AMIH TV 3

AMIH TV 3 Burimmu shine isar da saƙon Addinin Musulunci ga dukkan abin halitta.

Allah ta'ala ya kaimu lokacin da za mu shaida Mala'iku na dora Miki kambu na zinari a farfajiyar Alkiyama Allah ya albar...
01/10/2024

Allah ta'ala ya kaimu lokacin da za mu shaida Mala'iku na dora Miki kambu na zinari a farfajiyar Alkiyama

Allah ya albarkacin Rayuwarki

Yadda ake yin taimama  || Dr Abdullahi M Getso || (018) Al-wajeez A ci gaba da darasin littafin Alwajeez a wannan makon ...
19/09/2024

Yadda ake yin taimama || Dr Abdullahi M Getso || (018) Al-wajeez

A ci gaba da darasin littafin Alwajeez a wannan makon darasin ya mayar da hankali ne akan abinda ya shafi hukunce hukuncen *TAIMAMMA* bayan kammalawa da Babin wanka a musulunci

*Taimama* shine yin wankan tsarki ko alwala amma ba tare da yin amfani da ruwa ba saboda dalilai

Ko biyo mu ta cikin wannan bidiyo don jin kaifiyyar yadda ake taimama hukunce hukuncen ta da kuma sauran darussa da suke da alaka da tsarki

Domin kallo sai ku latsa nan
👇
https://youtu.be/uwmfdVemCSo?si=PzkKnQucdXa6d7J3

Domin shiga zaurukan malaman Sunnah sai ku tura da saƙon sallama da kuma bayyana sunan ku ga wannan lamba *+2349137671784*

Amih tv Tashar Sunnah

A ci gaba da darasin littafin Alwajeez a wannan makon darasin ya mayar da hankali ne akan abinda ya shafi hukunce hukuncen *TAIMAMMA* bayan kammalawa da Babi...

03/08/2024

Zanga-Zangar Tsadar rayuwa: "ƙilu ta ja Bau" yayin da Al'amarin ke shirin barin baya da ƙura

Tun kafin ɗaya ga watan Agusta 1/8/2024 duniyar soshiyal midiya ta ɗauki ɗumi yayin da matasa s**a riƙa jifan malamai da kausasan lafuzza na cin mutuncin, zagi, tsinuwa, cin zarafi, ƙage, da aibatawa.

Ba don komai ba sai abubuwan da su malaman s**a faɗa na hangen nesa da zurfin tunani akan shirin da ɗaukacin matasa Najeriya ke yi na kaddamar da zanga zangar da s**a kira #"ENDBADGOVERNMENT" # ko #"ZANGA-ZANGAR TSADAR RAYUWA" #

Sai dai za a iya cewa *GANI YA KORI JI* yayin da tun a ranar farko al'amurra s**a sauya daga Zanga-Zangar lumana zuwa tarzoma

Tun da farko matasan sun fito cikin fushi da fusatar halin kunci, fatara da ake ciki

sai dai daga bisani ɓata garin waɗanda da dama cikin malamai s**a yi ishara da su sai ga su sun bayyana

Inda s**a fake da wannan yanayi na zanga zangar s**a tada tarzoma tare da sace-sacen kayayyaki mallakin gwamnati da ɗai-ɗaikun mutane.

AMIH TV ta zagaya faɗin kwaryar birnin Kano kuma ta tattaro rahotanni da bayanai cikin hoto mai motsi na yadda wannan zanga zangar ta kasance

domin kallo latsa nan
👇

Enjoy the videos and music that you love, upload original content and share it all with friends, family and the world on YouTube.

An kai mutane maƙura,shugabanni su saurara, lallai a sassauta, a sauƙaƙawa mutane rayuwa wannan shine zai tabbatar da nu...
26/07/2024

An kai mutane maƙura,shugabanni su saurara, lallai a sassauta, a sauƙaƙawa mutane rayuwa wannan shine zai tabbatar da nutsuwa a cikin al'umma shine zai tabbatar da kwanciyar hankali, kuma wannan shine zai tabbatar da zaman lafiya da aminci da kyautatuwar makomar al'umma.

Wannan kira ya fito ne daga bakin limamin masallacin juma'a na Jami'ur Rahma (Kundila) Kano kuma shugaban Jami'ar Al-Istiqama dake sumaila Farfesa Salisu Shehu a yayin hudubar da ya gabatar a ranar juma'a 20/Al-muharram 1445

Farfesa ya yi zazzafar khudubar ne akan yadda shugabanni ke rub da ciki da wadaƙa da dukiyar ƙasa wadda yace tamuce ta mu duka ba wasu kebantattuba

Kazalika ya ce Najeriya za ta ci gaba da zama a matsayin ƙasa mai dunkulalliyar al'umma muddin shugabanni s**a tsai da adalci a shugabanci

Haka kuma khudubar ta zo a washe garin ziyara da s**a kaiwa shugaban ƙasa Bola Tinubu dangane da halin da Nigeria ke ciki

Yan Najeriya dai na ci gaba da kokawa bisa halin matsi da tashin Gwauron kayan masarufi da suke ciki haka kuma kwanaki kaɗan ya rage al'ummar ƙasar su tsunduma Zanga-Zanga ta tsawon kwana goma domin neman samun sassauci na tsadar rayuwa.

