwai yiyuwar a sake yin Inconclusive a jihar Kano a Zabe 2013, Ganduje ya roki Shugaban ‘yan Sanda ya tura CP kolo Kano amatsayin kwamishina domin magudin zaben 2023.

Kafin ya zama kwamishina CP Kolo shine ya Jagoranci rundunar STS wacce ta shahara wajen k**awa Kuma itace rundunar da Ake Zargin da kashe farar hula ciki harda wani matashi Dan jihar Kano.

CP kolo ya shahara wajen anfani da 'yan Sanda wajen shirya magudin zabe a duk lokacin zabe.

Rahotonni sun tabbatar da cewa Gwamna Ganduje ya bukaci a Kai Kolo Yusuf Jihar Kano amatsayin kwamishinan Yan Sanda na jihar wanda zai Jagoranci zaben 2023.

Daga Shafin Mikiya

Da Maigirma Wazirin Adamawa Atiku Abubakar Mai kishin Arewa ne, sai ya janyewa Maigirma Engr. Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso....
18/06/2022

Da Maigirma Wazirin Adamawa Atiku Abubakar Mai kishin Arewa ne, sai ya janyewa Maigirma Engr. Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso.

Domin shine Talakawa s**a aminta dashi, domin sun san in ya samu sun samu. Su Atiku kuwa kowa yasan zasu zuba Jari ne suci riba,dama a baya su s**a dinga sayarwa kansu da kansu Kadarorin gwamnati.

Ina Fatan Atiku zaiyi Kishin Arewa ya bari mu Gwafza da wancan Bayarben ɗan OPC mai tsananin Ƙaɓilanci.

Haba Malam ina Bahaushe ɗan Arewa ka kawomin wata Bola, mu ko a Kauye Gona muke Kaita.

Allah ya zaɓa mana mafi alkhairi

To indai ba Mantuwa ba waye zai sake Zaɓar APC, b***e ka jefa Kuriarka a Bola.Haka itama PDP duk shegiyar ɗarin ce.Kanas...
18/06/2022

To indai ba Mantuwa ba waye zai sake Zaɓar APC, b***e ka jefa Kuriarka a Bola.

Haka itama PDP duk shegiyar ɗarin ce.

Kanason gaskiya nemi Jam'iyyar nan ta Kwankwaso mai Kayan Dadi NNPP.

Wallahi shine ya damu da mu Talakawa, muma kuma mun damu dashi.

Allah kayi mana Jagora

13/06/2022

Su APC ma da suna da kunya ko tsoron Allah, Bai Kamata s**e da Ƴan Nigeria wani abu ba, in bayan su fito su bamu Hakuri, kuma s**e sun Gaza.

Amma abin mamaki sai s**a ɗauko mana wani Ruɓaɓɓen Bayarabe mai tsananin nuna Ƙabilanci ga matasanmu na Arewa masu zuwa cirani Lagos.

Baza mu taba mantawa da irin kashe Hausawa da akayi a lokacin yana gwamnan Lagos. Baza mu manta da wulakanta ƴan Arewa da ake yi a karkashin mulkin yaransa Baba Jide San-Olu ba.

Akwai wata salon magana da ake cewa "NAKU NAMU NE, NAMU KUMA NAMU NE" Ma'ana in mune muke Mulki sai kaga sun Zaƙalƙale kuma sai sunfi'Yan Arewa amfana a mulkin. Misali na kusa Mulkin Buhari duk wani Burinsu wallahi saida aka biya musu shi.

Amma wallahi in sune akan mulki ba Lagos ba ko Abuja tamu da take a Arewa sai ta gagaremu, b***e kuma a biya mana wasu bukatun, ko kuma mu samu damar miƙe ƙafa a Jihoshinsu.

Mu dena yaudarar kanmu, in zamu farka mu Farka. Ajendar wadannan mutanen su ɗora daga inda Buhari ya tsaya bawa wasu ƴan uwanmu Mak**ai da Ƙwayoyi suci gaba da garkuwa damu da kashemu. Su kuwa yankin su na Kudu yana ɓunkasa. Suna gama gina Kudu zasu nemi ɓalle daga Nigeria. Mu kuma su bammu da Filanin Daji da Matasanmu Ƴan Ƙwaya marasa aikin yi.

Wayyo Arewa Allah ka zama Gatanmu 😭😭😭

12/06/2022

Mu Farka Ƴan Arewa

Shima fa Kwankwaso Ya kafa Gwamnoni a Yankinsa Kamar yadda Tinubu Yayi kawai dai... Daga Khadija Garba SanusiKamar yadda...
11/06/2022

Shima fa Kwankwaso Ya kafa Gwamnoni a Yankinsa Kamar yadda Tinubu Yayi kawai dai...

