Zabiya Hausa

Zabiya Hausa Sabuwar Kafar Yaɗa Sahihan Labaran Duniya, cikin harshen Hausa za ku iya bamu taku gudun mawar waj

Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun Ni ganau ne ga yadda likitocin wani Asibitin gwamnati a jihar Kano,  s**ai ta jeka ka ...
05/09/2020

Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun

Ni ganau ne ga yadda likitocin wani Asibitin gwamnati a jihar Kano, s**ai ta jeka ka dawo da mahaifin wani yaro Ɗan kimanin shekara 1 da rabi da haihuwa , game da yadda ya hadu da iftila'in Ƙonuwa da tafashashshen ruwan zafi.

Amma kuma ƙememe likitocin asibitin sun gaza tai maka masa a. Kwantar dasu ma, har kawo lokacin nan karfe 11pm na dare.

Babu tabbacin mahaifiyar yaran da mahaifinsa sun iya kai abinci bakinsu, tun misalin karfe 2 na rana da lamarin ya faru, wanda da ruwan girkin ne amma kuma abincin da ba'a kammala ba kenan, tun misalin karfe 2 s**a isa cikin asibitin kawo karfe 11pm na dare, ba'a basu wajen kwantar da yaran ba.

Wai abayanin likitocin Gado 3 ne kadai na Yara a asibitin kuma duk anyi Booking dinsu, wato dai da masu su.

Kashhhhhj

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un
Lamarin ya bani mamaki da tsoro yanzu a akasata wannan Al'amari. Yake faruwa...?

Wa'iyya zubillah wannan wane irin rashin imani da tausayine haka...?

😢 😢

Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari, ta yi maganarta ta farko bayan dawowarta daga Dubai, hadaddiyar daular Larabawa UA...
22/08/2020

Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari, ta yi maganarta ta farko bayan dawowarta daga Dubai, hadaddiyar daular Larabawa UAE bayan gajeriyar jinyar da tayi.

Ta mika godiyarta ga yan Najeriya da s**a sanyata cikin addu'o'insu yayinda take kwance babu lafiya a Dubai.

Ta ce yanzu ta warke kuma ta samu lafiya.

Aisha Buhari tace Yayinda dawowarta jirginsu ya dan samu mishkila cikin hazo, amma matukan sun samu daman shawo kan lamarin.
Cikin wani Jawabinta a shafinta na Twitter.

27/11/2017

Kyautar Mota Ga Wanda Ya Amsa Wadannan
Tambayoyi Da Hujja Bisa Dalili. Don Amsar
Kyautarka Ka Tuntubeni A Wannan Numbar
(07033803929 ko 08103513807
1. Wanene mutum na farko da yafara tura
amalanke (wheel barrow) a kasar Nigeria?
2. Wacece matar farko da tafara tuyan kosai ko
doya na sayarwa?
3. Naira nawa Anini ya sata lokacinda yake raye?
a) nawa yabaiwa talakawa?
b) nawa ya baiwa yan'uwansa?
4. Wanene dalibin farko da yafara takawa izuwa
makaranta daga gidansu?
a) a wane gari yake?
b) wace Makaranta yaje?
5. A wace gari aka fara samun mahaukata?
a) su nawane
b) yaya sunayensu?
6. Menene sunayen wadannan abubuwa da
turanci?
a) gyatsa?
b) shaquwa?
c) kwarkwasa
d) gurasa
7. Wanene mutum na farko daya fara shigowa
Nigeria bayan hadewarta?
a) ta wace gefe ya shigo?
b) daga ina yake?
c) a wane lokaci?
8. Bayan shigar shugaba Buhari A*o Rock
a) sauro nawa ya samu a villa?
b) zuwa yanzu nawa aka kashe?
c) nawa s**a saura?
9. Wanene mutumin farko da ya fara shan Garri
babu Sugar a Africa?
10. Waye ya fara tarewa a cikin garin Abuja bayan
bata Babban Birnin Tarayya
ALLAH YA BADA SA'A.

