
06/09/2024
Ofishin Shugaban Maaikata na jihar Kano ya tabbatar da nadin Hajiya Habiba Abubakar Balarabe a matsayin darakatar sashin kula da shirye shirye na nan gidan Radio Kano.
Da yake mika mata takardar nadin a ofishinsa shugaban gidan radio Alhaji Adamu Abubakar Rano ya bayyana nadin nata da cewar abune da ya dace bisa la’akari da kokarinta wajen gudanar da aikinta.
Alhaji Adamu Abubakar Rano ya taya ta murna tare da jan hankalinta da ta kara kokari wajen gudanar da aiyukanta.
Da take jawabinta jimkadan bayan karbar takardar sabuwar daraktar sashin shirye shiryen ta nan Gidan Radio Kano Hajiya Habiba Abubakar Balarabe ta godewa Allah bisa wannan dama da ya bata tare dayin alkawarin yin iyakar kokarinta domin ganin ta baiwa marada kunya.
Hajiya Habiba Abubakar Balarabe ta maye gurbin tsohon daraktan sashin ne Malam Nuhu Gudaji wanda yayi ritaya bayan kammala wa’adin shekaru talatin da biyar yana aikin gwamnati.