Daga Khadija Garba Sanusi

Kamar yadda ake ta Yamaɗaɗi cewar ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam'iyyar APC kuma tsohon Gwamnan Jihar Lagos Sanata Bola Tinubu ya kafa Gwamnoni a yankinsa na Yarabawa shiyasa ya samu damar amfani da yaran nasa wajen samun tikitin takarar shugaban ƙasa a Jam'iyya mai mulki to fa shima Ɗan Takarar shugaban ƙasa a Jam'iyyar NNPP kuma Tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso haka ya Kakkafa Gwamnoni a nasa yankin na Arewacin Nigeria kawai dai shi kwankwaso ya tsinci kansa ne acikin Al'ummar da basu ɗauki Butulci abakin komai ba kuma Al'ummar da s**a ɗauki sarar nakaika Inuwa ka Kaini Rana, Al'ummar da s**a zamo tamkar Macijin da zaka kiwata daga baya ya sareka.

Barrister Simong Bako; Gwamnan Jihar Plateau na yanzu kuma shugaban Gwamnonin Arewa Barrister Simong Bako Lalong yana ɗaya daga cikin Gwamnonin da kwankwaso ya kafa da hanunsa domin takarar Lalong ta Farko a 2015 ko office na Campaign Bashi da shi ballantana kuɗin sayen Form na Jam'iyyar APC a Chamber ɗinsa ta aikin Lauya yake gudanar da abubuwansa na siyasa, Kwankwaso ne ya saya masa Form na Takarar Gwamna sannan ƙungiyar Kwankwasiyya ta Plateau state ta bashi kyautar office ɗinta na Badamasi Plaza dake Bauchi Road acikin garin Jos domin yayi harkokinsa na siyasa sannan kuma Kwankwason ya tsaya kai da fata domin ganin Barrister Simong Bako Lalong ya tsallake a zaɓen cikin gida na Jam'iyyar APC wanda Badon Kwankwason ba da Solomon Dalung yayi ƙasa-ƙasa da Simong Lalong saboda yafishi kuɗi kuma yafi sanuwa acikin Al'umma amma haka kwankwaso ya shiga ya fita sai da Simong Lalong ya tsallake dukka zaɓubbukan 2015.

Badaru Abubakar; Gwamnan Jihar Jigawa Badaru Abubakar Talamiz duk da kasancewarsa Hamshaƙin mai kuɗi amma saura kaɗan tikitin takarar Gwamnan Jihar Jigawa ya kubce masa a 2015, Allah ya Tarfawa garinsa nono ne bisa ɗaukin da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kai masa, domin a lokacin har an ayyana Barrister Hassan Hadejia amatsayin wanda zai tsayawa APC takarar Gwamna a jihar Jigawa saboda rikici yaƙi ci yaƙi cinyewa tsakanin Badaru da Ubale to amma shi Barrister Hassan Hadeja da kansa yace bazai iya takarar Gwamna ba saboda bashi da kuɗi gashi kuma Jam'iyya mai mulki ta PDP zai tunkara hakan tasa rikici ya dawo ɗanye nan da nan Kwankwaso yakaiwa Badaru ɗauki kuma Allah ya taimake shi ya samu tikitin takarar Gwamna a jihar Jigawa cikin Jam'iyyar APC kuma Kwankwason bai rintsa ba sai da Badaru ya zama Gwamna a Jigawa wasu na ganin tsoma Hanun kwankwso dumu-dumu a siyasar Jigawa ta 2015 wanda yayi sanadiyyar faduwar Gwamnatin Sule Lamiɗo itace ta ƙara ta'azzara adawar siyasa tsakanin Sule Lamiɗon da Kwankwaso wacce har yanzu take ci Ganga-Ganga.

Nasiru Ahamad el-rufai; k**ar dai a Jihar Jigawa itama Jihar Kaduna abunda ya faru kenan tsakanin Nasiru elrufai da Shehu Sani, rikici ya kaure tsakaninsu kan wanda zaiyiwa APC takara a Jihar Kaduna shima dai Kwankwason ne yaje ya dafawa Nasiru elrufai domin ganin ya riƙewa APCn tutar takarar Gwamna a 2015 a Jihar Kaduna kuma hakan akayi Allah ya bashi Sa'a da taimakon Kwankwaso ya zama ɗan Takarar kuma Kwankwaso bai huta ba saida Nasiru ya zama Gwamna a Jihar Kaduna duk da barazar da s**a sha daga hannun Gwamna Maici Lamaran Yero wanda ya dinga ikirarin idan yaga dama sai ya rushe gidan el-rufai.

Abdullahi Umar Ganduje; a jihar Kano basai nace komai ba game da irin Gudun mowar da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayar wajen Tabbatuwar Gwamna Ganduje akan Kujerar Gwamnan Jihar Kano domin zai zamo k**ar ɓata baki ne babu abinda baku sani ba, abunda zan ƙara akai kawai shine a yau duk wani ɗan siyasa da Ludayinsa ke kan dawo a siyasa jihar Kano idan ka cire Sanata Mallam Ibrahim Shekarau to gaba dayansu Rainon Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ne rankatakaf babu ragin ɗaka.

