03/05/2025
“SCENARIO” MAI SAUKI A KAN YADDA GINA “WEBSITE” YAKE KAMAR A RAYUWA TA ZAHIRI
Gina website aiki ne mai wahala wanda yake bukatar kwarewa, fikira, dogon nazari, da tunani. A wannan rubutun, CEO zai nuna muku yadda gina website yake kamar a rayuwa ta zahiri, idan ka shirya biyo ni mu je:
—Royalmaster yana so ya gina gida zai yi aure
—CEO yana so ya gina website na chatting
Ga yadda abun nasu zai kasance 👇
🔵 STEP 1: MALLAKAR PLOT OF LAND
Duk wanda zai gina gida yana bukatar ya fara sayen fili (plot of land), don haka yanzu sai Royalmaster ya je ya sayi fili na N100k, ni ma sai na je na sayi fili (web hosting) a yanar gizo na N100k (na yi bayaninsa a rubutuna na baya)
🔵 STEP 2: MALLAKAR ADDRESS
Duk wani gida ko fili yana bukatar address ta yadda duk inda kake a duniya da zaran an ba ka wannan address din to za ka iya zuwa inda gidan yake. Misali, "No. 2, Mohiddeen Road, Damaturu, Yobe State, Nigeria" Kun ga yanzu Royalmaster ya san filinsa yana No.2 Mohiddeen Rd, to ni ma sai na je na sayi nawa address din wanda muke kira domain name a yanar gizo, sai na saka masa suna www•mohiddeen•com
🔵 STEP 3: FARA GINI
Royalmaster constructor ne, ya iya gina gida normal. Sai ya buga blocks, ya tona foundation ya fara daura blocks din nan. Ni ma sai na dauko HTML na fara gina website dina. Blocks din da Royalmaster yake amfani da su wajen gina gidansa daidai suke da HTML dina wanda nake amfani da shi wajen gina website. [HTML prog lang ne da ake amfani da shi wajen gina website] A nan Royalmaster zai yi ta gini har ya kai linter, sannan ya yi rufi ya yi plaster. Ni ma ina aiki da HTML dina.
🔵 STEP 4: PAINTING
Bayan Royal ya gama plaster, sai ya sayo fenti mai kala-kala ya fara fente gininsa. Ni ma sai na dauko CSS na fara kayata website dina. [CSS prog lang ne da ake amfani da shi wajen kayata website] A nan Royalmaster zai yi ta fente gininsa yana kayata shi yadda yake so da colours kala-kala. Ni ma ina kayata website dina da CSS dina.
🔵 STEP 5: DYNAMIC FUNCTIONALITIES
Yanzu an kammala fenti. Sai Royal ya ce ya kamata ya sa wa gidansa solar, da fanka, da bulb, da switch, da sockets, da sauran electric wiring. Ni ma sai na dauko JavaScript na fara sanya wa website dina irin wadannan abubuwan. [JavaScript prog lang ne da ake amfani da shi wajen sanya wa website dynamic functions wadanda za su ba shi damar yin wasu abubuwa kamar validation, alerting, redirection da sauransu.] A nan zan yi aiki da JS da kuma PHP prog lang don karban bayanan users, da tantance su, da yunkurin shigar da su database don adana su, da sauransu.
🔵 STEP 6: SAMAR DA DATABASE KO “SAFE”
Royalmaster ya ce yana bukatar ya kirkiri wata “safe” a gidansa wacce zai rinka adana credentials dinsa, kudi, da wasu muhimman abubuwansa. Sai ya kirkire ta ya saka mata padlock. Ni ma sai na dauko PHP tare da SQL na fara kirkirar database wacce za ta ba ni damar adana bayanan users, da tantance su, da shige da fice, da sanya musu password da sauransu.
______________________________
A wannan dan takaitaccen bayanin za mu fahimci yadda wadannan programming languages din: HTML, CSS, JS, PHP, da SQL suke taka rawa a kowanne mataki na gina website, kamar dai yadda yake a rayuwa ta zahiri cewa ana bukatar daura blocks don yin gini, da kayata shi da fenti, da sanya sauran functions.
Web Development shi ne aikin gina website, wanda yake yin aikin ana kiransa Web Developer. Muna koyar da shi a Flowdiary tun daga beginner, intermediate, da advanced.
📌 MUHIMMAN BAYANI
A ka'idar foundation of programming, HTML da CSS ba programming languages ba ne, saboda ba za a iya gudanar da wasu ayyuka da su ba kamar validation, printing date/time, conditional statement da sauransu. Amma kawai ana musu jam'i ne a kira su da prog langs don kowa ya gane. Ga bayaninsu duka a kasa:
—HTML markup language ne, ana amfani da shi wajen gini da ado, cikakken sunansa HyperText Markup Language
—CSS styling language ne, ana amfani da shi wajen kayatarwa, ado, da kaloli, cikakken sunansa Cascading Style Sheet
—JavaScript (JS) programming language ne, ana amfani da shi wajen gudanar da tantance-tantance a shafi da sauran functions din da sauran prog langs suke yi.
—PHP prog lang ne, ana amfani da shi don tantance-tantance, mu'amala da hidimar database don adana bayanai, tantance users da sauransu. Shi ne yake aiki hand-in-hand da SQL. Cikakken sunansa Hypertext Preprocessor.
—SQL kuma database access language ne, ana amfani da shi wajen adana bayanai a cikin database, da editing, da deleting, da sauran ayyukan da ake bukata wajen managing database. Cikakken sunansa Structured Query Language.
📍 TAMBAYA: Shin a wanne mataki na gini ake saka bulb da fan? Kwatanta aikinsu da wani programming language cikin wadanda na zayyano a sama.
Kamar dai kullum... idan ka fahimta ka yi sharing ga wasu ↗️
✍️ Muhammad Auwal Ahmad ( )
Cofounder & CEO, Flowdiary
Published: 10th September 2024
Updated: 24th April 2025