07/11/2017

TARIHIN KANO DABO CI GARI
CHAPTER 3

BAGAUDA YAZO KANO.A irin labarin da barbushe yake yine wata shekara ya baiwa jama'arsa labarin cewa watarana na zuwa ko a zamaninsu ko a zamanin yayanzu wata alumma zato zo ta karbe kasar daga garesu ta gina masallatai harkuma yace dasu farkon abin wani mutun ne zaizo da rundunarsa ya mallake kasar da s**a tanbayesa ko akwai dabara sai yace dasu ba wata dabara sai hakuri domin lallai wannan mutum ba abunda zai hanashi zuwa.yakara dacewa zaizo ya shafe kabilarsu a manta dasu dungurum zai kafa tasa kabilar wanda zata shahara takuma yi shekaru masu yawa tana mulki.watau kenan gunkin tsumburbura yana iya jama'arsa ishara da zuwan BAGAUDA DAN BAWO JIKAN BAYAJIDDA wanda zaku karanta shikayar kakanninsa nan gaba
Saboda tsawon zamani sai irin mutanen barbushe masu tsananin tsafi da karfin jiki s**a fara karewa sai mazauna wadannan duwatsu dake kewaye da kano s**a zama basu da tsayayyen shugaba don haka sai zalunci da sauran abubuwan barna s**a yawaita har s**a ringa kai kukansu wajen wata sarauniya dake mulkin arewa da kano ita wanan sarauniya itace sarauniya DAURAMA sarauniyar daura.
Ita dai daura tsohuwar masarauta ce mai dadadden tarihi ga yadda tarihi ya nuna bagauda yana daya daga cikin yayan bawo dan bayajidda wanda yazo daura a zamanin sarauniya daurama har yakashe wata mashahuriyar macijiya wacce ake cemata sarki ance yazo barno daga gabas da rundunarsa ya mallake kasar BAGARMI kuma ya kwararo barno sai sarkin barno yaji tsoron yaki dashi sai ya hillaceshi ya bashi wata yarsa wai ita MAGARAM ya aura da ganin wanan amana da sarkin barno ya bashi sai bayajidda ya saki jikinsa har ya rinka baiwa sarkin barno aron jarumawansa in za shi yaki da kadan da kadan sai bayajidda ya watsa rundunarsa kowa ya k**a gabansa da sarkin borno yaga bayajida bashi da kowa sai ya tasarma kasheshi bayajida ya gudo da matarsa yayiwo yamma har ya iso garin gabas ta kasar hadeja anan magaram saboda tsananin wahalar ciki takasa ci gaba don haka bayajida ya barta anan bayan ya tafi sai ta haifi da namiji aka sa masa suna BIRAM shikuwa bayajida yayi ta tafiya har daura
Ya iso daura cikin dare ya sauka gidan wata tsohuwa yace ta bashi guga zai bawa dokinsa ruwa sai tace dashi ai rijiyar ba a samun ruwa sai kwana bakwai domin akwai wata macijiya kowa yaje dibar ruwan ba alokacin dibaba sai ta kashehi bayajida yace ta bashi gugar yaje yagani da yaje ya zura gugar a cikin rijiyat da ake ce da ita KUSUGU sai macijiyar nan mai suna sarki ta rike gugar bayajida ya jawo gugar tare da ita yak**a kan macijiyar ya datse da takobinsa ya jibge gawar a bakin rijiyar ta taho da akan ya kawo gugar da ruwa ya bawa tsohuwa ita wanan rijiyar har yanzu tanan a daura
Da gari ya waye mutane s**aga macijiyar nan sarki a mace babu kai nan da nan aka gayawa saraujiya daurama sai sarauniya tace wanda duk yakashe macijiyar nan yakawo kan zan bashi rabin mulkina sai mutane s**a ringa saro kan macizai ana gwadawa amma in an gwada da gangar jikin sai a ga baiyi daidai ba ana cikij haka sai tsohuwar nan da bayajida ya sauka a gidan ta tazo ta ce akwai wani bako da yazo da wata dabba k**ar saniya (WATO DOKI) yaje rijiyar nan da daddare yako samo ruwa da aka kirashi sai yace shine yakashe macijiyar nan ya kuma nuna kan aka ga kuwa yayi daidai sarauniya tace za ta bashi rabin mulkinta sai yace a a sai dai a daura masu aure aka daura masu da sarauniya mutane s**a sawa bayajida lakabi makas-sarki da ga baya a ka daina fadar makas sai sarki kawai daga nan ne kalmar nan sarki ta samo asali amma kafin bayajidda yazo daura har yakashe macijiyarnan ita dai sarauniyar nan kiran ta KABARA watau ubangiji da bayajida ya auri sarauniyar sai ta bashi kwarkwara wacce ta haifi da namiji da aka sawa suna (KARAB-GARI) nufin wanan kwarkwara tunda bayajida ya samu gadonsa kwarkwara da danta sun karbe gari kenan har yanzu akan yiwa sarakunan daura kirari ana cewa KARAB-GARI ) kai ab bawo da sarauniya ta haihu sai aka sawa dan suna BAWO watau a nan sarauniya ta mayarwa da kwarkwara martani kenan da nufin (KAWO GARI DA KUKA KARBA ) daga nan ake kiran dan bawo