To yanzu kuyi tunani da'ace waɗannan Gwamnonin Simong Bako Lalong,Badaru Abubakar,Nasiru elrufai da Ganduje sun tsayawa Kwankwso akan Lamuransa na siyasa da yake buƙatar yanzu a tsaya masa k**ar yadda ya tsaya musu a nasu lamuran na siyasa a lokacin da suke buƙatar a tsaya musu ɗin kwatankwacin yadda Gwamnoni yaran Tinubu s**a tsaya masa a yanzu da yake buƙatar tsayawarsu tunda shima ya tsaya musu a lokacin da yake da damar tsaya musu kuma suke buƙatar a tsaya musu ɗin. MENENE ZAI FARU?

Sannan kuma kuyi Tunanin da ace Gwamnoni da Tinubu ya kafa sun Butulce masa a yanzu da yake buƙatar taimako k**ar yadda Gwamnonin yaran Kwankwaso s**a Butulce masa a daidai lokacin da yake buƙatar taimakonsu, MENENE ZAI FARU?

11/06/2022

MAGANA TA GASKIYA DA GASKIYA

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya fi Atiku Abubakar da Bola Ahmed Tinubu cancantar ya shugabanci Nigeria idan aka auna su a mizani na adalci

Babu shakka a manyan 'yan siyasar Nigeria da suke tashe a yanzu babu wani dan siyasa a Arewa da yake kusa da talakawa, yake son talakawa tamkar 'ya'yan cikinsa, yake da zuciyar ya taimaki talakawa wanda babu shamaki tsakaninsa da talakawa k**ar Sanata Rabiu Kusa Kwankwaso

Ina da yakini a raina idan Kwankwaso ya zama shugaban Kasar Nigeria zai zama sanadi na kawo saukin rayuwa a Nigeria, talakawa zasuyi walwala, abinci zai yi sauki, zai dauki nauyin yaran talakawa su tafi manyan jami'o'i na duniya a Turai su samo ilmi na zamani

To amma inda babbar matsalar take shine Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a yadda yake yanzu haka bai da karfi da tasirin da zai iya kawo Nigeria, sai idan wani abu ya faru
Zan kawo cikakken bayani Insha Allah

Muna rokon Allah Ya mana zabi mafi alheri

Daga Datti Assalafy

Malam Ka Raba Kanka Da Ruɗani Ka Zaɓi Kwankwaso Da Yakinin Cewa Ko A Wurin Allah ka Fita, Domin Ka Zaɓi Mutum Mai Nagart...
11/06/2022

Malam Ka Raba Kanka Da Ruɗani Ka Zaɓi Kwankwaso Da Yakinin Cewa Ko A Wurin Allah ka Fita, Domin Ka Zaɓi Mutum Mai Nagarta.

Inji Ahmad Tijjani Gafai

DA DUMI-DUMINSA.Dan Majalissar Tarayya Mai Wakiltar Daura da Sandamu Hon.Fatahu Muhd da takwaransa Dan Majalissar Tarayy...
10/06/2022

DA DUMI-DUMINSA.

Dan Majalissar Tarayya Mai Wakiltar Daura da Sandamu Hon.Fatahu Muhd da takwaransa Dan Majalissar Tarayya Mai Wakiltar Mani da Bindawa a Jahar Katsina Sun Fice daga Jam'iyyar APC Zuwa Jam'iyyar NNPP Mai Kayan Marmari ta Kwankwaso.


Usman Kwankwason Rijiyar Lemo.

Farin jinin Kwankwaso ya sanya wata matashiya ikirarin fatan auren kwankwaso inda ta wallafa a shafinta k**ar haka "Ni s...
09/06/2022

Farin jinin Kwankwaso ya sanya wata matashiya ikirarin fatan auren kwankwaso inda ta wallafa a shafinta k**ar haka "Ni shi nake so domin ko nan da jibi ne a daura mana aure"

~ Inji Matashiya Maryam Hussaini

Kai Jama'a duk da ni ba ɗan APC bane amma jiya naji Takaicin abin da Gwamnonin Arewa s**a yiwa Baba Buhari.Duk irin cin ...
08/06/2022

Kai Jama'a duk da ni ba ɗan APC bane amma jiya naji Takaicin abin da Gwamnonin Arewa s**a yiwa Baba Buhari.

Duk irin cin mutunci da cika baki da Jagaba Bola Tinubu yayiwa Baba Buhari, Amma haka gwamnoni marasa kishin Shugaban su tare da kishin Al'ummar su, s**ayi fatali s**a marawa Tinubu baya.

Tinubu ya cika baki wai harda cewa Buhari ya fashe da kuka bayan ya fadi zabe sau uku, amma shi Tinubu ya lallasheshi yace zamu taimake ka. Tinubu ya ƙara da cewa amma bayan mun taimaki Buhari Ko Fura bai bamu ba b***e gari Kwaki.

