19/10/2025
Kungiyar Matan ‘Yan Sanda ta Najeriya (POWA) reshen Jihar Kano, tare da haɗin gwiwar Gidauniyar El ta Ƙarfafa Mata, sun shirya wani taron wayar da kai da duba lafiya domin ƙarfafa matan Kano su kula da lafiyarsu tare da guje wa shan miyagun ƙwayoyi.
An gudanar da taron ne a Police Officers’ Mess da ke Bompai, inda aka halarta da mata daga yankunan umarni na ‘yan sanda guda goma sha ɗaya (11) a fadin Jihar Kano.
Haka kuma, an gudanar da shi tare da haɗin gwiwar ɓangaren mata na Kwamitin Haɗin Kan ‘Yan Sanda da Al’umma (PCRC Women’s Wing).