Sing ....................daga

Naku a koda yaushe wato Abba mai gidan zagezagi kanon dabo ci gari
07033803929

06/11/2017

TARIHIN KANON DABO CIGARI

A kashen karni na tara (9th century) na masihiyya wadanda maharba wadanda babu hakikanin daga inda s**a fito sosai amma dai daga wajen arewa suke s**azo s**a zauna kan duwatsun dake ke waye da sararin da ake kira kano yanzu irin duwatsun sune irin (DALA DA GWAURON DUTSE)
Su maharban nan s**a ringa yin farauta a wanan kurmi wanda yake shine tushen rafin jakara inda kasuwar kurmi ta kano ta samo suna da wadannan maharba s**a jarraba dan noma s**a ga gurin yana da albarka sai s**a ci gaba suna saran daji suna gonaki albarkar gurinnan mai ban mamaki sai tajawo wadansu mutane daga wadnsu wurare suna zuwa da taron mutanen yafara yawa sai s**a yi shugaba wanda a bisa aladar mutanen wanan lokacin mai nisa ya kan zama mutum ne dake da fifiko da karfi game da tsafi
Babu tahakikanin akan irin tsarin mulkin da wadannan alumma s**a gina shugabancin su amma duk da haka ana iyacewa aikin shugaba awanan lokacin bai wuce tsara dokokin farauta ba dakuma kusanci da tsafin da mutane ke bautawa ba
BARBUSHE DA TSUMBURBURA
shugaban da wadannan mutane s**a zaba shine barbushe shikuwa mutum ne kato karkarfa mai tsananin gizo da gashin baki yakan sanya warki ya rike kulki a hannunsa yana iya kashe giwa ya daketa yayi tafiyat wuni guda da ita gidansa a kan dutsen dala yake inda wani gunki da jama'ar ke bautawa yake cikin kewayayyiyar bukka wanan gunkin tsumburbura shi ake kira SHAMUS daya daga cikin gunakan zamanin annabawa irin su YAKUKA DA YAGUSO wadanda aka ambacesu a cikin alkur'ani cikin sutarun nuhu tsumburbura shine ainahin aljanin nan da yan bori ke kira (DANKO DAN MUSA)
barbushe shine sarkin fadan tsumbirbira shine tamkar wakilin wanan gunki wanda alhakinsa shine kula da jama'ar dake bautawa wanan tsafin da yake shi barbushe shikadai yake da izinin shiga wajen zumburbura shi yake karbo sakon shekara daga gunkin ya fadawa mutane yana da fadawa k**ar su TUNZAGU mai gida a gindin gwauron dutse daga gabas a kwai kuma DANBURU mai gida a jigirya da JANDAMISA mai gida a magwan da HAMBARAU mai gida a tanagar da GUMBARI mai gidan fanisau da wadansu da yawa wajen dutsen DANBAKOSHI DA DANKWAI
Gidan barbushe a kan dutsen dala yake baya saukowa sai shekara idan lokaci yayi sai mutanen nahiyoyi da fadawan nan nasa suke su hadu a jikin dutsen dala s**anzo tare da bakaken bunsurai da karnuka wadanda zasu yankawa gunkin nan idan angama basu labari da zarar almuri tayi sai barbushe ya gangaro da makada sufara kida shukuma sai yayi ihu da karaji sa'anan yayi wadansu maganganu na kalmomin tsafi yace jamuna akasa mungama sai mutane s**e ga tsumburbura kanawa ga magajin dala sa'anann sai ya koma bisa dala jama'ar nan na ta biye dashi da bunsurayenan da karnuka sai a yanyankasu sai kuma shi barbushe yace nine magajin dala da kunki da kunso ku bini ba ra'ayi ba sukuma sai s**e maigida bisa mamabum mun bika ba ra'ayi. ba sa anan sai suyi tsirara mazansu da matansu su kewaye ginin da tsumburbura ke ciki shukuwa barbushe sai ya tafi da manyansu kofar dakin tsumburbura suyi sujjada kuma sai ya shiga wurin tsumburbura ba zai fito ba sai da safe in ya fito sai yabasu labarin abinda zai auku a wanan shekara k**ar yadda yajiyo abakin tsumburbura

