19/09/2025
Ƙalubale Zuwa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf
Tsohon Gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya karyata kalaman Gwamna Abba Kabir Yusuf, inda ya jaddada cewa tarihi da kansa ne zai shaida ayyukan da ya gudanar a Kano.
Ganduje ya ce kafin a fara magana akan cigaban jihar, ya kamata a tuna manyan ayyukan da s**a sauya fasalin Kano a mulkinsa. Ya ambaci gadar Zoo Road, gadar Asibitin Murtala, gadar Saban Titin, gadar Aminu Dantata Bukavo Barrack, gadar Hotoro, da gadar Kofar Mata a matsayin shaidu na zahiri.
A cewarsa:
"Idan Gwamna Abba na da shakku, to ya fito fili ya nuna ainihin wane aiki guda daya da ya kammala tun bayan hawansa kan karagar mulki. Kano ta san wa ya yi aikin gani da ido, kuma wa ya tsaya kan zance kawai."
Wannan kalamai na Ganduje na kara zafafa rikicin siyasa a tsakanin gwamnan mai ci da wanda ya gabace shi, lamarin da ke cigaba da janyo cece-kuce a fadin jihar.
Me zakuce?
Follow Gambiza Tv