Yace kai ko wata kwangila ko wani Muƙami bai tuna dani ba b***e ya bani. Yayi maganganu da yawa wanda lokaci bazai bari in zayyano muku su ba.

Anan nake ƙara tausayawa Buhari da magoya bayan sa duk da irin gwaninta da ayyukan raya kasa da akayi musu,ga Mataimakin Shugaban Ƙasa OSINBAJO amma lokaci daya s**a watsawa Buhari Ƙasa a ido.

Wannan ne zai tabbatar maka da wataƙila ƙarshen siyasar Buhari da magoya bayan sa yazo, domin ranar da wadannan mutanen s**a k**a Sitiyarin Motar, to ba masoyin Buhari ba duk wani ɗan Arewa kashin sa ya bushe.

A ƙarshe muna Allah wadai da wadansu daga gwamnonin Arewa da s**a marawa Makiyin Ƴan Arewa wannan tafiya.

Muna fatan kowa zaiyi karatun ta nutsu a babban zabe mai zuwa mu zaɓi Masoyin Al'umma Engr.Dr. Muhammad Rabiu Musa Kwankwaso na jam'iyyar NNPP mai Kayan Dadi

🍉🍉🍉🍉🍍🍍🍍🍍🍓🍓🍓🍓🍌🍌🍌🍌

Dan Ganduje da ya kai karar mahaifiyarsa EFCC ya gudu kasar EgyptBabban dan Gwamnan jihar Kano Abdulaziz Ganduje ya arce...
26/09/2021

Dan Ganduje da ya kai karar mahaifiyarsa EFCC ya gudu kasar Egypt

Babban dan Gwamnan jihar Kano Abdulaziz Ganduje ya arce zuwa kasar Masar bayan ya kai mahaifiyarsa Gwaggo EFCC kan badakalar kudade da cuwa cuwar filaye a Kano.

Abdulaziz Ganduje ya kwashe iyalansa gaba daya ya arce zuwa kasar Masar da su. Sannan ya bayyana cewar ha zai dawo Kano ba sai Ganduje ya sauka daga Gwamnan Kano.

Muddin A Kasamu Sauyin Gwamnati, :Ba iya Orji Uzor Kalu ba Hatta Ganduje Da Wasu Mukusan Tansa Saimun Tabbatar da Cewar ...
22/09/2021

Muddin A Kasamu Sauyin Gwamnati, :Ba iya Orji Uzor Kalu ba Hatta Ganduje Da Wasu Mukusan Tansa Saimun Tabbatar da Cewar Sun Girbi Abinda S**a Shuka A Gidan Yari, Cewar Lauya Femi Falana,

Shahararran Lauya Mai Kare Hakkin Dan Adam Wato Femi Falana Yayi Wasu Kalamai inda Yake Nuna Cewar Babu Wanda Zasu Bari Yaci Banza A Wadanda Aka Mayar Yan Gata A Wannan Gwamnati bayan Kowa Yasan Suna Da Kashi A gindi,

Femi Falana Ya Lissafo Mutum 3 Duk da Yace Akalla Suna da list din Mutum 16 Wadanda Yace Suna da Kashi A gindi Kuma Zasu tabbatar da cewar An turasu gidan Yari Su Girbi Abinda S**a Shuka Sannan A Yanzu Sun tura list din Sunanansu Wasu Manyan Kasashen Waje Domin Kwace Kadarorinsu Gamida Samu Ta Kunkumin Zuwa Wadannnan Kasashe,

Falana Yayinda yake Hira Da Gidan jarida Na The Channel Yace ba iya Orji Uzor Kalu ba Har Ganduje Da Wasu Manyan Makusantansa Sai Sun Girbi Abinda S**a Shuka Agidan Yari.

Saidai Femi Falana Bai Bayyana Sunan Makusancin Gandujen Da Yake Magana Akai ba Saidi Kwanakin baya Dan Gwamna Ganduje ya Kai Karar Gwaggo Gaban EFCC Wadda Take Matar Gwamnan Kano ce Kuma Mahaifiya Ga Wanda Yakai Karar.

The real Fake news is Buhari Government.
21/09/2021

The real Fake news is Buhari Government.

Abdulaziz Ganduje ya kai karar mahaifiyarsa Gwaggo EFCC kan batun almundahanaBabban dan Gwamnan Kano, Abdulaziz Ganduje ...
13/09/2021

Abdulaziz Ganduje ya kai karar mahaifiyarsa Gwaggo EFCC kan batun almundahana

Babban dan Gwamnan Kano, Abdulaziz Ganduje ya maka mahaifiyarsa Hafsat Ganduje gaban hukumar yakibda yiwa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC akan zargin da yake yi mata da almundahana da kuka azurta kanta ta hanyoyin da basu dace ba.