DAGA NAKU ABBA MAI GIDAN ZAGEZAGI KANON DABO CI GARI

07033893929

05/11/2017

TARISHIN KANON DABO CIGARI
Kashi na daya (1)
KANO DA MUTANENTA NA ASALI

DANGANTAKA DA SAURAN KASASHEN idan ana so a lakanci tarishin kano sosai dole sai an tabo tarihin kasar hausa shikuwa tarihin kasar hausa sai an leka cikin tarihin sudan shikuwa tarihin sudan sai an leka cikin tarihin daular larabawa ta banu ummayyata da ta banu abbasi har ila yau kuma da binciken labarin wani tunzuri da yasa jama'a s**a rinka kauratowa daga tsakiyar kasar asiya s**a yiyo yamma.
Kasar sudan itace yankin kasar afrika na wajen tsakiya daga gabas tayi iyaka da kasar habasha wato (ETHIOPIA) daga arewa tayi iyaka da sahara daga kudu tayi iyaka da yankin gabas tekun Atlantic da ake kira (GULF OF GUINEA) da kuma kasashen sunkurun kurmin nan na tsakiyar afrika kalmar nan sudan ma'anarta baki saboda galibin alummar dake zaune a yankin sudan masu bakar fatane ance zafin rana shike sasu baki gama dukkan kasar sudan tana daf da wurin da ake kira (HUDDUL-ETIDALI)wato equator kasar hausa itace yankinnan na kasar sudan wadda ke wajen tsakiya-tsakiya daga gabas da ita ga kasar BORNO daga yamma ga kasar DAHOMEY wacce yanzu ake kira jamhuniyar benin daga arewa ga hamadan sahara daga kudu kuma ga kasashen nupe da kasashen da ake kira MIDDLE BELT kasar kano tana daga yankin zakiya na arewacin kasar hausa daga gabas tayi iya ka da kasashen borno da bauchi daga yamma tayi iyaka da katsina daga kudu tayi iyaka da zariya daga arewa tayi iyaka da kasar neja tun daga yanzu za a fahimtar alle kano wajibine ta zama babbar alkarya saboda itace k**ar zakiyar kasar sudan duka tunda dadewa kasar hausa dakuma sauran kasashen sudan sun samu aladunsu na zaman duniya daga fuska biyu mabanbanta wato gabas da yamma sa'ad da sabawa ta sa jama'ar kasar mangoliya ta zakiya s**a ringa fuskantowa yamma yamma a hankali sai masarautar ta ringa kafuwa in wannan ta fadi sai wannan ta tashi. a chan gabas shine daga bisani mulkin faris (WATO PERSIA)ya kafu ya mallaki kasashen duka
Bayan wanan sai mulkin yunana(WATO GREECE) ya kafu a yamma cikin turai (WATO EUROPE) tundaga sannan gaba ta kunsu tsakanin gabasawa dake bin mulkin yunana da farisawa na daular gabas labarin yadda sarki yunana zulkalnaini (WATO SALADIN SARKI DA KAHO) ya mamaye kasar fatisa ya zarce har hindu (wato India) ba boyayye bane
A kwana a tashi sai mulkin rumawa (roman empire) ya daukaka yakai ga ya rabu biyu daya gabas daya yamma (wato Byzantium empire) sai gabar dake tsakanin gabas da yamma ta mike bayan kafuwar annabi da sahabbai sai daular bani ummaiyata ta kafu ta sheka dari tana mulki a birnin kudus (wato Damascus) sa annan daular bani abbas ta motsa ta kori ta ummaiyu ta gaje bagadaza (wato Baghdad) da Allah yasa banu ummaiyata da sauran shan ruwansu a sarauta sai jama'ar su dake chan yamma wajen magribul-aksa s**a nada abdurrahaman halifan gabas a andalusiya cikin kasar hispaniya (wato Spain) sai tsohuwar gabannan gabas da yamma ta sake kafuwa domin gabas ga banu abbas yamma ga banu ummaiyyata tsakanin kasar sudan da daulolin nan guda biyu hanyoyi biyune kawai hanya daya agabas daya a yamma don haka ashe mutanen gabashin sudan lallai daga daular larabawa ta gabas suke wato daular banu abbas zasu sami saduwa ta hanyar gabas
Na yammacin sudan kuma ta hanyar yamma zasu sami saduwa da daular larabawa ta banu ummaiyata takasar anldalusiya haka kuwa abin ya gudana sai mulkin KANEM ya kafu a gabas cikin sudan a yamma kuma mulkin songhey (songhey ) da malle sai tsohuwa gabban

Address

Hotoro Easter By Pass Kano
Kano

Telephone

+2348068413283

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Zabiya Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Zabiya Hausa:

Share