Domin kallo latsa nan 👇

An kai mutane maƙura,shugabanni su saurara, lallai a sassauta, a sauƙaƙawa mutane rayuwa wannan shine zai tabbatar da nutsuwa a cikin al'umma shine zai tabba...

Daur! Daura!! Daurah!!! Ga jadawalin yadda za a gudanar da Daura karo na 19 wanda kwamitin ilimi na Almajlisul islami Ho...
24/07/2024

Daur! Daura!! Daurah!!!
Ga jadawalin yadda za a gudanar da Daura karo na 19 wanda kwamitin ilimi na Almajlisul islami Hotoro ya saba shiryawa

Lacca Kenan Da Aka Gabatar Ranar  Juma'a 19/07/2024, Dan taya Murnar Bikin Ya'yan Shaykh Muhammad Bn Uthman Babban  Lima...
21/07/2024

Lacca Kenan Da Aka Gabatar Ranar Juma'a 19/07/2024, Dan taya Murnar Bikin Ya'yan Shaykh Muhammad Bn Uthman Babban Limamin Masallacin Juma'a Na Sahaba Kundila Maiduguri Road Kano

Maudhu'i: "AURE TSAKANIN JIYA DA YAU NAZARI AKAN TASIRIN TSADAR RAYUWA AKAN AURE"

Malamai:
- Shaykh Muhammad Bn Uthman
- Dr. Umar Ibrahim Indabawa
- Sheikh Dr. Aliyu Yunus
- Dr. Abdulkadir Isma'il
- Sheikh Mu'azzam Sulaiman Khalid
- Sheikh Barr Ishaq Adam Ishaq Rijiyar
- Sheikh Lawan Abubakar Shu'aib Triumph

Domin Kallo latsa nan 👇

Lacca Kenan Da Aka Gabatar Jiya Juma'a 19/07/2024, Dan Murnar Bikin Ya'yan Shaykh Muhammad Bn Uthman Babban Limamin Masallacin Juma'a Na Sahaba Kundila Maid...

A yayin gabatar da darasin littafin Alwajeez a wannnan rana Malam ya binciki ra'ayoyin dalibai dangane da batun Zanga-Za...
18/07/2024

A yayin gabatar da darasin littafin Alwajeez a wannnan rana Malam ya binciki ra'ayoyin dalibai dangane da batun Zanga-Zanga da yake ta yamutsa hazo a Najeriya, bayan samun rinjayen marasa goyon bayan zanga zangar sai babban malamin ya yi nasiha da wa'azi bisa irin tarin matsalolin da wannan Zanga-Zanga za ta haifar ga al'ummar Arewa ya buga misali da kasar Sudan,Libiya Mali, Da sauransu wanda yace farawar shigar su bala'in yaƙi daga ZANGA ZANGA ne.

Domin kallo latsa nan
👇

A yayin gabatar da darasin littafin Alwajeez a wannnan rana Malam ya binciki ra'ayoyin dalibai dangane da batun Zanga-Zanga da yake ta yamutsa hazo a Najeriy...

Haihuwa da raɗa wa jarirai suna wani al'amari ne da ake shan fama da dambarwarsa a kasar Hausa musamman duba da cewa tas...
15/07/2024

Haihuwa da raɗa wa jarirai suna wani al'amari ne da ake shan fama da dambarwarsa a kasar Hausa musamman duba da cewa tasirin al'ada ya sanya da yawan mutane aikata abubuwan da Shari'ar Musulunci ba ta zo da su ba kamar Taron suna,ƙauri, Neman tabaraki da sauransu. A cikin wannan Bidiyo fitaccen malamin Addinin musulunci nan Shaykh Ja'afar Mahmoud Adam ya yi fayyacaccen bayani kan abinda ya shafi Daga yaushe ake radawa jariri suna?
Hukuncin Raɗa wa jariri suna
Hukuncin yi wa jariri addu'a
Hukuncin mace ta radawa jaririnta suna
Hukuncin yi wa yaro aski
Hukuncin yanka da ladubbansa

Domin kallo latsa nan👇

Fayaceccen bayani dangane da abinda ya shafi-:Yaushe ake raɗawa jariri suna?Hukuncin Raɗawa jariri sunaHukuncin yi wa jariri addu'a Hukuncin mace ta raɗawa j...

Lacca mai taken ILLAR ZUBAR DA JINI Mai gabatarwa :Shaykh Shamsudeen Auwal Mai Ta'aliƙi :- Dr Abdullahi Muhammad Getso G...
24/06/2024

Lacca mai taken ILLAR ZUBAR DA JINI
Mai gabatarwa :Shaykh Shamsudeen Auwal
Mai Ta'aliƙi :- Dr Abdullahi Muhammad Getso
Guri :-Islamic centre Hotoro,Kano

📸Hoto:Abdallah Adam Danhausa

Address

Kano
Kano
234

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when AMIH TV 3 posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to AMIH TV 3:

Share

Category