Tuni hukumar EFCC ta aikewa da Hafsat Ganduje mai dakin Gwamnan Kano da goron gayyata domin amsa tambayoyi kan zargin amma taki amsa gayyata, ba kuka tare da ta bayar da wani uzuri a rubuce ba.

A cikin wasikar da Abdulaziz Ganduje ya aikewa da EFCC ta shafi badakalar filaye da kuma kudade. Sai dai kakakin hukumar EFCC Wilson Uwujaren yaki cewa komai gake da batun da aka yi masa tambaya akai.

Idan ba a manta ba, a baya an zargi Gwamnan Kano Alhaji Abdullahi Umar Ganduje da yin badakala ta sama da dalar Amurka miliyan biyar, inda aka nuno shi a wani faifan bidiyo yana karbar dalar Amurka daga cikin kudaden 'yan kwangila, Gwamnan dai ya karyata bidiyon tare da kai karar jaridar Daily Nigerian da mawallafinta Jaafar Jaafar gaban kotu game da batun bidiyon Dala.

'A cire tsoro ayi abinda ya dace'Uwar gidan Shugaban kasa Hajiya Aisha Buhari ta wallafa wani faifan bidiyo na Ministan ...
12/09/2021

'A cire tsoro ayi abinda ya dace'

Uwar gidan Shugaban kasa Hajiya Aisha Buhari ta wallafa wani faifan bidiyo na Ministan Sadarwa Isa Ali Pantami yana kuka a wani darasi da yake gabatarwa a Masallacin Annur dake Abuja, ta rubuta 'A cire tsoro ayi abinda ya dace'. Aisha Buhari ta wallafa wannan sako ne a shafinta na Instagram.

08/08/2017

WASU INYAMURAI SUN DAMFARI GWAMNAN KANO.

wasu yan kabilar Igbo sun damfari gwamnan kano abdullahi umar ganduje

Su dai wayannan inyamurai sun zo ne Daga Abuja k**ar yadda s**ace

Wai uwar jam'iyyar APC ce ta turosu domin ayi zaben shugabanni

Anan ne maigirma gwamna yabasu masauki tareda yi musu alheri na milliyoyin nairori

Amma bayan tafiyar su Sai uwar jam'iyyar APC ta kasa tace ita bata turo kowa ba

Dan haka batasan dawani zabe ba
Umar haruna doguwa Wanda aka zaba tun 2014 Har yanzu shine shugaba

Yanzu dai Ganduje yana tsaka mai wuya tun bayan wannan damfarar da sojan gona da akayi masa

Daman dai damfarar gwamnoni yanzu yazama ruwan dare a Nigeria
Inda ko akwanakin baya Saida wasu mutane s**a damfari gwamnan jihar ekiti ayodele fayose ta hanyar nuna masa hotunan bogi Wanda s**ace na shugaban kasa buhari ne

Ance dai fayose yakashe wajen million 20 kafin yasamu hotunan

Wanda Daga baya aka tabbatar da cewa na bogi ne yan damfara ne kawai s**a cuceshi

Sai gashi yanzu ma sun kuma aikata irin wannan damfarar ajihar kano

To Allah ya kyauta

08/06/2017

A Yaune Senator Rabi'u Musa kwankwaso yaje Da Kudurin Rage kudin Aikin Hajji Gaban majalisar dokoki daga 1, 500, 000 zuwa naira #800,000

20/05/2017

Ra'ayi

Gwamna Ganduje Da Albazaranci

Sheriff Almujir

Na rasa da mai zan wasafta abunda kuka yi, wauta ce wannan ko mugunta? shin kun dauka Allah ba zai tambaye ka akan almubazzaranci ba ne?

Kwanaki zan shiga tashar Unguwarmu, aka ce sai na biya N100 na ce saboda me? Aka ce wata mata ce ta sayi tashar kuma ta kara kudin shiga daga N50 zuwa N100, sannan har motocin da ba na kasuwa ba ma su kawo fasinha sai sun biya. 'Yan Kamishon sun nuna takaici matuka da wannan shawara.

Yau kuma na wayi gari da hotunan wannan Hall na Coronation watau dakin taro din da aka kammala shi gaf da karshen gomnatin Kwankwaso. Kowa yana yaba kyawun shi da ingancin kujerun cikin shi. Kun b***e komai cikin shi kun chanza. Ba don rashin kyau ba, kawai saboda adawa da almubazzaranci da dukiyar talaka. Bayan ga makarantu, asibitoci, kasuwanni, tituna na neman gyara.

Ina kira ga talakan Najeriya musamman na Arewa, da mu yi Allah wadarai da adawar da za ta kai ga cutar da talaka saboda zunzurutun bukatun 'yan siyasa.

