19/10/2025
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa, wasu majiyoyin tsaro sun bayyana ma ta cewa, jami’an sojan da ake zargi da shirin juyin mulki a Najeriya sun tsara kai hari da kuma kashe manyan jami’an gwamnati, ciki har da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, da mataimakinsa, Kashim Shettima, da wasu shugabanni na majalisa.
Majiyoyin sun shaida wa jaridar Premium Times cewa shirin ya haɗa da kai hari a lokaci guda ga waɗanda aka nufa, a ranar da dukkan su za su kasance cikin ƙasa.
“Sun tsara su hallaka su duka a lokaci guda. Suna neman lokaci da za su tabbata duk manyan jami’an nan suna cikin ƙasa. A duk inda suke, za a kashe su,” in ji wata majiya.
Rahoton ya ƙara da cewa waɗanda ake zargi sun kuma yi niyyar k**a wasu manyan jami’an tsaro ciki har da shugabannin rundunonin soja.
“Haka kuma sun tsara su k**a manyan hafsoshin soja, ciki har da shugabannin rundunoni, amma ba su da niyyar kashe su,” in ji wata majiya daga cikin binciken.
Rahoton ya ce sunan waɗanda aka nufa da kisan ya haɗa da:
* Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu
* Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima
* Shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio
* Shugaban majalisar wakilai Tajudeen Abbas
An ce waɗanda ake zargi sun samu taimako daga wasu jami’an da ke aiki a fadar shugaban ƙasa da wasu wurare masu muhimmanci don tattara bayanai game da motsin waɗanda ake son kai wa hari.
A wata sanarwa da rundunar sojojin ta fitar, an bayyana cewa binciken da ake yi bai tabbatar da wani yunkurin juyin mulki ba tukuna, amma ana duba yiwuwar take dokoki da rashin ladabi daga jami’an da ake zargi.
Rahoton ya ce wannan lamari ya haifar da damuwa a tsakanin hukumomin tsaro da gwamnati, inda ake ganin shi ne daya daga cikin dalilan da ya sa aka dakatar da bikin ranar ’yancin kai ta bana.
Rundunar sojojin Najeriya ta bayyana cewa tana ci gaba da bincike kan lamarin, tare da tabbatar da cewa ba za ta lamunci duk wani yunkuri da zai barazana ga tsarin dimokuraɗiyya da zaman lafiya a ƙasar ba.
゚