Sheikh Ja'afar Mahmud Adam Rahimahullah

Sheikh Ja'afar Mahmud Adam Rahimahullah Mun Bude Wannan Shafin Domin Kawo Muku Karatuttukan Malam Ja'afar Da Sauran Malaman Sunnah.

Allah kajikan wadannan bayi naka da Rahama.1. Amadu Bollo2. Sheikh Abubakar Mahmud Gumi3. Sheikh Ja'afar Mahmud Adam4. S...
23/07/2024

Allah kajikan wadannan bayi naka da Rahama.

1. Amadu Bollo
2. Sheikh Abubakar Mahmud Gumi
3. Sheikh Ja'afar Mahmud Adam
4. Sheikh Muhammad Auwal Albany Zaria.

19/07/2024

Mudai na bata lokutan mu akan Abubuwan da basu dace ba mutashi mu nemi Ilimi Arabbi da Boko sannan Musa gaskiya a zuciyar mu in shaa Allah Komai zezama daidai a Nigeria.

Yanayi na tsadar Rayiwa bazai taba can jawa ba semun fara canja Kawu kanmu yaku Yan Uwa Musulmi muji tsoron Allah mudin ...
19/07/2024

Yanayi na tsadar Rayiwa bazai taba can jawa ba semun fara canja Kawu kanmu yaku Yan Uwa Musulmi muji tsoron Allah mudin kasa gaskiya a dukkan al 'amuran mu domin hakan shine mafitar mu muddin muna son canji a wannan yanayi da kasar mu keciki

Sheikh Ja'afar Mahmud Adam Rahimahullah

19/07/2024

Barkanmu da juma'a da fatan kowa zeyi Sallah Lafiya. Allah ya kawo mana mafuta a wannan kasa tamu mai Albarka.

*Tarihin Sheikh Jafar Mahmud Adam***An haifi marigayi Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam a garin Daura, a shekara ta 1962 (ko d...
08/07/2024

*Tarihin Sheikh Jafar Mahmud Adam***

An haifi marigayi Sheikh Ja'afar Mahmoud Adam a garin Daura, a shekara ta 1962 (ko da yake wani lokacin
yakan ce 1964). Marigayi Sheikh Ja'afar ya fara karatunsa na allo a gidansu, a wurin mijin yayarsa, Malam Haruna, wanda kuma dan uwansu ne na jini. Daga nan kuma sai aka mayar da shi wajen wani Malam Umaru a wani gari wai shi Koza, kimanin kilomita 9 a arewa da Daura, wanda shi ma akwai dangantaka ta jini a tsakanin su, wanda kuma shi ne musabbabin zuwansa Kano. Bayan sun zo Kano ne tare da wannan malami nasa, a shekara ta 1971 (ko 1972), sai s**a zauna a makarantar Malam Abdullahi, wanda asalinsa mutumin jamhuriyar Nijar ne, amma yake zaune a unguwar Fagge a Kano. Tun kafin zuwansu Kano, tuni marigayi Sheikh Ja'afar ya riga ya fara haddar Alkur'ani mai girma, wanda ya kammala a shekara ta 1978. Bayan da Malam ya kammala haddar Alkur'ani mai girma, kasancewarsa mai sha'awar ilimi, sai ya shiga makarantu biyu a lokaci daya a shekara ta 1980. Ya shiga makarantar koyon Larabci ta mutanen kasar Misra a cibiyar yada al'adun kasar Misra, (Egyptian Cultural Centre), sannan kuma ya shiga makarantar manya da ba su yi boko ba ta Masallaci Adult Evening Classes, tunda a lokacin shekarunsa sun wuce shekaru na primary, amma duk da haka a wannan lokaci shi ne mafi kankanta a ajinsu. Haka ya rika yin wannan karatu guda biyu: Waccan makarantar ya je ta da daddare bayan sallar isha'i, waccan kuma ta koyo harshen larabcin da yamma. Ya kammala wadannan makarantu a shekara ta 1983. Wannan kuma shi ya ba shi damar shiga makarantar GATC Gwale a shekara ta 1984, kuma ya kammala a shekara ta 1988. A shekara ta 1989, malam ya sami gurbin karatu a jami'ar musulunci ta Madinah, a inda ya karanta ilimin tafsiri da Ulumul Kur'an, wanda kuma ya kammala a shekara ta 1993. Sannan kuma Sheikh Ja’afar ya sami damar kammala karatunsa na digiri na biyu (Masters) a Jami’ar Kasa-Da-Kasa Ta Afrika da take Khartoum, Sudan.Sannan kuma, kafin rasuwarsa, ya riga ya yi

Address

Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sheikh Ja'afar Mahmud Adam Rahimahullah posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share