(c) Kano a Yau

11/05/2017

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso

Allah Daya Gari Bambam Yayinda Galibin Yan Majalisu Gwamnoni Da Kusan Daukacin Shuwagabannin Siyasa Masu Rike da Madafun Iko Ke Tsallake Rijiya Da Baya Da Shan Ruwa Duwatsu Daga Wasu Fusatattun Mabiyan su. Sak**akon Zargin Yan Siyasar Da Jefa Kasa Da Yan Kasa Cikin Mawuyacin Hali,

Nan Tsohon Gwamnan Jihar Kano Ne Kuma Jigo a Jam'iyyar APC Mai mulki Kuma Sanata Kano ta tsakiya Rabiu Musa Kwankwaso Yayin Wata Ziyara A Jihar Kaduna Inda Ya Ratse Da Yan
Tawagarsa Wani Gidan Mai Don Shan Mai

Amma Abin Mamaki Kan Kace Kwabo Tuni Matasa Da Yara S**a Cika Gidan Man nan don ganin Sanata Kwankwaso tare da kiran Sunansa da Zummar Daga Buhari Sai shi Zuwa Villa Kome Masu Karatu Zasu'ce Akan Haka?

Daga Musa A. Musa

08/05/2017

Jerin Sunayan 'Yan Matan Chibok 82 Da Mayakan Boko Haram S**a Saki Jiya:

1. Kwatah Simon
2. Grace Dauda
3. Jummai Paul
4. Tabita Pogo
5. Yanke Shetima
6. Jummai Miutah
7. Juliana Yakubu
8. Mary Yakubu
9. Rulh Kolo
10. Mairama Yahaya
11. Racheal Nkeke
12. Fibi Haruna
13. Asabe Manu
14. Eslher Usman
15. Filo Dauda
16. Awa Ababa
17. Lydia Joshua
18. Na Oni Bitrus
19. Marlha James
20. Palmata Musa
21. Aisha Ezekiel
22. Mwada Baba
23. Hannatu Ishaku
24. Mwa Daniel
25. Rifkafu Soliman
26. Maryamu Yakubu
27. Rebecca Joseph
28. Ladi Audu
29. Amina Pagu
30. Sarah Nkeki
31. Esther Joshua
32. Saraya Yanga
33. Ruth Amos
34. Hauwa Musa
35. Hauwa Ishaya
36. Glory Aji
37. Mary Ali
38. Rahilla Bitrus
39. Luggwa Mutah
40. Lataba Maman
41. Lydia Habila
42. Deborah Peter
43. Naomi Yaga
44. Kwajigu Haman
45. Lugguwa Samuel
46.Maryamu Lawan
47.Tabita Hellapa
48. Ruth Ishaku
49. Maryamu Musa
50. Magaret Yama
51. Kauna Lalai
52. Solomi Tacitus
53. Naomi Yahona
54.Maimuna Usman
55.Grace Paul
56.Hauwa Ntakai
57.Yana Joshua
58. Comfort Bulus
59. Ramatu Yaga
60. Rhoda Peter
61. Naomi luka
62. Naomi Adamu
63. Iyatu Habila
64. Victoria wullgam
65. Ladi Ibrahim
66. Christiana Ali
67. Hanatu Stephen
68. Patina Fagbi
69. Martha James Bello
70. Tabita Silas
71. Yana Bukar
72. Abigail Bukar
73. Hadiza Yakubu
74. Naomi Zakariya
75. Maryamu wavi
76. Amina Bilama
77. Asabe Lawan
78. Mary Dauda
79. Maryamu Bilama
80. Naomi Filiman
81. Saratu Ayuba
82. Awa Yirma.

Bashir Ahmad
P.A New Media
7/5/2017

07/05/2017

Copied

MALAM AISAR FAGGE NE YA RUBUTA

Mu ceci rayuwar Nayif!

Nayif Isma'il yaro ne matashi dan kimanin shekara 19-20. Ga shi mahaddacin Alqurani kuma malamin makarantar Ansarissunnah Littahfizul Qur'an da ke Fagge.

Sama da shekaru biyar da s**a wuce, yana daya daga cikin limaman da suke jagorancin sallar Tarawih da Tahajjud a masallacin marigayi Sheikh Abubakar Hussein (Albany).

Allah ya bawa Nayif murya mai dadin gaske. A duk lokacin da yake jagorancin sallah za ka ji yana sa ma shauqin karatu da haddar Alqurani.

Allah ya jarrabi Nayif da ciwon qoda duk guda biyun. Yanzu ya zama tilas indai ana so Nayif ya rayu, kuma ya ci gaba da rairawa mutane qira'annan mai dadi, to dole sai an yi masa dashen koda (transplant).

Kusan tun 2015 aka gano (test) cewa qodarsa guda daya na da dan matsala. Amma wannan banzan tsarin na Asibitin Malam Aminu Kano na ba za ka ga Likita ba (appointment) sai bayan wata daya ko biyu ya taimaka wajen lalacewar daya qodar.

