09/09/2025
🚨✔️ KURUNKUS: MAFARKIN SZOBOSZLAI YA CIKA AKAN CRISTIANO RONALDO.......
Wani labari mai ban mamaki a duniyar ƙwallon ƙafa… Mafarki ya zama gaskiya.
📆9 ga Satumba, 2009 — Hungary vs Portugal
Dominik Szoboszlai ya shiga filin wasa tare da ‘yan wasan Portuga matsayin yaro da ake riƙe hannunsu...
🗣️Dominik Szoboszlai a 2022:
“Lokacin da nake shekara 8 kuma wasan Hungary da Portugal za'a buga a filin Puskás Arena, na shiga filin tare da ‘yan wasan Portugal Na tsaya a kusa da shi mutane uku kacal ne tsakani na da Cristiano Ronaldo Wannan shi ne mafi kusa da na taɓa zuwa wajen ganinsa, amma ina fata na kusanci shi watarana fiye da haka.”
📆9 ga Satumba, 2025 — Hungary vs Portugal yau Kenan
A Yau, bayan shekaru 16, Dominik Szoboszlai zai shiga filin wasa a matsayin kyaftin ɗin ƙungiyar ƙasa ta Hungary sannan zai sake saduwa da gwarzon sa kuma kyaftin ɗin Portugal, Cristiano Ronaldo 🤯❤️
🗣️Dominik Szoboszlai kan fuskantar Cristiano:
“Na shaida da kaina Ya faru daidai shekaru 16 da s**a wuce. Ina tuna shi sosai. Har yanzu ina tuna yadda na ji a lokacin.
Na taɓa buga wasa da manyan ‘yan wasa, amma ban taɓa buga wasa da shi ba Cristiano Ronaldo shi ne gwarzon da nake kallo tun ina yaro Yanzu za mu zama abokan hamayya, kuma ina fatan ya sanya wannan wasa ta zama abin da ba zan taɓa mantawa da shi ba.” inji Szoboszlai
🗽Yakuke ganin batun dan wasan???