Kuma s**a zo s**a ringa canki-in--canka, su ce aje ayi test din ulcer, typhoid, malaria, dss har al'amura s**a lalace. Irin wannan dabi'ar ta su ce tayi sanadiyar mutuwar wata babbar mace a unguwarmu! Shi ya sa danta wani Farfesa ya rubuta article ya kira su da "Killer Hospital!".

Nayif yana kwance a Asibitin Nassarawa. Da, sau daya ake yiwa Nayif wankin qoda, amma yanzu abun ya tsananta ya zama dole sau biyu ake wanke ta. Kwana biyu bani da lafiya, domin ranar Litinin daTalata ko fita ban yi ba, amma jiya da naje naga Nayif wallahi sai naji na warware.

Halin da yake ciki dole ya sa ka zubar da hawaye. Yanzu an samu wani asibiti a India za su yiwa Nayif aiki amma ana buqatar kusan miliyan goma sha daya. Subhanallah!

Yanzu taimako kala biyu su Nayif suke buqata: Kudin da ake masa wankin qoda da kuma Kudin da za a fita da shi waje.

'Yan uwa bayin Allah; wanda Allah ya horewa, ko wanda ya san wani mai tamakawa, mu hadu duka mu taimakawa Nayif. Mu ceci rayuwarsa.

Mai girma chairman din Fagge; Hon Habibu Sale Mai Lemo, mai girma dan majalisar jiha na Fagge; Hon. Abdullahi Yusuf Ata, Mai girma dan majalisar tarayya na Fagge; Hon. Aminu Suleiman Goro, dukkaninku kuna da rawar da za ku taka wajen ceto rayuwar wannan hafizin alquranin.

Wadanda suke da kusanci da wadannan mutanen su taimaka wajen sanar da su halin da Nayif yake ciki. Allah ya bawa kowa ikon taimakawa. Amin. Allah ka yiwa Nayif tsawon rai. Amin.

Ga wanda Allah ya horewa zai iya taimakawa fi Sabilillah ga account din yayansa k**ar haka:-

Account name : Assad Isma'il Zakariyya
Account Number :3019347746
Bank Name : First Bank

07/04/2017

Muna da gwamnoni, da suke tafiya China, Su shafe kusan wata daya , a karshe su dawo da yarjejeniyar bashi. China ta baka rancen 1.8 billion 💲 wai ka gina Rail🚈 mai amfani da lantarki. Bayan
Jirgin daga China
Titin Jirgin daga China
Enjiniyoyi daga China
Leburori daga China
Direbobin daga China

A karshe me ka amfana dashi ?
Baka gina wata Masana'anta da masu hawa jirgin zasuje suyi aiki ko su samu aiki ba.
Baka gina wata Makaranta da Dalibai zasuje suyi amfani da Jirgin ba.
A karshe ka kashe harkar kananan masu sufuri k**ar Adaidaita Sahu, da Sauran 'Yan Kabu Kabu ba.

A makalar Sarkin Kano Muhammad Sunusi ll da yayi jiya a Kaduna.

31/03/2017

A madadin dukkan ma'aikata na wannan gida mai albarka muna taya abokan aiki na sashen Hausa na BBC murnar cika shekaru 60 suna watsa shirye shirye da harshen Hausa. BBC Hausa Allah ya kawo wasu Shekaru masu albarka.

15/03/2017

Kwankwaso: Garkuwar Arewa

Kafafen watsa labaru na waje sun ruwaito ziyarar da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya kai jiya garin Ile-Ife tare da jakadan kasar Nijer a Nigeria don jajantawa Hausawa wadanda rikicin satin da ya wuce ya shafa. Mu ma muna mika jajenmu gare su.

Wannan ba shi ne karo na farko da Sanatan yake jefa kansa cikin ayyukan taimako ga tsirarun al'ummunmu wadanda ake zalunta a kudancin Nijeriya ba. Kan ba a mance ba - dan'adam kuwa mai saurin mantuwa ne - ya kai irin wannan ziyara lokacin da aka yi fada a Mile 12 har ya taimaka da karbo belin yaranmu da aka tsare bayan taimako na kudi da ya bayar.

Yabon gwani ya zama dole. Kwankwaso - k**ar yadda muka saba kiransa - yana cikin manyan Arewa kalilan wadanda za su iya fitowa su danganta kansu da mutanensu a cikin halin rikici. Akasarinmu mun gwammce mu yi shiru mu yi ta sambatu a boye ko dak'uwa cikin duhu wai don kar daya bangaren su zarge mu da kabilanci, miyarmu ta siyasa ko mukami ta baci. An sha a yi rikici a zalunce mu, mafi yawa ko tari ba sa iya yi.

Ga dukkan alamu Kwankwaso bai damu da irin wadannan zarge-zarge ba duk da cewa shi dan siyasa ne. Haka ake son namiji. Ina fata zai ci gaba da wannan hali nasa mai matukar kyau har ma ya jawo wasu manyan cikin wannan kokari. Abin da Arewa ta ke nema ke nan tun shekaru don mutanenta su fita maraici.

Kan da ina da iko, da na nada shi "Garkuwar Arewa." Ina fata wadanda suke da wannan halin za su yi masa wannan karimcin. A wannan shafin nawa, ni kam na ba shi. Saura su dada masa.

Dr. Aliyu U. Tilde
15/3/17

14/03/2017

Assalamu Alaikum

Ga sakon gaggawa ga yan Kwankwasiyya, gwamnatin jihar Kano ta hannun kwamishinan yada labarai Muhammad Garba ta biya kuma ta dauki nauyin wasu manyan Jaridun Nigeria domin su buga labarin karya cewar wai Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya fice daga Jam'iyyar Apc ya koma Jam'iyyar PDP.

Wannan kwamishinan yayi hakane da nufin su kawar da hankulan magoya bayan Sanata Kwankwaso daga yada abubuwan alkairan da Kwankwaso ya jagoranci yiwa al'ummar Arewa mazauna garin Ile Ife.

Saboda haka muna kira ga dukkanin yan Kwankwasiyya da kada wanda ya tsaya bata lokacinsa wajen mayar musu da martani akan waccar karyar da s**a shirya.

Muci gaba da yada ayyukan alkairi na Sanata Kwankwaso mubarsu suyi ta karairayinsu.

Salisu Yahaya Hotoro.

14/03/2017

DA A BAKA LABARI.

Sanata Kwakwaso Ya Nufi Jihar Osun Kan Rikicin Hausawa Da Yarbawa A Ile Efe

A yanzu haka Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na Ibadan inda ya shiga mota zuwa Oggomosho Babban Birnin Jihar Osun domin ganawa da gwamnan Jihar Osun Alhaji Rauf Aregbesola a daren yau dangane da kisan gillar da aka yi wa Hausawa a garin Ile Ife.

Bayan sun gama tattaunawa da gwamnan Jihar Osun a daren yau, gobe da safe Sanata Kwankwaso zai nufi garin Ile Ife domin tattaunawa da Sarakunan gargajiya na masarautar Ife da nufin jin musabbabin wannan kisan gillar da aka yi wa Hausawa a garin na Ile Ife domin a zakulosu su fuskanci hukuncin abinda s**a aikata.

14/03/2017

Masha Allah. Yabon gwani ya zama dole.

A yanzu haka Sen. Rabiu Musa Kwankwaso sun kammala tattaunawa da gwamnan Jihar Osun Alh. Rauf Aregbosola akan batun kisan gillar da aka yiwa yan uwanmu Hausawa a garin Ile Ife.

Gobe da Safe Sen. Kwankwaso zai wuce garin Ile Ife domin tattaunawa da Sarakunan gargajiya na wannan garin.

07/03/2017

Bayan Amarya Ta Haihu A Daren Farko. Wa Ya Auri Kanwar Sa.

Jim kadan bayan gurfanar da Habiba Inusa a gaban kotun Shari’ar Musulunci ta karamar hukumar Doguwa a jihar Kano da laifin Zina da kuma boye juna biyu. Wata sabuwar badakala ta kara bulla yayin da Wa da kanwa s**a hada baki s**a je aka aurar da su a matsayin masoya domin karbar kayan dakin amarya.

Jaridar ta jiyo daga kwakkwarar majiya cewa, wannan ‘yar burum-burum ta faru ne a karamar hukumar Tarauni. Kana kuma nan ba da jimawa ba za a iya samun wasu abubuwan marasa dadi da aka kitsa a yayin auren.

07/03/2017

"Rashin Kunyar Da Kwankwaso Ya Dinga Yi Wa Jonathan Ce Silar Faduwarmu Zabe"

Tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo a cikin raha ya fadawa tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso cewa rashin kunyan da Kwankwason ya dunga yiwa mai gidansa Jonathan ce ta jawo 'yan Nijeriya s**a yi musu bore a rumfunan zaben shugaban kasa da gwamnonin da aka gudanar a shekarar 2015.

Namadi Sambo ya bayyana hakan ne a wurin bikin cika shekaru 80 da haihuwar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.

Sai dai a nashi martani Sanata Kwankwaso ya mayar masa da martani nan take inda ya ce boren da kuka yi wa kakanku Obasanjo shine silar faduwarku don kuwa duk wanda ya bijirewa kakansa ko ubansa ba zai gama lafiya ba ko waye shi.

A cikin raha Namadi Sambo ya ce "e na yarda da maganarka. Aku sarkin magana".

Kwankwaso ya ce to gobe sai ku kara.

Address

Farm Center Street, Opposite Tarauni
Kano

Telephone

+966540047745

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kano a Yau Kano Today posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Kano a Yau Kano Today:

Videos

Share


Other News & Media Websites in Kano

Show All